Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-30 14:57:59    
Charles Taylor, tsohon shugaban kasar Liberiya

cri

Charles Taylor, tsohon shugaban kasar Liberiya an haife shi ne a shekarar 1948 a karkarar birnin Monrovia, hedkwatar kasar Liberiya. Shi jikan bakaken fata na kasar Amurka ne, ya taba zama makanike a lokacin samari takarsa, ya koma kasar Liberiya ne bayan da ya gama karatunsa a jami'ar kasar Amurka.

A shekarar 1979, ya taba rike mukaman mataimakin ministan kasuwanci na gwamnatin kasar Liberiya da sauransu. A shekarar 1984, ya gudu zuwa kasar Amurka sabo da cigayar kama shi da aka yi da zarginsa da laifin cin hanci, daga baya dai hukumar 'yan sanda ta birnin Boston na kasar Amurka ta kama shi. Bayan da ya gudu daga gidan yari a shekarar 1985, ya taba zuwa kasar Ghana da Burkinafaso da Cote D'ivoire da sauran kasashen yammacin Afrika don yin harkokinsa. A shekarar 1987, Taylor ya sami horo soja a kasar Libya tare da wasu mutane masu yin adawa da gwamnatin kasar Liberiya.

A watan Disamba na shekarar 1989, Taylor ya jagoranci dakarun Jam'iyyar National Patriotic Front ta Liberiya da ya kafa a kasashen waje don komawa gida, bayan haka an shafe shekaru 7 ana yin yakin basasa a kasar Liberiya. A shekarar 1996, bangarori daban daban masu gwagwarmaya da juna na kasar Liberiya sun sami ra'ayi daya a kan batun tsagaita amon wuta da na yin babban zabe da sauransu. A watan Febrairu na shekarar 1997, an canja sunan Jam'iyyar National Patriotic Front da ya zama Jam'iyyar National Patriotic Party wato NPP. A watan Yuli na wannan shekara ne, aka yi zaben shugaban kasar Liberiya da majalisar kafa dokoki ta kasar, Taylor kuma ya ci zaben zaman shugaban kasar.

Bayan da ya hau kujerar mulki, Taylor bai samar da zaman lafiya ga kasar Liberiya da jama'arta ba, an ci gaba da yin yakin basasa. Tun daga shekarar 2000, da babbar murya wasu kasashe wadanda Amurka ke shugabanta suka nemi tumbuke mulkin Taylor, kuma sun daina ba da gudummomar tattalin arziki ga kasar Liberiya. A watan Mayu na shekarar 2001, kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya kakaba wa kasar Liberiya takunkumin makamai da na tattalin arziki sabo da goyon baya da kasar ta nuna ga dakaru masu adawa da gwamanti na Saliyo da sauran kasashe da ke makwabtaka da ita, sa'an nan kuma an hana Taylor ya bar kasarsa yadda ya ga dama.

Taylor ya ga tilas ya ajiye mulkinsa ne a watan Yuli na shekarar 2003, sabo da matsi da kasar Amurka da gamayyar tattalin arziki ta kasashen yammacin Afrika suka yi masa, kuma ya yi gudun hijira zuwa kasar Nijeriya a watan Augusta na shekarar. Ta haka an samar da wata hanyar da aka bi don kawo karshen yakin basasa da aka shafe shekaru 14 ana yinsa a kasar Liberiya da kuma yin babban zabe. Bayan haka kotun musamman ta majalisar dinkin duniya da ke a kasar Saliyo ta sha neman da a gurfanar da Taylor a gaban kuliya sabo da zarginsa da laifuffukan yaki da na nukura da dan adam da keta dokar jin kai ta kasa da kasa da sauran irinsu guda 14. Amma kasar Nijeriya ta sha bayyana cewa, babu yadda za a yi ta mika Taylor ga kowa, sai dai ga gwamnatin kasar Liberiya da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya.

A watan Oktoba na shekarar bara, a karo na farko ne aka yi zaben shugaban kasar Liberiya da majalisar dokokin kasar tun bayan yakin basasa, sai aka kafa sabuwar gwamnatin kasar . A farkon watan Maris na shekarar nan, a hukunce, sabuwar gwamnatin kasar Liberiya ta gabatar da cewa, ta nemi da a komar da Taylor gida. A ran 25 ga atan Maris, fadar shugaban kasar Nijeriya ta bayar da sanarwar cewa, kasar Nijeriya ta riga ta yarda da komar da Taylor gida. A daren ran 27 ga wata, Taylor ya bace daga masaukinsa a kasar Nijeriya yayin da yake gudun hijira. Hukumar 'yan sanda ta kasar Nijeriya ta tabbatar a ran 29 ga wata cewa, hukumar 'yan sanda ta kasar Nijeriya ta riga ta kama Taylor. (Halilu)