Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanmu da sake saduwa a cikin shirinmu na yau na Duniya ina Labari. A ran 27 ga wata da dare an gama aikin kidayar yawan mutanen kasar Nijeriya da aka shafe sati daya ana yinsa. Wannan aikin kidayar yawan mutanen kasar Nijeriya ya jawo hankulan mutanen kasar da sauran kasashen duniya da kafofin watsa labaru sosai. Muhimman kafofin watsa labaru da dama wadanda suka fi shahara a duniya sun bi sawun aikin sun bayar da labaru da yawa game da wannan aiki. Wakilin kamfanin dillancin labaru na Xin Hua na kasar Sin wanda ke aiki a Afirka yana ganin cewa, ya kasance da dalilai biyu da suka sa aka fi mai da hankali kan wannan aikin kidayar yawan mutanen kasar Nijeriya.
Da farko dai, adadin mutanen kasar Nijeriya ya fi sauran kasashen Afirka yawa. Halin yawan mutanen kasar Nijeriya da ake ciki yana yin tasiri kai tsaye ga jimlar yawan mutanen duk Afirka. A kasashen Afirka, yawan mutanen wata kasa magana ce da ke jawo hankulan mutane sosai. Karuwar yawan mutanen kasashen Afirka a kai a kai ta zama wata matsala mai tsanani ga tattalin arziki da zaman al'ummar wurin. A shekarar 1963 a karo na farko ne, kasar Nijeriya ta yi aikin kidayar yawan mutanenta bayan da ta samu 'yancin kai a shekarar 1960. A wancan shekara, yawan mutanenta ya kai miliyan 55 da dubu 660. A shekarar 1991, a karo na uku ne ta yi aikin kidayar yawan mutanenta, duk yawan mutanenta ya kai miliyan 88 da dubu 510. Amma ya zuwa yanzu, shekaru 15 sun wuce, kasar Nijeriya tana da mutane nawa? Ba a san daidai adadin ba tukuna. Sabo da haka, ana mai da hankali sosai kan wannan aikin kidayar yawan mutanen kasar Nijeriya.
Sannan kuma, aikin kidayar yawan mutane yana shafar halin siyasa da tsarin neman bunkasuwar kasar Nijeriya. Shugaba Olusegun Obasanjo na kasar Nijeriya yana ganin cewa, sanin daidai yawan mutanen wata kasa muhimmin tushe ne da za a dogara a kai lokacin da ake tsara manyan tsare-tsaren raya kasar, musamman kasar Nijeriya, wato ko da yake tana da wadatattun makamashin man fetur, amma har yanzu tana daya daga cikin jerin kasashe masu fama da talauci. Sabo da haka, ya sa wannan aikin kidayar yawan mutane a kan gaban dukkan ayyukan da gwamnatinsa take yi. A sa'i daya kuma, Mr. Obasanjo ya jaddada cewa, ana aikin kidayar yawan mutanen kasar ba domin dalilin siyasa ba ne.
Amma a hakika dai, aikin kidayar yawan mutane maganar siyasa ce da ke jawo hankulan mutanen kasar Nijeriya sosai. A kasar Nijeriya, ana raba kujerun majalisar wakilan dokokin kasar bisa yawan mutane na yankuna daban-dabam. Idan wani yanki yana da mutane da yawa, wannan yanki zai fi sauran yankuna samun kejeru da yawa a cikin majalisar wakilan dokokin kasar, wato yankin nan zai iya kara samun ikon mulkin kasar.
A shekarar 1962, kasar Nijeriya ta taba yin aikin kidayar yawan mutanenta, amma domin ya kasance da wasu dalilan siyasa, ba a samu daidai taccen adadi ba. Bisa labarin da aka bayar, an ce, tun daga shekarar 1960, an taba tayar da wasu rikice-rikcen nuna karfin tuwo a kasar Nijeriya wadanda kuma ke da nasaba da maganar yawan mutanen kasar.
A watan Yuni na shekarar da muke ciki ne za a bayar da sakamakon wannan aikin kidayar yawan mutanen kasar Nijeriya. Ko wannan aikin kidayar yawan mutanen kasar zai yi tasiri ga halin siyasa da ake ciki a kasar Nijeriya, ko yaya gwamnatin kasar Nijeriya za ta daidaita manufarta ta yawan mutane bisa wannan sabon sakamako, har yanzu ba a sani ba tukuna. Amma an ce, a cikin dogon lokaci mai zuwa, kasashen duniya da kafofin watsa labaru na duniya za su kara mai da hankulansu kan kasar Nijeriya domin yawan mutanenta ya fi na sauran kasashen Afirka yawa, kuma tana kan matsayin farko wajen fitar da man fetur a Afirka. (Sanusi Chen)
|