Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-04-03 10:25:55    
Sashen dauka Sinima na kasar Sin yana kara samu karfi

cri
'Yan kallon Sinima na kasar Sin suna son shiga dakin nuna Sinima na kasar Sin da na kasashen waje. Duk wannan ya kara ingiza bunkasuwar kasuwanin nuna Sinima na kasar Sin. A kowce shekara kasuwannin kasar Sin sukan shigo da Sinima iri iri daga kasashen waje. Amma, yanzu kasuwannin nuna Sinima sun kafa sabon tsarin nuna Sinima wato a kan sashen nan an shiga gasa sosai da sosai, har wannan ya kawo karfin matsi ga masu dauka Sinima.

A kasar Sin akwai wadansu shahararrun masu ba da jagora ga dauka Sinima, kamar wani mai ba da jagora ga aikin dauka Sinima mai suna Zhang yimou, wanda baya da ya gama karatu daga jami'ar koyon dauka Sinima ta Beijing sai ya fara nuna hikimma sosai ga aikin dauka sinima, daga cikin wadansu Sinima da ya dauka sun yi shahara a gida da a kasashen duniya. Har ya sami lambobin yabo da yawa kan aikinsa.

Kwanan baya, wannan shahararren mai ba da jagora ga aikin dauka Sinima mai suna Zhang Yimou ya fara dauka wata sabuwar Sinima mai jawo sha'awar mutane sosai, yawan kudin da shi zai kashe kan aikin dauka wannan Sinima za su kai miliyan 360. Kafin wannan, wata sinima da ya dauka tana siffanta yadda wani tsohon mai mika wasiku da jaridu na wani kauye ya yi kokarin aikinsa har tsuffa sosai, sa'an nan 'dansa ya ci gaba da kama aikinsa. A cikin wannan Sinima, wani shahararren 'dan wasa na kasar Japan ya yi kwaikwayo wannan tsohon mai mika masiku da jarida na wannan kauye, bayan da aka nuna wannan Sinima sai wannan shahararren 'dan wasa na kasar Japan ya sami babban yabo daga 'yan kallo na kasar Sin.

A kasar Sin ban da shahararren mai ba da jagora ga dauka Sinima mai suna Zhang Yumou kuma akwai wani daban sunansa Feng Xiaogang, wannan mai ba da jagora ga dauka Sinima yana son dauka Sinima kan tatsuniyoyi iri na kasar Sin.Wato irin Sinima da ya dauka sun fi jawo sha'awar tsofaffin mutane na kasar Sin. Domin irin tatsuniyoyi sun bayyana zaman rayuwar farar hula sosai, sai 'yan kallo suna gani cewa, mutane dake cikin sinimar da aka dauka suna yin zaman rayuwarsu kusa namu sosai.

Kwanan baya, a cikin dakunan nuna Sinima na birnin Beijing, an nuna wata Sinima da wata mace mai suna Hong Huang ta ba da jagora ga dauka wannan Sinima, a cikin Sinima, wasu mata matsakaitan shekaru sun bayyana zaman rayuwarsu, koda yake dukkansu masu ilmi kuma masu kudi amma ba su ji dadin zaman rayuwarsu, domin sun gamu da wahalhalu da yawa a kan sassa daban daban. Wata mace mai suna Hong Huang ta dauka wannan Sinima har ta jawo hargitsi, wasu mutane sun la'anci wannan Sinima, amma wadansu mutane sun nuna ra'ayinsu daban ga wannan Sinima.

Bisa lisafin da aka yi ba cikakke ba, a shekara ta 2005,yawan sinima da kasar Sin ta dauka sun kai fiye da 260, wato sun karu da kashi kusan daya cikin kashi hudu.Dga cikinsu akwai Sinima na tatsuniyoyi da na wasan raye raye da na wake wake. Don kara karfin sashen dauka Sinima, gwamnatin kasar Sin za ta dauki matakai don ciyar da aikatayyar sha'anin aikin dauka Sinima na kasar Sin tare da kasashen waje kuma za a kara habaka hanyoyin musanye musanye tsakanin masu aikin Sinima na kasar Sin da na kasashen waje.(Dije)