Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-13 19:08:40    
Sinawa wadanda sai kara yawa suke suna mai da muhimmanci kan lafiyar kwakwalwa

cri

Mr. Feng Yuxuan wani dalibi ne na rukunin B na kolejin koyon fasaha na jami'ar jama'ar kasar Sin. Sabo da matsin da aka yi masa wajen karatu da soyayya, shi ya sa yakan yi zaton iska, wannan kuma ya jawo mugun tasiri ga yin karatu. Ya ce, "A lokacin hutu, nakan yi tunani ba bisa gaskiya ba, wato nakan yi zaton iska, kuma ban iya samun hutawa da kyau ba, shi ya sa na gaji a lokacin da ake yin darasi."

Wata rana ba da dadewa ba, Mr. Feng ya shiga cikin dakin karatu tun da wuri, sabo da a wannan rana da safe an bude darusa na "babban dakin karatu kan lafiyar kwakwalwa" da cibiyar binciken matsalolin hankali ta birnin Beijing da jami'ar jama'ar Sin suka shirya tare.

Wannan babban dakin karatu kan lafiyar kwakwalwa yana hade da darusa 24, ciki har da batun yadda za a gane cutar damuwa da kawar da cutar, halayen musamman da tuntubar masana ingancin tunani game da lafiyar kwakwalwa da kaunar zuci da matsalolin hankali na dalibai.

Mr. Feng ya gaya wa wakilinmu cewa, ya taba ganin likitan duba lafiyar kwakwalwa, amma har ila yau ba a daidaita matsalolin tabin hankalinsa ba tukuna. Ya ce, "Akan kashe kudi da yawa domin ganin likitan duba lafiyar kwakwalwa, wato farashin tuntubar masana ingancin tunani ya kai kudin Sin Yuan 40 zuwa 80 na kowane sa'i. Na kasa biyan kudi mai yawa haka, amma darusan da aka bayar cikin babban dakin karatu kan lafiyar kwakwalwa a kyauta ne kuma a kayadadden lokaci."

Cao Lianyuan, direktan cibiyar binciken matsalolin tabin hankali da shiga tsakani ta birnin Beijing ya bayyana cewa, "sakamakon sauyawar zaman al'umma ya jawo kalubale ga hankulan duk mutunne. Matsalar lafiyar kwakwalwa ba matsalar tabin hankali na mutun daya ba ne kurum, amma matsala ce da ta shafi kiwon lafiyar jama'a da zaman al'umma sosai."

Mutane fiye da 300 ciki har da malaman koyarwa da daliban da suka zo daga jami'o'in birnin Beijing da masu hidima na sa kai domin ceton rayukan mutane da mutanen birnin sun shiga darasi na farko, har da wasu mutane wadanda ba su samu kujeru ba sun tsaya da kafafuwansu don jin darasin da masanin ingancin tunani ya bayar.

Tsoho Li Renze wanda yake da shekaru 73 da haihuwa kuma ya yi ritaya, yana zaune a jihar Haidian na birnin Beijing, bayan da ya ji labarin yin wannan darasi daga wurin dansa, sai ya yi tafiya mai nisa zuwa wurin ba da darasin, ya ce, "lafiyar kwakwalwa ta fi kome". Kullum yana da sha'awa wajen karanta littattafan lafiyar kwakwalwa, ya kuma bayyana cewa, jin dadi ya fi kome, idan wani mutum yana jin dadi wato yana fara'a, zai iya kawo ingancin tunani ga sauran mutane.

Yana fatan ta hanyar sauraron wadannan darusa zai iya samun ilmin kiyaye ingancin tunani, kuma zai kara fadakar da kansu kan lafiyar kwakwalwa.

Mr. Cao Lianyuan ya kuma bayyana cewa, ta hanyar shirya irin wannan darasi da masanan ilmi suka bayar domin yadada da yin furofagandar ilmin kimiyya game da lafiyar kwakwalwa da ingancin hankali, za a iya sa mutane da yawa su mai da hankulansu kan lafiyar kwakwalwa, da fadakar da tarin jama'a kan ilmin lafiyar kwakwalwa da ingancin tunaninsu, da kuma daga matsayinsu kan ingancin hankalinsu, da kara karfinsu wajen fahintar matsalolin hankali da shiga tsakanin. (Umaru)