Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-29 16:54:07    
Taron koli na kawancen kasashen Larabawa ya karfafa kasancewar Sudan tamkar gada a tsakanin kasashen Larabawa da kasashen Afirka

cri

Bayan taron shugabannin kawancen kasashen Afirka da aka yi tare da nasara a watan Janairu na wannan shekara a birnin Khartoum, hedkwatar kasar Sudan, a ran 28 ga watan nan da muke ciki kuma, an kira taron koli na kawancen kasashen Larabawa a birnin. Manazarta sun nuna cewa, mai yiwuwa ne taron kolin nan zai karfafa kasancewar kasar Sudan tamkar wata gada a tsakanin kasashen Larabawa da kasashen Afirka, a sa'i daya kuma, daidaita batun Darfur cikin hadin gwiwa zai zamanto dandalin hadin gwiwa a tsakanin bangarorin biyu.

Wani masanin watsa labaru na kasar Somaliya wanda ya zo musamman domin sa ido kan wannan taron koli na kawancen kasashen Larabawa, ya bayyana cewa, bi da bi ne shugabannin Afirka da na kasashen Larabawa suka taru a birnin Khartoum, wannan shi ya sa Sudan ta zama tauraruwar da ke jawo hankulan kasashen Afirka da na Larabawa, haka kuma ya daga matsayin Sudan a nahiyar Afirka da kuma a kasashen Larabawa.

Sudan wakiliya ce ta kawancen kasashen Larabawa, haka kuma wata kasa ce da ke cikin kawancen kasashen Afirka. A gun taron shugabannin gamayyar Afirka da aka yi a watan Janairu, Sudan ta ci zaben zama kasar da za ta shugabanci kawancen kasashen Afirka a zagaye mai zuwa, kuma za ta hau kan kujerar a shekara ta 2007. A gun bikin bude taron shugabannin kawancen kasashen Larabawa, Sudan za ta kuma karbi ragamar jagorancin kawancen kasashen Larabawa. Hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen Larabawa da Afirka za ta zama muhimmin abin da za a tattauna a gun wannan taron shugabannin kawancen kasashen Larabawa, wannan kuma halin musamman ne na wannan taro wanda har ya sa taron ya bambamta da tarurruka na da. Bayan haka kuma, halin da Palasdinu ke ciki da batun Iraki da gyare-gyaren hukumomin kawancen kasashen Larabawa wadanda suka fi daukar hankulan kasashen Larabawa su ma za su kasance abubuwan da za a tattauna a gun taron.

A gun taron, za a kuma gabatar da hakikanan shawarwari da bukatu a kan batun Darfur na Sudan. Da ma, kawancen kasashen Afirka ne ke jagorancin shawarwarin shimfida zaman lafiya a tsakanin gwamnatin Sudan da kuma kungiyoyin Darfur wadanda ba su ga maciji da gwamnatin kasar, kawancen kasashen Larabawa sai kawai ya tsaya ya yi kallo. Amma bisa daftarin kudurin da aka zartas a gun taron ministocin harkokin waje na kwamitin daraktocin kawancen kasashen Larabawa wanda aka yi daga ran 25 zuwa 26 ga wata, an ce, kawancen kasashen Larabawa zai fara taka rawa mai yakini a wajen shimfida zaman lafiya a yankin Darfur, don tallafa wa Sudan da kawancen kasashen Afirka wajen daidaita matsalar kamar yadda ya kamata. Bayan haka kuma, kawancen kasashen Larabawa zai nuna goyon baya ga Sudan a wajen kin yarda da rukunonin waje da su yi amfani da matsalar Darfur don neman tsoma baki cikin harkokin gida na kasar, kuma zai jaddada cewa, duk wata rundunar soja da ba ta kasashen Afirka ba, ba za ta iya shiga yankin Darfur ba sai dai ta samu amincewa daga gwamnatin Sudan. A sa'i daya kuma, kawancen kasashen larabawa zai nuna goyon baya ga kawancen kasashen Afirka da ya ci gaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya a yankin Darfur, kuma zai yi kira ga kasashen Larabawa da su bayar da kayan agaji ga rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya da kawancen kasashen Afirka ya jibge a yankin Darfur kamar yadda ya kamata, zai kuma kirayi kasashen Larabawa da ke nahiyar Afirka da su kara tura rundunar sojoji don su hada kai da rundunar kiyaye zaman lafiya ta kawancen kasashen Afirka.

Idan za a cimma nasarori a wajen kokarin da kawancen kasashen Larabawa da kawancen kasashen Afirka za su yi cikin hadin gwiwa, to, batun zai sa kaimi ga bangarorin biyu da su karfafa hadin gwiwa tsakaninsu, kuma zai ba da taimako a wajen daidaita sauran matsalolin shiyya shiyya.(Lubabatu Lei)