 A ran 8 da ran 9 ga wata, Mr. Dennis Sassou-Nguesso, shugaban Tarayyar Afirka, kuma shugaban kasar Congo Brazaville ya yi shawarwari da kungiyoyin wakilan gwamnatin Sudan da kungiyoyi masu rike da makamai kuma masu adawa da gwamnatin Sudan a birnin Abuja na kasar Nijeriya. Shugaba Olusegun Obasanjo na kasar Nijeriya da mataimakin shugaban kasar Sudan Ali Osman Taha da Mr. Salim Ahmed Salim, mai shiga tsakani na farko na Tarayyar Afirka sun kuma halarci wannan shawarwari, inda suka taimaki bangarori daban-dabam na kasar Sudan kan yadda za su yi watsi da sabane-sabanen da ke kasancewa a tsakaninsu domin cimma wata yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya daga duk fannoni a kasar Sudan a karshen watan da muke ciki.
Babban nauyin da aka dora wa wannan shawarwari shi ne, ana son kawar da ra'ayoyi daban-dabam da suke kasancewa a tsakanin gwamnatin Sudan da kungiyoyi masu rike da makamai kuma masu adawa da gwamnati na shiyyar Darfur kan yadda za a raba ikon mulkin kasa da dukiyoyin shiyyar da kuma maganar tabbatar da zaman karko a shiyyar. A gun shawarwarin, Mr. Sassou Nguesso ya yi kira ga bangarori 2 na Sudan da su canja matsayin da suke bi yanzu, kuma su nuna fatan siyasa da ya wajaba domin neman ci gaban shawarwarin. Amma, an gano cewa, a hakika dai, a gun wannan shawarwari, ba a samu ci gaba kan maganar ba. Bayan da aka kawo karshen shawarwarin, Mr. Obasanjo ya ce, bangarorin da abin ya shafa za su ci gaba da yin shawarwari domin neman hanyoyin kawar da wadannan sabane-sabane. Mr. Salim ya kuma bayyana cewa, wannan shawarwarin ya kafa wani muhalli mai kyau ga shawarwarin da za a yi a nan gaba. Amma Mr. Majzoub al-Khalifa, shugaban kungiyar wakilan gwamnatin Sudan ya bayyana cewa, shawarwarin ya samu wasu ci gaba. Ya kara da cewa, Mr. Ali Osman Taha, mataimakin shugaban kasar Sudan zai ci gaba da zama a birnin Abuja har na tsawon wasu kwanaki domin zai ci gaba da yin shawarwari da wakilan kungiyoyi masu adawa da gwamnatin Sudan.
Wakilan Tarayyar Afirka sun bayyana cewa, muhimmin sabanin da ke kasancewa a tsakanin gwamnati da kungiyoyi masu adawa da gwamnati na kasar Sudan shi ne yadda za a raba ikon mulkin shiyyar Darfur. A gun zagaye na 7 na shawarwarin da aka yi, wakilin kungiyoyin shiyyar Darfur masu adawa da gwamnatin kasar Sudan ya taba gabatar da wata shawarar cewa, ya kamata a kara wani mukamin mataimakin shugaban kasar Sudan, ya kuma ce, dole ne wakilin da ya zo daga shiyyar Darfur ya rike wannan mukamin mataimakin shugaban kasar Sudan. A sa'i daya kuma, suna fatan za a iya hada larduna 3 na shiyyar Darfur domin kafa wata gwamnati mai cin gashin kanta a shiyyar Darfur. Amma, wakilin gwamnatin kasar Sudan ya ki amincewa da wadannan sharudan da kungiyoyi masu adawa da gwamnati suka bayar.
A ran 24 ga watan Janairu na shekarar da muke ciki, lokacin da ya hau kan mukamin shugaban Tarayyar Afirka, Mr. Nguesso ya taba bayyana cewa, bayan da ya zama shugaban Tarayyar Afirka, zai yi namijin kokarinsa domin kawo karshen rikice-rikicen da suke nan a Afirka. A ran 6 ga watan Afrilu, a karo na farko ne Mr. Sasso Nguesso ya kai wa kasar Kwadivwa ziyara a matsayin shugaban Tarayyar Afirka, kuma ya sa bangarori daban-dabam na kasar Kwadivwa da su kulla wata yarjejeniya game da share fagen babban zaben kasar. Ba tare da bata lokaci ba ne ya je kasar Nijeriya, shi da Mr. Olusegun Obasanjo na kasar Nijeriya kuma tsohon shugaban Tarayyar Afirka tare ne suka nemi yin sulhu a tsakanin bangarori masu adawa da juna na kasar Sudan. Wannan ya bayyana cewa, shugabannin kasashen Afirka suna kokarin daidaita hargitsin siyasa a kullum bisa ka'idojin tsarin mulkin Tarayyar Afirka. Amma, manazarta sun nuna cewa, domin sabane-sabanen da suke kasancewa a tsakaninsu sun yi tsanani kwarai, akwai wuyar samun ci gaban shawarwarin shimfida zaman lafiya a tsakaninsu a cikin gajeren lokaci. (Sanusi Chen)
|