Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-14 17:30:37    
Kasar Sin za ta kara saurin raya kananan motoci

cri

Barka da sake saduwa a cikin shirinmu na yau na Bunkasuwar kasar Sin. Tun daga shekarar da muke ciki, gwamnatin kasar Sin ta tsaida kudurin cewa, za a kara saurin raya kananan motoci a kasar domin yin tsimin makamashin halittu. Sabo da haka, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta nemi kananan gwamnatocin wuri da su soke dukkan manufofin kayyade raya kananan motoci kafin karshen watan Maris na wannan shekara. Sannan kuma, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta ce, za ta tsara da bayar da manufofin sa kaimi ga yunkurin kera da yin amfani da kananan motoci. Masana sun bayyana cewa, wannan yana almantar cew za a kara saurin raya kananan motoci a nan kasar Sin. Kananan motocin da ake sayar da su za su samu karuwa cikin sauri.

A wata kasuwar sayar da motoci a nan birnin Beijing, Mr. Ou Qing wanda yake zaben karamar motar da yake so ya gaya wa wakilinmu cewa, dalilin da ya sa ya zabi karamin mota shi ne, manufar sa kaimi ga yunkurin yin amfani da karamar mota da gwamnatin ta bayar, da kuma karuwar man fetur. Mr. Ou ya ce, "Babbar mota tana da tsada, ba ni da isashen kudin sayenta. A da an kayyade karamar mota da ta yi tafiya a kan wasu tituna. Bayan da aka soke irin wannan manufofin kayyade yin amfani da karamar mota. A ganina, ba za a kayyade karamar mota da ta yi tafiya a wasu tituna. A sa'i daya kuma, karamar mota tana da arha, kuma ba ta sha mai da yawa ba. Ko da yake farashin man fetur yana ta karuwa, zan iya biyan kudin sayen man fetur."

Yanzu a kasar Sin, mutane da yawa kamar Ou Qing suna son sayen kananan motoci. Amma wasu mutanen suna jin damuwa ga ingancin kananan motoci, musamman ingancin tabbatar da zaman karfo na mutanen da ke cikin mota. Mutane wadanda suke aiki a sana'ar motoci suna kuma da ra'ayoyi daban-dabam. Mr. Tang Tan, mataimashin babban direktan kamfanin kera mota kirar Dongfeng-Peugeot, wato daya daga cikin manyan kamfanonin kera motoci a nan kasar Sin ya ce, "Mai yiyuwa ne wasu mutane suna nuna bambanci ga kananan motoci. Domin lokacin da a ga wata karamar mota, da farko dai ana zaton cewa danyen mota ce maras wuya. Fasahohin da ake yin amfani da su a kan kananan motoci suna ja da baya. Amma a hakika dai, a kasuwannin sayar da motoci, an riga an kyautata ingancin kananan motoci sosai."

Yawancin motocin da Kamfani na farko na kera motoci da ke birnin Tianjin yana kera kananan motoci ne. A shekarar bara, yawan kananan motocin da ya sayar ya kai fiye da dubu dari 2, wato ya kai kashi 30 cikin kashi dari na duk yawan kananan motocin da aka sayar a kasuwar kasar Sin. Mr. Wang Gang, babban direktan kamfani na farko na kera motoci da ke birnin Tianjin ya bayyana cewa, domin yanzu gwamnatin kasar Sin ta riga ta bayar da manufofin sa kaimi ga yunkunrin kera da yin amfani da kananan motoci, a nan da gaba, kamfanin zai kara kyautata ingancin kananan motocin da ya kera. Sakamakon haka, mutane da yawa za su yi sha'awar kananan motoci. Mr. Wang ya ce, "Za mu yi amfani da wasu kayayyaki masu inganci a kan kananan motoci kamar yadda muke kera manyan motoci masu tsada. Sabo da haka, idan wani mutum ya sayi motar da muka kera, ba ma kawai wannan mota za ta biya bukatarsa ba, har ma zai kashe kudi kadan kuma ba zai yi amfani da makamashin halittu da yawa ba. A kai a kai ne yunkurin sayen kananan motoci zai zama wata al'ada ga masu kashe kudi."

An bayar da labari cewa, a shekarar bara, gwamnatin kasar Sin za ta bayar da matakin rage yawan harajin da ake buga wa kananan motoci. Idan ka sayi wata karamar mota, ba za ka kashe kudi da yawa ba, kuma ba za a buga haraji da yawa ba ga wannan karamar mota.

An bayyana cewa, a kasashen Turai da kasashen Japan da Koriya ta kudu, an yi maraba da kananan motoci sosai. Wadannan kasashe ma sun bayar da jerin manufofin sa kaimi ga mutane domin su sayi kananan motoci. Sabo da haka, an raya masana'antun kera kananan motoci ciki sauri a wadannan kasashe. Bayan da gwamnatin kasar Sin ta sauya manufar raya masana'antun kananan motoci, tun daga shekarar da muke ciki, mai yiyuwa ne kananan motoci za su zama motocin da mutane za su zaba.

An yi hasashen cewa, a shekarar da muke ciki, yawan motocin da za a sayar da su a kasuwar kasar Sin zai samu karuwa, wato zai karu da kashi 12 cikin kashi dari bisa na makamancin lokaci na shekarar bara. Jimlar yawan motocin da za a sayar da su a nan kasar Sin za ta kai fiye da miliyan 6 da dubu dari 4. Domin yanzu gwamnatin kasar Sin ta riga ta soke manufofin da suke kayyade yin amfani da kananan motoci a kai a kai, kananan motocin da za a sayar da su a kasuwar kasar Sin za su samu karuwa cikin sauri.  (Sanusi Chen)