Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-29 15:20:57    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(03/23-03/29)

cri
Shugaban kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing Mr.Liu Qi ya gana da shugaba mai daraja na duk rayuwa na Hadaddiyar Kungiyar Wasannin Olympic ta Duniya Mr. Juan Antonio Samaranch da ke ziyarar Beijing a ran 24 ga wata. A lokacin ganawar, Mr. Liu Qi ya nuna wa mr. Samaranch yabo saboda gudummowar da ya bayar wajen shiryawa wasannin Olympic da birnin Beijing ya samu damar yi da kuma yada wasannin Olympic a kasar Sin. Ran 23 ga wata, Mr. Samaranch ya halarci harkoki a jere da suka shafi wasannin motsa jiki, bayan da ya halarci dandalin tattaunawa na karo na 3 tsakanin kasashen Sin da Spain a birnin Shanghai tun daga ran 21 zuwa ran 22 ga wata.

Akwai labaru 3 da aka ruwaito mana game da filayen wasannin da za a yi amfani da su a lokacin wasannin Olympic na shekara ta 2008 na Beijing. Ran 23 ga wata, an fara gina cibiyar wasan kwallon tennis da ke wurin shakatawa na Olympic ta Beijing. Wannan cibiya tana cikin wurin shakatawa na Olympic na Beijing, za a yi amfani da ita domin gasannin wasan kwallon tennis na wasannin Olympic na Beijing da kuma gasannin wasan kwallon tennis kan keken guragu na wasannin Olympic na nasakassu na Beijing.

Bayan da tawagar Hadaddiyar Kungiyar Wasan Kwallon Kafa ta Duniya wato FIFA ta dudduba ci gaban shirya gasannin kwallon kafa na wasannin Olympic na Beijing tun daga ran 21 zuwa 22 ga wata, mataimakin shugaban kungiyar FIFA Mr. Issa Hayatou da ke shugabancin tawagar ya bayyana cewa, kungiyar FIFA ta nuna gamsuwa kan ayyukan shiryawa gasannin wasan kwallon kafa na wasannin Olympic na Beijing, ta yi imanin cewa, za a tafiyar da gasannin lami lafiya.

Ban da wannan kuma, wani jami'in kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing ya fayyace a kwanan baya cewa, don tabbatar da amfanin filayen wasa na wasannin Olympic na Beijing, da kuma share fage ga shiryawa da kuma tafiyar da gasanni, kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing ya tabbatar da yin gasannin jarrabawa 42 tun daga watan Agusta na shekarar da muke ciki zuwa watan Mayu na shekarar 2008.

An rufe wasannin kasashen renon Ingila wato Commonwealth na karo na 18 a birnin Melbourne na kasar Australia a ran 26 ga wata. Kasar Australia ta zama lambawan saboda samun lambobin zinare 84 a wannan gami. Kasar Birtaniya ta zama lambatu tare da samun lambobin zinare 36, kasar Canada ta zama ta uku tare da lambobin zinare 26. An bude wannan wasanni a ran 15 ga wata, 'yan wasa fiye da dubu 4 daga kasashe da yankuna 71 mambobin Commonwealth ne suka shiga manyan gasanni 21 da ke kunshe da wasan guje-guje da tsalle-tsalle da iyo da wasan kwallon badminton da wasan kwallon kwando da dai sauransu.

A cikin gasar gudun Marathon ta duniya da aka yi a birnin Xiamen da ke kudancin kasar Sin a ran 25 ga wata, 'yar wasan kasar Sin Sun Weiwei ta zama zakara a cikin rukunin mata da sa'o'i 2 da mintoci 26 da dakikoki 32. A cikin rukunin maza kuma, dan wasan kasar Kenya Stephen Kamar ya zama zakara. 'Yan wasa fiye da dubu 20 daga kasashe da yankuna 39 suka shiga wannan gasa.(Tasallah)