Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-13 16:32:32    
Ina dalilin da ya sa jama'ar kasashen Afirka suna kaunar al'adun Kongfu na kasar Sin?

cri

Ko da yake wasu kasashen Afirka ba su da kudi da yawa, haka kuma jama'arsu ba su kashe kudi da yawa domin sayen kayayyakin al'adu ba, kuma Kaset-kaset da bidioyoyi na kasar Sin ba su jawo hankalinsu sosai ba, amma jama'ar kasashen Afirka suna kaunar al'adun Kongfu na kasar Sin sosai da sosai.

A kasashen Larabawa da ke arewacin Afirka da kasashen da ke yammacin Afirka da tsakiyar Afirka da kuma gabashin Afirka, film na Kongfu na Sin ya fi jawo hankulan jama'a a gidajen film. Cheng Long da Li Lianjie suna zama alamar Sinawa, haka kuma Cheng da Li suna zama manyan taurari a kan film. A cikin ko wane kantin sayar da kaset-kaset da bidiyoyi a ko ina na kasashen, kana iya ganin kaset-kaset da bidiyoyi na kasar Sin kamar 'Huo Yuanjia' da 'Houquan' da kuma 'Menglongguojiang' da dai sauransu, wadanda ake sayar da su da kyau.

Film na Kongfu na Sin yana haddasar wasu abubuwa masu ban sha'awa a kasashen Afirka. A cikin birane da yawa a Afirka, akwai dakunan horar da mutane da ke iya Kongfu. Wasu malamai matasa na wurin ne wadanda suke iya Kongfu kadan. A kasar Somaliya, wani Basinne ya kan yi wasan lankwashe jiki idan yana da lokaci, amma wasu mutanen wajen suna ganin cewa, wannan Basinne yana iya Kongfu, sa'an nan wasu sun roke shi da ya koya musu Kongfu. Ko da yake haka ne, amma har kullum dakunan horar da mutane da suke iya Kongfu suna da mutane masu yawan gaske, kuma dakunan suna samun kudi da yawa. Wani abu mai ban sha'awa shi ne 'yan Afirka sun fi son wasannin komfuta da ke da siffar Sinawa, kamar 'Zhen Sanguo Wushuang'. Idan aka tabo magana a kan Diao Chan, wata yarinya ta zamanin da na kasar Sin, wasu 'yan Afirka suna tsammani cewa, ita jaruma ce a wasan komfuna na 'Zhen Sanguo Wushuang'.

A hakika dai, kasar Sin tana sayar da kayayyakin al'adu da yawa a Afirka, ban da kokarin da hukumomin al'adu na ofisoshin jakadanci na kasar Sin da ke Afirka suke yi cikin shekaru da yawa, jama'ar kasar Sin suna fitar da bidiyoyi a fannoni daban daban zuwa kasashen Afirka, amma jama'ar Afirka suna fi mai da hankali a kan al'adun Kongfu. Ina dalilin da ya sa haka? Kusan ko wane yaro na kantin sayar da bidiyoyi zai gaya maka cewa, 'al'adun kasar Sin suna da mamaki sosai, muna son dukkansu, amma ba mu iya fahimtar wasu abubuwa masu wuya ba. Mu kan sha wahala a cikin zama da aiki, sabo da haka ba mu son abubuwa da ke da ma'anoni masu zurfi a lokacin hutu. Film na Kongfu yana da kyau sosai, ko da yake a wasu lotuka ba mu fahimci me aka fada a cikin film ba, amma muna iya fahimtarn Kongfu da sauki.'

Haka ne, a wasu gidajen film ko a dakunan kofi, jama'a su kan kalli film na Kongfu, ko da yake a cikin wadannan film ana magana da yaren Guangdong na kasar Sin, wanda ba su fahimta sosai ba, amma jama'a suna kaunar wadannan film. Sabo da haka ne, suna son tsofaffin film na Kongfu kamar 'Shaolinsi' da 'Zuibaxian' da dai sauransu, amma ba su son sababbin film na Chenglong ba, haka kuma suna ganin cewa 'Crouching Tiger, Hidden Dragon' ba shi da dadi ko kadan. Game da sauran kayayyakin al'adu na kasar Sin da ake sayar a Afirka, wasu ba a iya fahimtar su da sauki, wasu kuma ba su da sha'awa, sabo da haka, ba su fi al'adun Kongfu a ganin jama'ar kasashen Afirka.

Yana da wuyar cudanya a tsakanin al'adu daban daban, amma ya kamata da farko a yi amfani da kayayyaki masu ban sha'awa da kuma wadanda ake iya fahimta da sauki domin jawo hankulan jama'a, ta yadda za a iya jawo sha'awarsu a kan al'adun kasashen waje.(Danladi)