Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-30 17:55:17    
Sabon salo na iyalan manoman kasar Sin

cri

Daga shekarar 2001 zuwa yanzu, birnin Zunyi na lardin Guizhou da ke kudu maso yammacin kasar Sin yana tafiyar da aikin "samun abubuwa 4 cikin iyalan manoma", wadannan abubuwa 4 su ne arziki da koyon ilmi da yin nishadi da kuma kayatarwa.

Cikin shekaru 4 da suka wuce, birnin Zunyi ya ware kudin Sin Yuan biliyan 200 domin tafiyar da wannan aiki. Muhimman ayyukan da aka yi su ne shimfida hanyoyi, da hakar ramukan gas, da gyara bayan gida da murahu, da samar da telebijin da wayar tarho da ruwan fanfo.

"Samun wadata tsakanin iyalan manoma" ya zama sharadin farko ne ga yin sauran aikace-aikace. Ding Fuqiu, babban jami'in furofaganda na birnin Zunyi ya bayyana cewa, lokacin da ake yin aikin "samun abubuwa 4 cikin iyalan manoma", ana tsayawa a kan mai da aikin bunkasa tattalin arziki a matsayin farko, kuma an dauki aikin kara samar da kudin shiga ga manoma ya zama muhimmin aiki, an taimaki manoma don neman hanyar samun wadata da sa kaimi ga daidaita tsarin sana'o'i".

Makasudin "ba da ilmi ga iyalan manoma" shi ne, a bunkasa sha'anin noma ta hanyar kimiyya da fasaha, da kawar da abubuwa na rashin da'a. An bude dakunan laburare, da yin aikin ba da ilmi na dogon zango, da kafa kos na yin horo domin koyon fasahar yin noma da ilmin tattalin arziki na kasuwanni da na dokokin shari'a, ta yadda za a kara fitar da manoma masu ilmi da yawa a birnin Zunyi.

"Yin nishadi tsakanin iyalan manoma" yana nuna cewa, za a kara wadatar da zamna rayuwar manoma, ta yadda za su kara murna da fara'a. An kara mai da hankali wajen yin gine-ginen al'adu, "bangunan al'adu da titunan zane-zane da duwatun wakoki" wadanda ke bayyana sauye-sauyen kauyuka sun zama abubuwa masu kayatarwa na wurin. Kungiyoyin 'yan wasa manoma, da na masu wasan kwallon kwando da aka kafa ba da dadewa ba suna ta fadi-tashi.

"Samun kayatarwa tsakanin iyalan manoma" makasudinta shi ne domin kayatar da muhalli da kyautata halayen da'a. Bayan da aka dauki matakai daban-daban ciki har da yin muhimman gine-gine da tsai da dokokin kauyuka da yarjeniyoyin kauyawa, an canja muhallin da aka kazamtar a kauyuka. "Girmama tsofaffi da nuna kauna ga yara, da yin jituwa tsakanin iyalai makwabta", da "dokokin iyalai sun sa kaimi ga samun wayewar kai" da sauran alluna da aka rataya a kauyuka sun kafa shahararrun maganganu cikin iyalan manoma, da cin gadon kyayyawan halayen gargajiya na al'umma, da kuma yada tunanin wayin kai.

Sabon halin "arziki da koyon ilmi da yin nishadi da kuma kayatarwa" ya bullo a kauyukan Zunyi, wannan ya ba da misalin koyo ga duk kauyukan kasar Sin.

Kasar Sin za ta dauki aikin raya sabbin kauyukan zaman gurguzu a matsayin farko wajen bunkasa kauyuka cikin shekaru 5 masu zuwa, ma'aunin sabbin kauyuka shi ne "a bunkasa tattalin arziki da samun zaman jin dadi, da kyautata halayen wayin kai da tsabtace muhalli da kuma tafiyar da harkokin kauyuka ta hanyar demokuradiya." Ban da wannan kuma an tsai da kudurin kawar da muhimman gine-gine da za a yi daga birane zuwa kauyuka.

Mutanen da abin ya shafa sun bayyana cewa, sabon aikin "samun abubuwa 4 cikin iyalan manoma" da ake yi ya zama wata sabuwar hanya mai amfani da ake bi don yin bincike kan yadda za a mai da babbar manufar gwamnatin tsakiya ta zama hakikanin abu mai kyau. (Umaru)