Bisa labarin da aka bayar, an ce, a gun taron dandalin fadin albarkacin bakinka kan tattalin arziki da ciniki da aka yi a tsakanin babban yanki da yankin Taiwan na kasar Sin da aka rufe kwanan baya, bangaren babban yankin kasar Sin ya bayar da matakai 15 na moriyar 'yan uwanmu na Taiwan da zai dauka kan yadda za a ciyar da yin musanye-musanye da hadin guiwa a tsakanin gabobi 2 da ke tsakanin mashigin tekun Taiwan. Wadannan matakai sun ta da amsoshi a yankin Taiwan sosai. Da'irori daban-dabam na Taiwan sun yaba wa wadannan matakai sosai.
Lokacin da yake ganawa da manema labaru, Mr. Ma Ying-jeou, shugaban jam'iyyar Kuomintang ya bayyana cewa, wannan dandali ya jawo 'yan kasuwa da masu tafiyar da masana'antu da yawa da su halarci wannan taro. Wannan ne makomar da ake nema.
Mr. Zhang Xianyao, direktan cibiyar nazarin manufofi ta jam'iyyar the People First Party ya bayyana cewa, wadannan matakai 15 da babban yankin kasar Sin ya bayar za su samar da moriya sosai ga yankin Taiwan. Wannan ya bayyana cewa, babban yankin yana daukar matakai iri iri bisa halin da ake ciki yanzu. Za a iya yin hasashen cewa, musanye-musanyen da ake yi a tsakanin gabobin 2 za su samu ci gaba kwarai. (Sanusi Chen)
|