
A ran 13 ga wata da yamma, Lien Chen, shugaba mai daraja na jam'iyyar KMT ta kasar Sin ya shugabanci kungiyarsa sun tashi daga Taiwan kuma sun bi ta hanyar Hong Kong har sun sauka nan birnin Beijing don halartar taron dandalin tattalin arziki da ciniki tsakanin gabobi 2 da za a yi a ran 14 ga wata.

Bayan saukarsa a babban filin jirgin sama na hedkwatar kasa wato Beijing, Mr. Lien Chen ya yi jawabi cewa, bisa halin da ake ciki wajen samun tsarin bai daya a duniya, dangantakar da ke tsakanin gabobin 2 wajen tattalin arziki da ciniki tana da kyau sosai. Yana fatan gabobin 2 za su yi kokari tare don sa kaimi ga hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki da samun moriyar juna domin kara jin dadin jama'a da samun wadatuwar zaman al'umma bisa harsashin zaman lafiya da samun moriya tare.
An ce, za a shafe kwanaki 2 ana yin wannan taro, muhimmin batun da za a tattauna a gun taron shi ne yin mu'amalar tattalin arziki da ciniki da yin zirga-zirgar jiragen sama kai tsaye tsakanin gabobin 2. A lokacin taron kuma, Hu Jintao, babban sakataren kwamitin tsakiya na J.K.S. zai gana da Mr. Lien Chen. (Umaru)
|