Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-12 17:07:13    
Mutumin da ya sadaukar da ransa ga aikin shimfida zaman lafiya a gabas ta tsakiya ----Marigayi Yitzhak Rabin

cri

An haifi Marigayi Yitzhak Rabin ne a ran 3 ga watan Maris na shekara ta 1922 a birnin Kudus, kuma ya girma ne a birnin Tel Aviv. Ya taba yin karatu a makarantar noma da jami'ar Miami ta kasar Amurka. A shekara ta 1967, Rabin ya shirya kuma ya shugabanci yaki na uku da ke tsakanin kasashen Larabawa da Isra'ila, sabo da haka kuma, ya zama jarumi na mutanen Isra'ila. A watan Janairu na shekara ta 1968, Marigayi Rabin ya janye jikinsa daga rundunar soja, kuma ya karkata akalarsa zuwa fagen siyasa. A wannan shekara kuma, ya kama mukamin jakadan Isra'ila a Amurka. A shekara ta 1973, ya koma Isra'ila kuma ya zama ministan 'yan kwadago, a watan Janairu na shekara ta 1974, an zabi marigayi Rabin a matsayin dan majalisa. A wannan shekara kuma, wato 1974, marigayi Rabin ya ci zaben zama shugaban jam'iyyar Lebur, a watan Mayu na wannan shekarar kuma, ya fara rike mukamin firaministan majalisar ministoci. A watan Afril na shekara ta 1977, sabo da kudin da matarsa ta ajiye a kasar Amurka wanda ba na halal ba, Marigayi Rabin ya yi murabus daga mukaminsa. Daga baya, marigayi Rabin ya zama ministan tsaro a cikin gwamnatin gamin gambiza da ke karkashin jagorancin jam'iyyar Lebur da kungiyar Lukud. A watan Faburairu na shekara ta 1992 kuma, marigayi Rabin ya sake cin zaben zama shugaban jam'iyyar Lebur, daga bisani a watan Yuni na wannan shekara, jam'iyyar Lebur ta ci babban zaben Isra'ila, a sabo da haka kuma, marigayi Rabin ya sake zama firaministan kasar.

Bayan da ya hau kan kujerar firaministan Isra'ila a karo na biyu a shekara ta 1992, sai marigayi Yitzhak Rabin ya yi matukar kokari a wajen neman tabbatar da zaman lafiya a gabas ta tsakiya. A cikin wa'adin aikinsa, bi da bi ne Isra'ila ta rattaba hannu a kan yarjejeniyoyin zaman lafiya tare da kungiyar Fatah ta Palasdinu da kuma Jordan, wanda shi ya sa aka sami ci gaba sosai a wajen shimfida zaman lafiya a gabas ta tsakiya. Amma duk da haka, manufar da ya gabatar ta musanyar kasa da zaman lafiya ta gamu da kiyewa sosai daga wajen masu tsattsauran ra'ayi na Isra'ila.

A watan Satumna na shekara ta 1993, kungiyar kula da ilmi da kimiyya da al'adu ta MDD, wato UNESCO ta baiwa marigayi Rabin lambar yabo ta zaman lafiya. Sa'an nan a shekara ta 1994, Yitzhak Rabin da ministan harkokin waje na Isra'ila da kuma shugaban kwamitin zartaswa na kungiyar Fatah Yasser Arafat sun sami lambar yabo ta Nobel a kan zaman lafiya tare. A wannan shekara ta 1994, Marigayi Rabin ya kuma samu wata lambar yabo daban, wato lambar yabo ta Prince of Asturias kan hadin gwiwar da ke tsakanin kasa da kasa.

Abin bakin ciki shi ne a ran 4 ga watan Nuwamba na shekara ta 1995, yayin da yake halartar wani biki na neman zaman lafiya a birnin Tel Aviv wanda ke da mahalarta dubu 100, wani mai tsattsauran ra'ayi na Isra'ila ya bindige marigayi Yitzhak Rabin har lahira, kuma ya mutu ne yana da shekaru 73 da haihuwa. A sakamakon haka kuma, marigayi Yitzhak Rabin ya zama firaminista na farko da 'yan hamayya na Isra'ila suka kashe tun bayan da aka kafa kasar. Daga baya, a ran 6 ga wannan watan, hedkwatar MDD ta saukar da tutarta zuwa rabin sanda don nuna ta'aziyya ga Yitzhak Rabin, wanda ya sadaukar da ransa ga aikin shimfida zaman lafiya a gabas ta tsakiya, kuma Boutros-Ghali, babban sakataren MDD ya halarci bikin jana'izarsa.

Doki bai gaji da gudu ba, amma ga karkara ta kare. Yanzu lokaci ya yi da za mu kawo karshen bayani a kan tsohon firaministan Isra'ial, marigayi Yitzhak Rabin. Muna fatan malam Habibu Mannir daga jihar Maiduguri ya ji dadin bayanin, kuma za ku ci gaba da rubuto mana don yi mana tambayoyi ko ba mu shawarwari. Kada kuma ku manta kuna iya kama mu a akwatin gidan wayarmu a kasar Nijeriya, wato Lagos Bureau, China Radio International P.O.Box 7210, Victoria Island, Lagos Nijeriya, ko kuma ku aiko mana wasiku zuwa nan kasar Sin, wato, Hausa Service CRI-24, China Radio International, P.O.Box 4216, Beijing, P.R.China,100040. kuna kuma iya aiko mana Email a kan Hausa @cri.com.cn.