Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-11 15:26:33    
Ozawa Ichiro, sabon shugaban jam'iyyar Dimokuradiyya

cri

Ran 7 ga wata da yamma, a birnin Tokyo na kasar Japan, jam'iyyar Dimokuradiyya mafi girma da ba ta kan kujerar mulkin kasar ba ta zabi Mr. Ozawa Ichiro da ya zama sabon shugabanta.

A gun babban taron 'yan majalisun wakiliai da dattijai na jam'iyyar Dimokuradiyya da aka yi a ran nan da yamma, an jefa kuri'u ba tare da rubuta sunaye ba, a karshe dai, Mr. Ozawa Ichiro ya lashe dan takararsa Mr. Kan Naoto, yayin da mutane 119 suke goyon bayansa, amma wasu 72 ba su amince da shi ba.

An haifi Mr. Ozawa a ran 24 ga watan Mayu na shekarar 1942, shekarunsa ya kai 63 a yanzu. Bayan da ya kammala karatu a sashen ilmin tattalin arziki na Jami'ar Keio, Mr. Ozawa ya shiga Jami'ar kasar Japan don neman samun digiri na biyu na ilmin shari'a. A shekarar 1969, ko da yake yana yin kokarin neman samun digiri na biyu, amma a matsayin dan jam'iyyar Jimin, ya shiga babban zaben 'yan majalisar wakilan kasar na karo na 32, ya ci nasarar zaman dan majalisar wakilan kasar a karo na farko, a lokacin nan shekarunsa ya kai 27. Daga baya, ya shiga rukunin Mr. Tanaka Kakuei. Bayan wannan kuma, Mr. Ozawa ya taba kama mukami a cikin jam'iyyar Jimin da majalisar wakilan kasar da kuma majalisun minitocin kasar rukunnoni guda 2 daya bayan daya. A shekarar 1989, Mr. Ozawa ya zama babban sakatare mafi karancin shekaru na jam'iyyar Jimin, wanda yake da shekaru 47 da haihuwa a lokacin nan.

Amma bayan wannan kuma, Mr. Ozawa ya gamu da wasu matsaloli a rayuwarsa ta siyasa. A shekarar 1993, ya bar jam'iyyar Jimin saboda ya sami rikicin siyasa a tsakaninsa da firaministan kasar na lokacin nan Mr. Miyazawa Kiichi, ya kafa jam'iyyar Shinsei, ya kuma zama sakataren da ya wakilci jam'iyyar Shinsei. A shekarar nan kuma, Mr. Ozawa ya hada kansa da wakilin jam'iyyar Nippon Shintou Mr. Hosokawa Morihiro, jam'iyyu 8 sun hada kansu sun kafa majalisar ministocin da ke karkashin shugabancin Mr. Hosokawa. Ban da wannan kuma, Mr. Ozawa ya ja gorancin kafa hukumar tsara manufofi ta jam'iyyar da ke mulkin kasar, wato 'hadadden taron wakilan jam'iyyar da ke mulkin kasar '.

Jam'iyyun Shinsei da Nippon Shintou da Minsyatou da kuma Komei sun hada kansu wajen kafa jam'iyyar Shinshintou a shekarar 1994, Mr. Ozawa ya zama babban sakatare, a shekarar 1995 kuma, an zabe shi da ya zama shugaban jam'iyyar. Amma bayan shekaru 3, jam'iyyar ta wargaza. A shekarar 1998, Mr. Ozawa ya sake kafa jam'iyyar Jiyutou, ya shugabanci wannan jam'iyya. Jam'iyyarsa da jam'iyyun Jimin da Komei sun kafa tarayyar gwamnatin kasar, an zabe shi da ya zama 'mutumin da ya fi jawo hankulan mutane a duk shekara'. A shekarar 2000, an kawo baraka ga jam'iyyar Jiyutou, ta kuma balle daga tarayyar gwamnatin kasar.

A shekarar 2002, wakilin jam'iyyar Dimokuradiyyar na lokacin nan da Mr.Ozawa sun tsai da kudurin gama kansu. A watan Satumba na shekarar 2003, an hada jam'iyyun Jiyutou da Dimokuradiyya tare, jam'iyyar Dimokuradiyya ta sami kujeru 177 a cikin babban zaben da aka yi a wannan shekara, ta tabbatar da matsayinta, ta zama jam'iyyar mafi girma da ba ta mulkin kasar ba, Mr. Ozawa ya hau kujerun mataimakin wakilin jam'iyyar. A watan Maris na shekarar da muke ciki, wakilin jam'iyyar Dimokuradiyya Mr. Maehara Seiji ya yi murabus saboda wasikar jabu da aka aiki da ita ta hanyar Internet wato E-mail. Mr. Ozawa da tsohon shugaban jam'iyyar Mr. Kan Naoto sun sanar da neman zaman wakilin jam'iyyar. A karshe dai, Mr. Ozawa ya ci nasara, saboda yana da fasahohi da yawa a fannin siyasa.

Har kullun Mr. Ozawa Ichiro yana tsayawa tsayin daka kan tabbatar da yin karbe-karbe wajen hawa karagar mulkin kasar Japan tsakanin jam'iyyun 2, ya kuma dora muhimmanci kan raya dangantakar da ke tsakanin kasar Japan da kasashen Sin da Korea ta Kudu da sauran kasashen Asiya. Sabdoda an kawo illa ga sunan jam'iyyar Dimokuradiyya, shi ya sa, an danka wa Mr. Ozawa babban nauyi, ya bayyana cewa, an danka masa babban nauyi na tabbatar da sake gina jam'iyyar Dimokuradiyya da neman samun karagar mulkin kasar, zai yi iyakacin kokarinsa wajen canja ikon mulkin kasar da kuma samun karagar mulkin kasar.(Tasallah)