Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-12 16:31:16    
Kudaden musaya masu yawan gaske da kasar Sin ta ajiye, jari ne kuma kalubale ne gare ta

cri

Kasar Sin ta tsaya kan matsayi na farko a duniya a karo na farko wajen ajiye kudaden musaya, wadanda yawansu ya kai dolar Amurka biliyon dari takwas da hamsin da uku da miliyan dari shida ; kasar Japan kuwa tana biye da ita. Ana tambaya, cewa me wadannan kudaden musaya za su kawo wa kasar Sin ? Wassu kwararrun da abun ya shafa sun ba da amsa, cewa kudaden musaya masu yawan gaske kamar haka da kasar Sin ta ajiye, ai jari ne kuma kalubale ne gare ta.

Sanin kowa ne, ajiye wadansu kudaden musaya yana amfana wa wata kasa da takan biya lokacin da take yin cinikayya tare da kasashen waje. Kasar Sin takan samo kudaden musaya ne daga jarin da ' yan kasuwa baki suka zuba a kasar da kuma kayayaykin da takan fitar da su zuwa kasashen ketare. Bari mu dau misali: a shekarar 2005, yawan jarin da ' yan kasuwa baki suka zuba a kasar Sin kai tsaye ya dara dola biliyon 60; kuma yawan rarar kudi da ta samu a fannin cinikin waje ya zarce dola sama da biliyon dari.

Shehun malami Zhao Xijun daga Jami'ar Jama'a ta kasar Sin ya yi nazarin, cewa" karuwar yawan kudaden musaya har ba fashi, wajabtaccen sakamako ne da kasar Sin ta samu wajen bunkasa tattalin arziki kamar yadda ya kamata, kuma lallai tana da ma'ana mai yakini ga kasar Sin a fannin raya kasar; Bugu da kari kuma, wannan ya shaida, cewa lallai kasar Sin ta kara karfin da take da shi wajen fuskantar tarzomar kudade da kuma abubuwa marasa da'a daga ketare".

A farkon shekarar 1980, yawan kudaden musaya da kasar Sin ta ajiye bai kai dola biliyon goma ba, amma yanzu ya zo na daya a duniya. Ko shakka babu, kudaden musaya masu yawan gaske da kasar Sin take da su, za su ba da tabbaci ga yalwata tattalin arzikin kasar kodayake suka kawo cikas wajen gudanar da wannan yunkuri. Shehun malami Zhao Xijun ya bayyana, cewa: ' Kudaden musaya masu yawan gaske da aka ajiye, sakamako ne da aka samu wajen yalwata tattalin arziki bisa matsayi maras daidaito, wannan ya shaida, cewa kasar Sin ta kara dogaro kan kasashen ketare wajen bunkasa tattalin arziki; Sa'annan kuma ya ba da tasiri ga manufar kudi; Dadin dadawa, kudaden musaya masu yawan gaske da kasar Sin ta samu sun shaida wanzuwar rarar kudi mai tsoka a game da cinikin waje, lallai wannan yana da saukin jawo rikici daga kasashen ketare a fannin cinikayya da na hada-hadar kudaden musanya.

Daidai saboda wadannan dalilai ne, ya kasance da muhimmiyar magana dake gaban hukumomin kula da harkokin kudaden waje na kasar Sin kan yadda za su yi amfani da kudaden musaya da yawansu ya zarce dola biliyon dari takwas da hamsin, da kuma gudun samun hadari saboda wannan.Mr. Ba Shusong, mataimakin shugaban hukumar nazarin harkokin kudi ta cibiyar nazarin harkokin raya kasa ta kasar Sin ya fadi, cewa:0'Ya kamata a aiwatar da manufar zuba jari ta hanyoyi da dama wajen tabbatar da samun riba mai tsoka daga kudaden musaya da aka ajiye.'

Yanzu, gwamnatin kasar Sin ta riga ta gane, cewa kudaden musaya masu yawan gaske da kasar ta ajiye kila za su kawo mugun tasiri ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar.

Kwanakin baya ba da dadewa ba, hukumar kula da harkokin kudaden waje ta kasar Sin ta bayyana, cewa za ta kara nuna himma da kwazo wajen neman wata hanya da ta fi dacewa da halin da ake ciki yanzu a kasar wajen yin amfani da wadannan kudaden musaya.( Sani Wang )