Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-11 16:31:07    
Ana more kallon wani irin shahararren fure a birnin Guiyang na kasar Sin

cri

Birnin Guiyang fadar gwamnatin lardin Guizhou ne da ke a kudu maso yammacin kasar Sin. A nan ba a zafi ba sanyi sosai, yanayin ya dace da girman wani irin fure da ake kira Orchid a Turance. Irin wannan fure shahararren fure ne mai gwanin kyau. 'Yan birnin Guiyang suna sha'awar furen nan ainun, kuma sun mayar da furen don ya zama fure da ke alamanta birninsu. A lokacin tohuwar furen nan, 'yan birnin masu dimbin yawa su kan sayi furen nan don more kallonsu. Madam Wang Ping wadda ke sayar da furen ta bayyana cewa, "a galibi dai, fure mai suna "Orchid" da nake sayarwa a kantina ba shi da tsada sosai. Amma farashin ko wane tasar furen nan ya kai kudin Sin Yuan 300 ko 400. Furen yana samun karbuwa sosai daga wajen 'yan birnin Guiyang."

A hakika dai, ba ma kawai 'yan birnin Guiyang suna sha'awar furen Orchid ainun ba, har ma mutane na sauran wurare da yawa su ma suna sha'awarsa kwarai. Malam Luo Wendian wanda ke zama a lardin Sichuan da ke makwabtaka da lardin Guizhou yana sha'awar furen daji irin na Orchid ainun, ya zo kantin Madam Wang Ping ne musamman domin sayen furen daji na Orchid. Ya ce, "birnin Guiyang wuri ne mafi arzikin furen daji irin na Orchid a duk kasar Sin. A ganina, kamata ya yi, a yi kokari sosai wajen kare furen dajin nan sosai. Ana iya cin gajiyarsa wajen kayatar da muhalli, da tsabbace iska da kuma kara daga matsayin al'adu na 'yan birnin. "

Malam Luo Wendian mai sha'awar furen nan ya kan ziyarci bikin baje koli na furen Orchid na kasar Sin wanda a kan shirya a ko wace shekara. An yi sa'a an shirya irin wannan bikin baje koli a birnin Guiyang a shekarar nan.

An shirya bikin baje kolin nan ne a fadar al'adu da ke a cibiyar birnin Guiyang. Yawan tasoshin fure da aka nuna a gun bikin nan don shiga gasar zaman fure mafi kyaun gani ya wuce 4,000. Wani dan yawon shakatawa wanda ya fito daga kasar Japan ya taba kashe kudin Sin Renminbi Yuan 20,000 don sayen wata tasar furen Orchid wanda ya zama zakara a cikin gasar.

Daga cikin tasoshin furen Orchid da aka nuna a gun bikin nan, akwai wata tasar furen Orchid mai launin ruwan hoda wadda maziyarta ke sha'awarta kwarai. Tasar nan ta sami babban yabo daga wajen Malam Hu Keqing wanda ya fito daga lardin Guangdong da ke a kudancin kasar Sin. Malam Wu ya bayyana cewa, yanzu masu sha'awar furen Orchid da yawa su kan je birnin Guiyang daga wurare daban daban na kasar Sin a ko wace shekara don more kallon irin wannan fure. A ganinsa, 'yan birnin Guiyang suna iya mayar da harkokin furen Orchid bisa matsayin wata babbar sana'a. Ya ce, "muhallin birnin Guiyang yana da kyau sosai, kuma an riga an mayar da birnin nan da ya zama kamar wani babban lambun shan iska. Wannan ya dace da bunkasuwar aikin dashe-dashen furen Orchid."

Ban da wannan furen Orchid mai launin ruwan hoda da aka nuna a gun bikin nan, kuma akwai wata tasar furen daban wadda ta shere maziyarta sosai. Kunnuwan furen nan masu launuka iri-iri ne kamar launin ja da rawaya da tsanwa da fari da dai sauransu. An sami wannan tasar furen ne daga lardin Sichuan da ke a kudu maso yammacin kasar Sin. Bayan da wata tsohuwa mai suna Huang Fuling ta ga wannan tasar fure, sai ta yi matukar farin ciki da cewa, a hakika dai "yau na more kallon furen Orchid da ban taba yi ba a da.

Ban da bikin baje kolin furen Orchid na kasar Sin da ake shiryawa yanzu a birnin Guiyang, kuma akwai wurare da yawa da ake iya more kallon furen Orchid a birnin nan. To, jama'a masu karatu, idan kun sami damar zuwa birnin Guiyang na kasar Sin a nan gaba, to, za ku iya ziyartar wadannan wurare ku more kallon irin furen nan da ake kira Orchid a Turance. (Halilu)