Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-12 16:07:06    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(06/04-12/04)

cri
A matsayin gasar jarrabawa ta farko domin wasannin Olympic na Beijing, za a bude gasar fid da gwani ta wasan soft ball ta mata ta duniya ta karo ta 11 a nan Beijing tun daga ran 27 ga watan Agusta zuwa ran 5 ga watan Satumba na shekarar da muke ciki, kwamitin shirya wannan gasa ya kira taron ganawa da manema labaru a Beijing a ran 10 ga wata, inda ya gabatar wa kafofin yada labaru da abubuwan da suka shafi gasar da za a yi. An ce, za a yi wannan gasa a filin wasan soft ball na Fengtai, wanda filin wasa ne na farko da aka kafa domin wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008. Kungiyar kasar Sin da sauran kungiyoyi 15 za su shiga wannan gasa. Bisa bukatun Kwamitin Wasannin Olympic na Duniya, ya kamata a yi gasannin jarrabawa a jere a cikin dukan filayen wasa kafin a bude wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008, don jarraba ingancin wadannan filayen wasa da kuma share fage ga shirya gasanni. Tun daga watan Agusta na shekarar da muke ciki har zuwa watan Afril na shekarar 2008, za a yi gasannin jarrabawa fiye da 40 a cikin dukan filayen wasa da za a yi amfani da su a cikin wasannin Olympic na Beijing.

Akwai wani labari daban da aka ruwaito mana daga birnin Seoul na kasar Korea ta Kudu game da wasannin Olympic, a ran 7 ga wata, shugaban Kwamitin Wasannin Olympic na Duniya Mr. Jacques Rogge ya fayyace cewa, kasashe 6 daga nahiyoyi 4 suna son shirya wasannin Olympic na lokacin zafi na shekarar 2016. Mr. Rogge ya kara da cewa, kasashen Indiya da Japan da Spain da Amurka da Brazil sun riga sun bayyana fatansu, kasar Italiya kuma tana yin la'akari da shirya wannan wasanni.

An yi gasar gudun yada kanin wani kan hanyar motoci ta duniya ta karo ta 21 a nan Beijing a ran 9 ga wata, mutane 6 na ko wace kungiya za su yi gudu daya bayan daya za su hada kansu wajen kammala dukan kilomita 42.195. Kungiyoyi sun yi takara mai tsanani a tsakaninsu, a karshe dai, kungiyar kasar Sin ta zama zakara a cikin rukunin mata, kungiyar kasar Kenya kuma ta zama zakara a cikin rukunin maza.

An rufe gasar fid da gwani ta gajeren iyo ta duniya a birnin Shanghai a ran 9 ga wata, wadda aka yi kwanaki 5 ana yinta. A gun wannan gasar, kungiyar kasar Sin ta sami lambobin zinare 5 da azurfa 1 da kuma tagulla 6, ta zama ta uku a cikin jerin suneyan kasashe wajen samun lambobin yabo. A ciki kuma, dan wasan kasar Sin Wu Peng ba ma kawai ya zama zakara a cikin gasar iyon da ake kira 'Mallam-bude-littafi' mai tsawon mita 200 ta maza ba, har ma ya karya matsayin bajimta na gasar fid da gwani, ta haka, Wu Peng ya zama dan wasan iyo na kasar Sin na farko da ya zama zakara ta duniya a cikin shekaru 13 da suka wuce. Kasashen Australia da Amurka sun zama lambawan da lambatu a wannan gami wajen samun lambobin yabo. Za a yi irin wannan gasar fid da gwani a birnin Manchester na kasar Birtaniya a shekarar 2008.(Tasallah)