Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-31 14:57:04    
An yi yawon shakatawa a jihar Rajastan ta kasar India

cri

Jihar Rajastan yana bakin iyakar kasa da ke tsakanin arewa maso yammacin India da kudu maso gabashin Pakistan. Wannan jiha ta hada da birane uku, wato Udaipur da Jodhpur da kuma Jaipur, inda a ko ina a wadannan wurare sai gidajen ibada da manyan fadoji da kuma abinci mai dadin ci.

Idan 'yan yawon shakatawa suka isa jihar Rajastan ba da dadewa ba, za su ji mamaki da tsananin gamshin abinci a ko ina a tituna. Amma idan suka ga yadda mazaunan wurin suke zama, to, za su fahimce su. Sabo da 'yan India da yawa suna zama a kan tituna, daga safe zuwa dare, su kan dafa abinci a tituna, a sakamakon haka, 'yan yawon shakatawa su kan ji gamshi na giya da nama da dai sauran abinci. Idan 'yan yawon shakatawa suke zauna a can cikin 'yan kwanakin kadan, za su saba da haka, da suka gama yawon shakatawa, ba za su iya mantawa da wannan gamshin abinci ba.

Mazaunan da yawansu ya kai miliyan biyu suna zama a birnin Jaipur na jihar Rajastan, a wannan birni titunan cike suke da mutane da motoci. Wani sarki mai suna Jai Singh a karni na 18 da ke kaunar al'adar gine-gine shi ne ya tsara shirin birnin Jaipur. A cikin birnin, wani gidan film mai suna Raj Mandir yana da abu na musamman a kan gine-gine. Amma wurin da ya fi jawo hankulan 'yan yawon shakatawa shi ne fadar Hawa Mahal, wadda take da hawa 5.

A halin yanzu dai, an gyara wasu manyan fadoji da su zama kyawawan hotel, sabo da haka, mutanen zamanin yanzu suna iya ganin yadda suke a cikin wadannan fada. Fadar Rambagh Palace ta zama wuri na farko da aka bude wa jama'a a shekarar 1957. Wannan fada tana da dakuna 90 tare da wani kyakkyawan wurin wasa. Game da abinci da sarakuna suka ci a zamanin da, wani mai kula da harkokin fadar ya ce, sabo da fadin hamada ya kai kashi 67 daga cikin dari na dukkan fadin jihar Rajastan, kayayyakin lambu da aka dasa a cikin hamadar sun fi dadin ci.

An gyara fadar Mehrangarh da ta zama wani dakin nune-nunen tsofaffin kayayyaki, a kewayensa sai wata tsofuwar ganuwa. A karni na 15, an shan yin cinikin magunguna masu gusar da hankali a fadar. Amma a halin yanzu, babu 'yan yawon shakatawa da yawa da suke ziyara fadar nan, amma za a iya bude wuraren yawon shakatawa da yawa a nan gaba.

A yankin da ke kewayen birnin Jodhpur, ya kasance da wani wurin shakatawa da fadinsa ya kai hekta 18, a cikinsa akwai wani kyakkyawar fada. An kafa wannan fada ne a shekarar 1930. A yayin da 'yan yawon shakatawa suke zagaya wannan fada, sai suka ji kamar suna zamanin da.

Da muke ziyarar birnin Jodhpur, watakila 'yan yawon shakatawa suna gani cewa, birnin ya fi da abubuwa na musamman na kasar India. Ba haka ba ne, sai mu ga birnin Udaipur. A cikin birnin Udaipur, iyalan gidan sarauta da suka fi dogon tarihi a duk duniya suna zama a birnin, iyalan gidan sarauta suna da zuriyoyi da yawansu ya kai 76. Wani hotel mai suna Lake Palace wanda ya fi suna a kasar India yana tsakiyar tabkin Pichola. Kafin shekaru 200, hotel din shi ne wata babbar fada, kafin shekaru 50, sai an gyaran ta da ta zama wata gidan sarauta. Wannan hotel yana da dakin cin abinci mai suna Neel Kamal da kuku-kuku, wadanda suka fi sunae a kasar India. Yanayin hotel din shi ma yana da kyau sosai, akwai wurin shan isaka da karamin kananan rafuka da kyawawan itatuwa, wadanda ba za a manta da su ba har abada.(Danladi)