An yi bikin bude taron ministoci na karo na farko na dandalin tattaunawa kan hadin guiwa tsakanin Sin da kasashen tsibirorin tekun Pacific don bunkasa tattalin arziki a birnin Nadi na kasar Fiji a ran 5 ga wata. A gun bikin nan, Mr Wen Jiabao, firayim ministan kasar Sin ya yi jawabi a kan babban taken taron nan inda ya bayyana manufofin kasar Sin dangane da harkokin kasashen tsibirorin tekun Pacific daga duk fannoni, kuma ya gabatar da hakikanan matakai da bangaren Sin zai dauka don gaggauta bunkasa tattalin arzikin kasashen tsibirorin nan da zaman jama'arsu.
Sin da kasashe tsibirorin tekun Pacific dukansu kasashe ne matasa a yankin Asiya da na tekun Pacific, kuma gaba daya suna kokari wajen farfado da tattalin arziki da raya zaman jama'a. A shekarar 2005, bisa shawarar da gwamnatin kasar Sin ta gabatar, an fara yin irin wannan taro don kara karfin hadin guiwa a tsakanin bangarorin biyu don neman samun bunkasuwa tare. A cikin jawabinsa, Mr Wen Jiabao ya bayyana cewa, "a fannin siyasa, muna girmamawa tsarin mulki da hanyar raya kasa wadanda kasashen tsibirorin tekun Pacific suka zaba, wadanda kuma suka dace da halin da suke ciki, sa'an nan muna girmamawa 'yancin kai da mallakar kai na duk kasashen tsibirorin, kuma muna kokari wajen kare zaman lafiya da zaman karko a yankinmu. A fannin tattalin arziki, muna kokarin cim ma manufar bunkasuwa na shekaru 1000 na majalisar dinkin duniya, muna kokarin ba da taimako ga kasashe daban daban da su sami bunkasuwa cikin cin gashin kai. Ko da yake kasar Sin ba ta da wadata, amma za mu yi duk abubuwa da muke iya yi wajen ci gaba da ba da gudummowa ga kasashen tsibirorin ba tare da wani sharadin siyasa ba. "
Mr Wen Jiabao ya jaddada cewa, daga tarihi, an tabbatar da cewa, ko da yaushe kasar Sin aminiyar kasashen tsibirorin tekun Pacific ce. Daga bisani ya gabatar da shawarwari kamar haka, "kara dankon aminci a tsakanin Sin da kasashen tsibirorin tekun Pacific da kara karfin hadin guiwarsu don moriyar juna buri daya ne ga jama'arsu, kuma ya dace da babbar moriyarsu, kuma yana ba da taimako ga tabbatar da zaman lafiya da wadatuwa a yankinsu. Sabo da haka na gabatar da shawarar cewa, Sin da kasashen tsibirorin tekun Pacific ya kamata su kara yin ma'amala a tsakanin gwamnatocinsu da majalisu da jam'iyyun siyasa da kuma jama'arsu, su kara fahimtar juna, su kara amincewa da juna. Haka nan kuma su kara yin tattaunawa a kan manyan batutuwan duniya da na shiyya-shiyya don samun daidaituwa, su nuna wa juna kulawa da goyon baya. Dadin dadawa a kafa sabuwar huldar hadin guiwa a fannin tattalin arziki da cinikayya don moriyar juna bisa bukatun da kasashen tsibirorin tekun Pacific ke yi."
Huldar tattalin arziki da ta ciniki wani babban kashi ne ga dangantaka a tsakanin Sin da kasashe tsibirorin tekun Pacific. Mr Wen Jiabao ya bayyana cewa, bisa bukatun da kasashen tsibirorin tekun Pacific ke yi wajen bunkasa harkokin tattalin arziki a yanzu, bangaren Sin ya tsaida kuduri cewa, "don kara karfin hadin guiwar zuba jari a tsakanin masana'antun Sin da na kasashen tsibirorin tekun Pacific, nan da shekaru uku masu zuwa, bangaren Sin zai samar da rancen kudi mai gatanci da darajarsu ta kai kudin Sin Yuan biliyan 3 don sa kaimi ga masana'antun bangarorin nan biyu da su hada guiwarsu a fannin aiwatar da albarkatu da aikin gona da na daji da kamun kifi da yawon shakatawa da kananan masana'antun saka da sadarwa da zirga-zirgar jiragen sama da sauransu. Haka zalika gwamnatin Sin za ta samar da mankudan kudade wajen sa kaimi ga masana'antun kasar Sin da su zuba jari a kasashen tsibirorin tekun Pacific." (Halilu)
|