Bisa gayyatar da takwaransa na kasar Australia John Howard ya yi masa, daga ran 1 zuwa ran 4 ga watan nan da muke ciki, firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya kai ziyara a kasar Australia. Ziyarar nan ta zama ta farko da firaministan kasar Sin ya kai wa kasar Australia a shekaru kusan 18 da suka wuce. Bayan dimbin ziyarce-ziyarce kusan 20 da ya yi, a ran 3 ga wata da yamma a birnin Canberra, firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya gana da ma'aikatan ofishin jakadancin kasar Sin a Australia da hukumomi masu jarin kasar Sin da wakilan Sinawa mazauna kasar Australia da kuma daliban da suke dalibta a kasar, inda ya yi farin ciki da cewa,'wannan ziyara ce da ta ci nasara'.
Birnin Perth tasha ce ta farko ta wannan ziyarar da Mr.Wen Jiabao ya yada zango. A cikin rabin yini, Mr.Wen Jiabao ya halarci taron bayyana albarkatun kasa da Ian Macfarlane, ministan masana'antu da yawon shakatawa da albarkatun kasa na tarayyar Australia ya shugabanta, kuma ya kai ziyara a wajen aikin narke karafa na Hismelt da cibiyar nazarin iskar gas ta jami'ar fasaha ta Curtin, ya kuma yi gajerar hira da daliban kasashen biyu.
Kasar Australia ta wadata da albarkatun kasa iri iri, ga shi a kasar Sin akwai babbar kasuwa, sabo da haka, babban makasudin wannan ziyarar da firaministan kasar Sin ya kai wa Australia shi ne kulla dawamammiyar hulda mai kyau ta saye da sayar da albarkatun kasa da makamashi a tsakanin kasashen biyu. Bayan da ya sami masaniya sosai a kan wadatattun albarkatun kasa da Australia ke da su, Mr.Wen Jiabao ya ce, wadatattun albarkatun kasa na Australia ba ma kawai arziki ne na jama'ar kasar ba, haka kuma wani muhimmin fanni ne da kasashen Sin da Australia za su iya aiwatar da hadin gwiwa a kai.
Kafin ya tashi daga birnin Perth, Mr.Wen Jiabao ya kuma gana da gwamnan jihar Australia ta yamma, Alan Carpenter. Mr.Wen Jiabao ya bayyana cewa, jihar Australia ta yamma ta wadata da makamashi da albarkatun kasa, a fannonin ba da ilmi da kimiyya da fasaha ma tana da rinjaye, sabo da haka ya yi fatan gwamnatocin kasashen biyu za su kara kasancewa tamkar gada, don su yi wa bangarorin biyu jagoranci da kuma ingiza su a wajen aiwatar da mu'amalar sada zumunta da hadin gwiwa a fannoni daban daban, ta yadda za su kara ba da taimako ga bunkasa huldar da ke tsakanin kasashen biyu a fannoni daban daban.
Daga baya, Mr.Wen ya ci gaba da ziyararsa zuwa birnin Canberra, hedkwatar kasar Australia. Ran 3 ga wata rana ce da aka fi samun nasara a wannan ziyarar da Mr.Wen Jiabao ya yi. A shawarwarin da ya yi tare da firaminista John Howard, gaba daya ne firaministocin kasashen biyu suka amince da bunkasa huldar hadin gwiwa ta samun nasara tare a tsakanin kasashen biyu daga dukan fannoni a karni na 21, kuma a kafa tsarin kai wa juna ziyara da ganawa da juna. Bayan haka, sun kuma amince da gaggauta yin shawarwari a kan kafa yankin ciniki mai 'yanci da kuma kulla dawamammiyar hulda mai kyau ta saye da sayar da makamashi da albarkatun kasa a tsakaninsu da tsarin farashi mai adalci, kuma su aiwatar da hadin gwiwa a fannin Uranium bisa ka'idar mallakar makamashin nukiliya cikin lumana, su kara mu'amala a fannin al'adu da ilmi, su kara fahimtar juna da dankon zumunci a tsakaninsu, su kara shawarwari a kan manyan al'amuran duniya da na shiyya shiyya.
A gun liyafar da Mr.Howard ya shirya don nuna maraba ga zuwan Mr.Wen Jiabao, a bayyane ne ya bayyana cewa, Australia tana yin marhabin da bunkasuwar kasar Sin, kuma ta nuna yabo a kan rawa mai yakini da kasar Sin ke takawa a harkokin duniya da na shiyya shiyya. Ya ce, saurin bunkasuwar kasar Sin za ta amfana wa duk duniya, ba za a samu moriya a wajen dakile kasar Sin ba. A nasa bangaren kuma, Mr.Wen Jiabao shi ma ya jaddada a cikin jawabinsa cewa, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka a kan bin hanyar neman bunkasuwa cikin lumana, kuma ita kasa ce da ke daukar nauyin da ke bisa wuyanta.
A lokacin ziyarar Wen Jiabao, kasashen Sin da Australia sun rattaba hannu a kan 'yarjejeniyar hadin gwiwar mallakar makamashin nukiliya cikin lumana' da 'yarjejeniyar musanyar kayayyakin nukiliya' da dai sauran yarjejeniyoyin da ke shafar hadin gwiwar bangarorin biyu.
Wannan ziyara ta jawo hankulan kasashe da dama. Ra'ayoyin bainal jama'a suna ganin cewa, wannan ziyarar da firaministan kasar Sin ya kai wa Australia za ta sa kaimi ga bunkasuwar huldar da ke tsakanin kasashen biyu, kuma tana da muhimmanci sosai.(Lubabatu Lei)
|