Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-28 16:08:11    
Kasar Sin ta tabbatar da makasudin shawo kan ciwon tibi a daidai lokacin da aka tsai da

cri

Ran 24 ga wata, ranar shawo kan ciwon tibi ta duniya ce. A ran nan, dukan mutanen duniya sun kara karfin shawo kan irin wannan ciwo. Kasar Sin, wata kasa ce da take fama da ciwon tibi, shi ya sa, a wannan ranar kuma, ta tafiyar da harkoki iri daban daban, ta takaita fasahohi da darussa da ta samu daga wajen shawo kan ciwon tibi. Wani jami'in kasar Sin ya bayyana cewa, a shekarar da ta gabata, kasar Sin ta riga ta tabbatar da makasudin da Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya wato WHO ta tsara wajen shawo kan ciwon tibi a daidai lokacin da aka tsai da.

Ciwon tibi yana yaduwa a ko ina a duniya, ya riga ya zama wata babbar matsala ga dan Adam da tilas ne ya fuskanta a fannonin kiwon lafiya da zaman al'ummar kasa. Kasar Sin kuma tana fama da wannan ciwo, akwai masu fama da wannan ciwo kimanin miliyan 5 a kasar Sin, yawansu ya zama lambatu a duniya gaba daya.

Don hana yaduwar ciwon tibi tun da wuri, hukumar WHO ta gabatar da makasudi a jere wajen shawo kan ciwon a shekarar 2001, bisa abubuwan da aka tanada cikin wadannan makasudi, ta bukaci kasashen duniya da su tafiyar da dabarar shawo kan ciwon tibi ta zamani a duk fadin kasashe kafin karshen shekarar 2005, kuma za su iya gano wadanda suka kamu da ciwon tibi da ke karuwa da yawansu ya kai fiye da kashi 70 cikin dari, yawan mutanen da suka warke zai kai fiye da kashi 85 cikin dari. Kakakin ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin Mr. Mao Qun'an ya bayyana cewa, kasar Sin ta riga ta tabbatar da wadannan makasudi. Har zuwa karshen shekarar 2005, kasar Sin ta aiwatar da dabarar shawo kan ciwon tibi ta zamani a duk fadin kasar, abubuwan da aka tanada cikin wannan dabara su ne, shirye-shiryen a jere da aka tsara don shawo kan ciwon tibi wajen hukumomi da kungiyoyi da ma'aikata, kuma yawan masu ciwon da ya karu kuma aka gano su ya kai kashi 79 cikin dari, haka kuma, yawan mutanen da suka warke ya kai kashi 91 cikin dari. Bisa wannan sakakamon kimantawa da aka samu, kasar Sin ta tabbatar da makasudi na mataki da ta yi wa kasashen duniya alkawari wajen shawo kan ciwon tibi a daidai lokacin da aka tsai da.

Don tabbatar da wannan makasudi, gwamnatin kasar Sin ta dauki mataikai masu amfani a jere. Ta tafiyar da dabarar shawo kan ciwon tibi ta zamani tun daga shekarar 2001, a shekarar nan, ta tsara shirin shawo kan ciwon tibi na tsawon shekaru 10, ta mayar da ciwon tibi a matsayin ciwo mai yaduwa da aka dora muhimmanci a kai, ta aiwatar da manufofin bincike da shawo kan ciwon tibi ba tare da biyan kudi a duk kasa ba sannu a hankali. Ban da wannan kuma, don tabbatar da zuba kudi kan shawo kan ciwon tibi, kasar Sin ta ware kudaden da yawansu ya kai kudin Sin yuan miliyan 40 a ko wace shekara tun daga shekarar 2001. ta yi amfani da wadannan kudade wajen ba da maguguna ba tare da biyan kudi ba da kara karfin ba da ilmin kiwon lafiya da kuma kyautata halin da ake ciki a fanin bincike da dudduba lafiya, daga baya kuma, kasar Sin ta kara wadannan kudade zuwa misalin kudin Sin yuan miliyan 300 a shekarar 2004.

Ko da yake an sami nasarori haka, amma har zuwa yanzu akwai sauran rina a kaba ga kasar Sin. Mashawarci na kwamitin ba da shawara na masana masu ilmin ciwon tibi na ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin Mr. Duanmu Hongjin ya bayyana cewa, rukunoni daban daban na kasar suna bukatar kara karfin shawo kan irin wannan ciwo don kawar da tasirin da ciwon ya kawo wa kasar Sin a fannin kiwon lafiyar al'ummar kasar. Yana ganin cewa, ya kamata kasar Sin ta tsaya tsayin daka kan tafiyar da ayyukan shawo kan ciwon tibi, musamman ma ta kara karfin shawo kan wannan ciwo tsakanin manoma da mutanen da ba su yi rajista ba.(Tasallah)