A ran 28 ga wata rana ce ta yin babban zabe a kasar Isra'ila. Wasu manazarta sun bayyana cewa, cikin wannan babban zabe, kuri'un da ke cikin hannun jama'a masu yin zabe wadanda yawansu ya kai miliyoyi ba ma kawai za su iya bude wani sabon zamanin siyasa ba, har ma za su iya tsara manufar halin da ake ciki a Isra'ila har da gabas ta tsakiya.
Kwanan baya, jaridar "Jerusalem Post" ta kasar Isra"ila ta buga wani bayani cewa, wannan wani zabe ne da ya yi tashi daya da na manyan zabubbuka sau 3 masu ma'ana wajen sauya tarihin Isra'ila, wato su ne, ta hanyar babban zaben da aka yi a shekarar 1977, rukunin Likud ya kawo karshen kanekanen da jam'iyyar Lebour a karkashin shugabancin Mr. Yitzhak Rabin ta yi tun bayan samun mulkin kasar, daga nan ne aka fara yin karbe karbe wajen hawa karagar mulki tsakanin jam'iyyu 2 masu karfi na kasar. Bayan da jam'iyyar Lebour da ke karkashin shugabancin Mr. Rabin ta ci babban zabe a shekarar 1992, an fara yunkurin shinfida zaman lafiya na Oslo. Bayan da Mr. Ariel Sharon ya ci babban zabe a shekarar 2003 ya shiga cikin fadar firayim ministan kasar, kuma ya soke yarjejeniyar Oslo da aiwatar da manufar janye jikin kasar Isra'ila daga zirin Gaza karfi da yaji.
Abun da ya fi jawo hankulan mutane cikin wannan zabe shi ne jam'iyyar masu ra'ayin tsaka-tsaka wadda tsawon lokacin kafuwarta bai kai rabin shekara ba wato jam'iyyar Kadima. Bisa binciken ra'ayoyin jama'a da aka yi an ce, ba tare da jan kafar wando ba jam'iyyar Kadima za ta sami nasara kan rukunin 'yan ra'ayin mazan jiya na Likud da jam'iyyar Lebour wato jam'iyyar masu sassaucin ra'ayi cikin zaben.
Kirarin takarar zabe da jam'iyyar Kadima ta yi shi ne "Za a mayar maka da wata Isra'ila daban", tafarkin aiki na jam'iyyar shi ne "janye jiki bisa gefe daya, da tabbatar da iyakar kasar Isra'ila ta nan gaba". Ra'ayin janye jiki daga yawancin yankunan da ake mamaye da su, da yarda da Palesdinu da ta kafa kasarta, da neman hanyar daidaita sabani a tsakanin Palesdinu da Isra'ila, ta yadda za a kwantar da matsanancin hali cikin dan lokaci, wannan ya zama muhimmin ra'ayin jama'ar Isra'ila a halin yanzu.
'Yan kallo suna ganin cewa, idan jam'iyyar Kadima ta ci zabe kuma ta kafa gwamnatin kasar ta hanyar hadin gwiwa a tsakaninta da jam'iyyar Lebour da sauran jam'iyyu masu sassaucin ra'ayi, mai yiyuwa ne "janye jiki bisa gefe daya" zai zama muhimmin aikin da za a yi cikin 'yan shekaru masu zuwa domin kyautata dangantakar da ke tsakanin Isra'ila da Palesdinu, amma har ila yau ba za a iya samun mafita mai haske ba wajen tafiyar da shirin "taswirar hanyar" shinfida zaman lafiya a gabas ta tsakiya.
Amma har ila yau ya kasance da abubuwa da yawa da ba su tabbatu ba domin tabbatar da shirin janye jiki bisa gefe daya da jam'iyyar Kadima ta gabatar. Dalilin da ya sa haka shi ne da farko, wannan ya danganta ga yawan kuri'un da jam'iyyar Kadima ta samu wajen zaben, na 2, shirin janye jiki bisa gefe daya ya saba wa kuduran da abin ya shafa na M.D.D. da kyar zai samu karbuwa daga wajen Palesdinu da sauran kasashen Larabawa, na 3, idan kungiyar Hamas ta canja ra'ayinta, ta amince da Isra'ila, Isra'ila kuwa za ta rasa dalilin karya da za ta dauka don janye jikinta bisa gefe daya.
Ra'ayoyin bainal jama'a na Isra'ila sun bayyana cewa, ban da jam'iyyar Kadima da ta shiga takarar babban zaben, kuma da akwai jam'iyyar Lebour da rukunin Likud. Duk da haka, Lior Chorev, mai yin sharhi kan siyasa na Isra'ila ya bayyana cewa, ko wace jam'iyya ce ma ta ci babban zaben a karshe, za a mika mulkin Isra'ila cikin hannun mutanen sabon zuriya. (Umaru)
|