Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-05 17:57:58    
Marigayi Shiek Ahmed Deedat

cri

Jama'a masu sauraro, barka da war haka, kuma barkanmu da sake saduwa da ku a zaurenmu na amsoshin wasikunku. Ni ce Lubabatu ke gabatar muku wannan shiri kuma ke yi muku sallama daga nan gidan rediyon kasar Sin da ke nan birnin Beijing. Kwanan baya, a cikin wasikar da ya aiko mana, mai sauraronmu daga jihar Nassarawa ta tarayyar Nijeriya Yanusa Madaki(yariman wuse) ya ce yana bukatar a ba shi tarihin babban malamin nan na musulunci, wato Shiek Ahmed Deedat. To, masu sauraro, a cikin shirinmu na yau, sai ku saurari wani bayani na dangane da tarihin marigayi Shiek Ahmed Deedat.

A ran 8 ga watan Agusta na shekara ta 2005, a cikin shirin safe na gidan rediyon musulmi da ke birnin Durban na kasar Afirka ta kudu, ba zato ba tsammani an fara karanta babin Yassin na alkur'ani mai girma, kuma an sanar da mazaunan birnin cewa, mashahurin malamin musulunci, Shiek Ahmed Deedat ya riga mu gidan gaskiya a ran nan da safe, da misalin karfe 7, kuma ya mutu ne yana da shekaru 87 da haihuwa. Marigayi Shiek Ahmed Deedat ya yi suna ne a kasashen Birtaniya da Amurka da kuma nahiyar Afirka. Sau tari ya taba shiga muhawarar da aka yi a gidan telebijin na Afirka ta kudu, inda ya bayyana ainihin gaskiyar addinin musulunci, kuma ya taba rubuta littattafai da dama.

An haifi marigayi Shiek Ahmed Deedat ne a shekara ta 1918 a kudancin kasar Indiya, ya bi iyayensa zuwa kasar Afirka ta kudu a shekara ta 1927. Sabo da talaucin da iyalinsa ya yi fama da shi, bayan da ya gama karatunsa a makarantar sakandare a yayin da shekarunsa ya kai 16 da haihuwa, sai ya fice daga makaranta ya fara aiki. Shi yaro ne mai hikima, ya yi kokarin karatu da kansa, har ma ya zama babban malamin musulunci a duk duniya.

Abin da ya yi wa marigayi Shiek Ahmed Deedat jagoranci zuwa hanyar addini shi ne wani littattafi mai suna 'neman gaskiya', wanda ya karanta a lokacin da yake saurayi. A cikin littafin, an bayyana wata muhawarar da aka yi tsakanin malaman musulunci da fasto na Christa, wanda ya jawo sha'awarsa a kan addinai, har ma ya kuduri aniyar karanta alkur'ani da Bible, ya nemi asalinsu, don ya fitar da bambancin da ke tsakaninsu. Ya yi ta karatu da sauraron jawaban addini da kuma shiga muhawara, don yalwata masaniyarsa a wannan fanni. A shekara ta 1940, Marigayi Shiek Ahmed Deedat ya shirya bikinsa na farko na bayar da jawabai, wanda ke da lakabi kamar haka, 'Annabi Mohammed manzo ne na zaman lafiya'. Ko da yake a lokacin, yana da masu sauraro guda 15 ne kawai, amma sabo da gwanintarsa a wajen yin jawabi, kana kuma sabo da kalmominsa masu kyau, nan da nan ne ya yi suna, har ma a kan gayyace shi zuwa tarurruka da dama, don ya yi jawabi. Kullum jawabansa sun jibinci bambancin da ke tsakanin manyan addinan nan biyu, wato Musulunci da Krista, wannan kuma abu ne da ya yi nazari a kai har duk rayuwarsa.

A shekara ta 1957, marigayi Shiek Ahmed Deedat ya kafa cibiyar yada musulunci, don neman yin nazari a kan dangantakar da ke tsakanin Musulunci da Krista. A cikin shekaru 40 daga baya, karatu da jawabai da rubuce-rubuce sun zama dukannin abubuwan da yake yi. Bi da bi ne ya rubuta littattafan da yawansu ya kai sama da 20, wadanda suka bayyana dangantakar da ke tsakanin Musulunci da Krista da kuma binciki batutuwan da suka jawo muhawara a tarihi. Ya kware a wajen muhawara. Wata muhawarar da ba za a iya mantawa da ita ba ta faru ne a tsakaninsa da mashahurin bishop Josh McDowell a shekara ta 1981 a birnin Durban na kasar Afirka ta kudu. Bayan muhawarar, ya yi suna kwarai da gaske. A sa'i daya kuma, rubuce-rubucensa ma sun fito a masallaci da dukunan karatu da coci-coci na wurare daban daban.

A shekara ta 1986, bisa gayyatar da sarkin kasar Saudiyya ya yi masa, marigayi Shiek Ahmed Deedat ya kai ziyara a kasar, kuma ya bayar da jawabi a gidan telebijin na kasar Saudiyya. Masaniyarsa da fahimtarsa dangane da ko wace shedara ta Alkur'ani sun shawo kan rukunonin addini na kasar. Sarkin kasar Faisal ya ba shi lambar yabo ta duniya ta yada musulunci.

A ran 3 ga watan Mayu na shekara ta 1996, jikinsa ya shanye sakamakon wata matsalar bugun zuciya. Daga bisani, ba a sake ganinsa a gun tarurruka iri iri ba.

To, masu sauraro, wannan shi ya kawo karshen bayanin da muka yi dangane da marigayi Shiek Ahmed Deedat. Muna fatan kun ji dadin bayanin. Da haka ni Lubabatu daga nan Beijing ke cewa, sai mako mai zuwa, ku zama lafiya.(Lubabatu)