Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-31 11:50:20    
Kasar Siu tana da karfi sosai kan bunkasuwar sashen buga jarida da mujalla

cri

A cikin 'yan shekarun da suka wuce, sashen buga jaridu da mujalla na kasar Sin ya sami bunkasuwa da sauri. Bisa sabuwar kididdigar da aka yi an ce, yanzu akwai jaridu iri iri fiye da 1900, da kuma mujalloli fiye da 9000 a kasar Sin, sashen buga jaridu da mujallu ya riga ya zama wani filin da ya fi karfi a cikin sana'ar watsa labaru.

A kasar Sin, an kashe jaridu da mujalla kamar iri biyu, iri daya shi ne na bangaren gwamnati, kamar jaridar "People's Daily", wato jaridar hukuma ta jam'iyyar kwaminis, wannan jaridar da ake bugawa ta fi yawa a kasar Sin; na biyu kuwa shi ne na birane da na sana'a. Ko da yake yawan iri wadanna jaridu biyu da ake buga bai fi sauran ba, amma jama'a suna sonsa sosai, kuma ya zama wani muhimmin sashe na zaman rayuwar al'adu na jama'a.



Madam Wang Guoqing, mataimakin shugaban sashen gudanar da jaridu da mujallu na hukumar kula da harkokin buga jaridu da aikin dab'i na kasar Sin tana ganin cewa, jaridu da mujalloli da kasar Sin ta ke bugawa sun riga sun biya bukatun bangarori daban daban na al'umma. Ta ce, "jaridun birane sun riga sun zama muhimman kafofin watsa labaru a cikin sashen buga jaridu da mujallu, kuma su ne kafofin watsa labaru da suka fi karfin wajen kawo tasiri. A cikin shekaru fiye da goma, jaridun birane sun sami bunkasuwa da sauri. Mun yi kididdiga kan jaridu 39 na muhimman birane, inda a nuna mana cewa, jimlar yawan wadannan jaridun da aka buga ya kai fiye da kashi 40 cikin dari bisa na dukan kasar. Ban da wannan kuma, bisa karuwar sana'ar, wasu jaridun suna buga labari sune kan masana'antun kauyuka, da aikin noma, musamman labarin manoman da suka sami bunkasuwa sosai. A kasar Sin akwai jaridun kananan kabilu 90 da wani abu, yawancin kananan kabilun da ke da harsunansu suna da jaridun harsunan kabulu nasu."



Kasar Sin kasa ce mai yawan mutane, ko shakka babu yawan masu karatu ya bayar da tushe ga bunkasuwar sashen buga jaridu da mujallu. Masu aikin buga jarida da mujalla suna iya shirya jaridu dabam daban bisa ra'ayi ko jin dadin masu karatu daban daban. Masu matsakaitan shekaru, ko samari, ko yara, ko nakasasu, da dai sauransu, dukansu suna iya samu jaridu da mujalloli da suka dace da su.

A cikin lokaci kankani na bunkasuwar sha'anin buga jaridu da mujallu ta kasar Sin, ya kasancewa da wasu matsaloli. Madam Wang Guoqing tana ganin cewa, "muhimmin matsalar sashen buga jaridu da mujallu shi ne yawan jaridu da mujalloli da ake bugawa da yawa sosai, ba a mai da hankali kan hanyar kasuwar sayar da su. Kamar misali, jaridun birane sun tattara a wasu manyan birane ne, sabo da haka, gasar da ake yi a tsakaninsu ta yi tsanani sosai."

Wannan kasuwar buga jaridu da mujalloli da ke da gasa mai tsanani, tana kasancewa da hadari sosai, amma bayan da kasar Sin ta shiga kungiyar WTO, kafofin watsa labaru na kasashen waje suna ta mai da sha'awa kan shigowa kasuwar kasar Sin. Wasu kafofin watsa labaru na kasashen waje sun riga sun samun nasara wajen shiga kasuwar buga jaridu da mujalloli. Madam Wang Guoqing ta bayyana cewa, "bisa alkawarin shigar WTO, kasar Sin ta bude filayen sayar da jaridu da mujalloli, kuma ta kara hadin gwiwa da kamfanonin kasashen waje a kan ayyukan dab'i, da yin talla."

Sashen buga jaridu da mujalloli na kasar Sin ya yi hadin kai da musaya da na kasashen waje. A cikin shekaru 20 da suka wuce, an bude sashen jaridar "People's Daily" ga kasashen waje, yanzu, jaridar nan ta riga ta kafa tashoshi bugawa 11 a kasashen waje, kuma tana fitar wa zuwa kasashe da shiyyoyi 86, yanzu ta riga ta zama jaridar da ake fitar wa kasashen waje da ta fi yawa.

Bayan haka kuma, wasu jaridun birane su ma suna buga jaridu a kasashen waje. Ya zuwa yanzu, halin buga jaridu da mujalloli ga kasashen waje da kasar Sin ke ciki yana da kyau sosai. (Bilkisu)