Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-07 15:58:21    
Kusoshin fasaha da mashahuran tamburan kaya suna daga karfin takarar harkokin kasuwanni na kasar Sin

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu karatu, barkanmu da sake saduwa a cikin shirinmu na yau na Bunkasuwar kasar Sin. An dade ana ganin cewa, kasar Sin wata babbar kasa ce da ke kere-kere da yin kayayyaki da yawa, amma lokacin da ake sayar da kayayyakin da aka kera su a nan kasar Sin ko a kasuwannin kasashen waje, an sa tamburan kamfanonin kasashen waje kawai a kan wadannan kayayyaki. Ko da yake kayayyakin da masana'antun kasar Sin suke mallakar cikkakiyar fasaha da tamburansu sun yi kadan, kuma ba su da isashen karfin yin takara a kasuwannin kasashen waje. Amma yanzu wannan halin da ake ciki yana samun sauye-sauye, masu tafiyar da masana'antu na kasar Sin suna kuma matukar kokari kan yadda za su iya mallakar cikkakiyar fasaha da raya tamburan kayayyakinsu da kansu domin kara karfin yin takara a kasuwannin duniya.

Yau da shekaru 5 da suka wuce, kamfanonin kasashen Jamus da Japan da Amurka ne ke mallakar kasuwar takardun kabon. Ko da yake wasu masana'antun kasar Sin suna yin irin wannan takardu na kabon, amma domin fasahar bayyana launi, wato wata fasaha mafi muhimmanci ga aikin yin takardun kabon tana cikin hannun kamfanonin kasashen waje, masana'antun kasar Sin ba su da karfin yin takara a kasuwar. A shekarar 1997, bayan da ya yi ta yin nazari a cikin dogon lokacin da ya wuce, kamfanin Ruifeng da ke lardin Henan na kasar Sin ya kirkiro sabon sinadarin bayyana launi. Ya kuma sami alamar mallakar wannan fasaha. Mr. Liu Zonglai, babban injiniya na kamfanin Ruifeng ya ce, "Fasahar bayyana launi da muka kirkiro ta iya bayyana launi sosai kuma cikin sauri."

Nan da nan ne wannan fasaha ta kawo wa kamfanin Ruifeng babbar moriya. Domin ingancin sanadarin da ya yi ya fi na kamfanin kasashen waje kyau, yanzu, yawan sinadarin bayyana launin da kamfanin Ruifeng yake sayarwa ya riga ya kai kashi 90 cikin kashi dari na duk kasuwar kasar Sin. Yawan kudaden da ya samu ya kai kudin Renminbi yuan kusan miliyan dari 1 a kowace shekara domin sayar da wannan sabon sinadarin bayyana launi. Haka nan kuma, kayayyakin da kamfanonin kasashen waje suka yi suna janye jiki daga kasuwar kasar Sin.

Lokacin da masana'antu wadanda suke da alamar mallaka suke cin nasara a kasuwar kasar Sin, suna kuma kokarin neman bunkasuwa a kasashen waje. Wasu masana'antu wadanda suke da ikon mallakar fasaha sun fara sayar da kayayyakin zamani nasu a kasuwannin kasashen waje. Injin binciken kwantunan kaya da hukumomin kwastam na kowace kasa suke yin amfani da shi yana daya daga cikinsu. A wasu shekarun da suka wuce, sai kasashen Amurka da Jamus suna da fasahar kera irin wannan inji. Amma yanzu, injunan binciken kwantunan kaya a hukumomin kwastam da kamfanin NUCTECH na kasar Sin ya kera sun riga sun kai kashi 57 cikin kashi dari na duk kasuwannin duniya, wato kamfanin NUCTECH yana sayar da kayayyakinsu a kasashe da yaunkuna 38. Mr. Kang Kejun, shugaban kamfanin NUCTECH ya ce, muhimmin dalilin da ya sa kamfaninsa ya samu nasara shi ne yana mallakar fasahar kera irin wannan inji mafi muhimmanci.

"Muhimmin dalilin da ya sa muka samu nasara shi ne mun ci nasarar kera tsarin binciken kwantunan kaya irin na tafi-da-gidanka da ake yin amfani da shi a hukumomin kwastam. Yanzu muna kan gaba a duk fadin duniya a cikin wannan fannin. Bugu da kari kuma, yanzu muna mallakar fasahar binciken kaya mai ruwa-ruwa. Bisa wannan fasaha, za mu gane cewa ko kayayyaki masu ruwa-ruwa da fasinjojin suke dauke da su ne da za su iya kamawa da wuta ko kaya ne mai fashewa cikin sauri."

Bugu da kari kuma, bayan da suka mallaki fasaha mafi muhimmanci ta wani kaya, masana'antun kasar Sin sun fara raya tamburan kayayyakinsu.

Kamfanin kera mota kirar Chery da aka kafa a shekarar 1997 yana da tambarin kaya nasa na kansa. A farkon rabin shekara ta 2005, yawan motoci kirar Chery da aka fitar da su zuwa kasuwannin kasashen waje ya kai kashi 1 cikin kashi 3 na dukkan motocin da kasar Sin ta fitar da su zuwa kasashen waje. Mr. Yin Tongyao, shugaba kuma babban direktan kamfanin kera motoci kirar Chery ya ce, idan kana da wani mashahurin tamburin kaya a kasuwa, za ka iya samun babbar moriya a kasuwannin kasashen duniya. Mr. Yin ya ce, "Idan kana da wani mashahurin kaya naka a kasuwa, za ka iya fitar da kayayyakinka zuwa kasuwannin kasashen waje. Ba zai yiyuwa ne mashahurin kaya na jarin waje ya kebe wasu moriya ga abokan aikinsa na kasar Sin ba. Wannan dalili ne ya sa muke iya fitar da motocinmu zuwa kasuwannin kasashen waje, amma sauran kamfanoni ba su iya fitar da kayansu."

Yanzu, ko a kasuwar gida ta kasar Sin ko a kasuwannin kasashen waje, ko a sana'o'in gargajiya ko a sana'o'in zamanin yanzu, yunkurin neman ikon mallakar fasaha da raya mashahuran tamburan kaya nasu sun riga sun zama buri daya da masana'antun kasar Sin suke neman cimmawa. (Sanusi Chen)