Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-28 10:49:55    
kasar Sin tana kara karfinta wajen kare ikon mallakar ilmi bisa shari'a

cri

A halin yanzu, kasashen duniya suna mai da hankali sosai a kan aikin kare ikon mallakar ilmi da kasar Sin take yi. Kasar Sin tana kokari sosai wajen kare ikon mallakar ilmi bisa shari'a. A ran 27 ga wata, hukumomin da abin ya shafa na kasar Sin sun bayar da wata sanarwa cikin hadin gwiwa da nufin kara ingancin aikin kare ikon mallakar ilmi bisa shari'a.

Game da kare ikon mallakar ilmi, kasar Sin tana gudanar da wannan aiki bisa hanyoyi biyu. Idan aka karya ikon mallakar ilmi maras tsanani, gwamnatoicin daban daban za su iya yankewa mai laifin masa hukuncin tara, amma idan aka karya ikon mallakar ilmi kuma ya aikata laifin da ya saba wa doka, to, za a gurfana da shi a gaban shari'a. A ran 27 ga wata, hukumar koli ta bin bahasi ta jama'ar kasar Sin da ma'aikatar tsaron zaman lafiyar jama'a ta kasar Sin da kuma ma'aikatar sa ido da bincike ta kasar Sin sun bayar da wata sanarwa mai suna 'game da kai wadanda suka aikata laifin karyan ikon mallamar ilmi a gaban shari'a'. Mataimakin shugaban hukumar koli ta bin bahasi ta jama'ar kasar Sin Zhu Xiaoqing ya bayyana cewa,

'Don hana gwamnatoci za su iya yankewa wadanda suka aikata laifi hukunci wajen karya ikon mallakar ilmi, amma gwamnatocin ba za su kai su gaban shari'a ba, don haka aka bayar da wannan sanarwa. Wannan sanarwa tana da muhimmanci sosai wajen kai babban naushi ga wadanda suka aikata laifin karya dokar ikon mallakar ilmi, da kara kare ikon mallakar ilmi bisa shari'a.'

Tun daga kasar Sin ta shiga cikin kungiyar cinikayya ta duniya, hukumar ikon dabi ta kasar Sin da hukumar kasuwanci da tashoshin shigi da fice na kasar Sin su kan gama kansu cikin yakini wajen kai naushi a kan wadanda suka karya dokar ikon mallakar ilmi. Sabo da haka, a shekarar 2004, yawan shari'a da aka yi wa masu laifin karya dokar ikon mallakar ilmi ya karu sosai. Amma ya kasance da matsaloli da dama a yayin da gwamnatoci suke kai masu laifin karya dokar ikon mallakar ilmi. Sanarwar da aka bayar ta ba da amsa mai kyau game da wadannan matsaloli da muka ambata wannan hukunci, Malam Zhu ya ce,

'Muna da matakai da yawa, na farko, muna sa ido a kan gwamnatoci daban daban domin ganin ko suna kai masu laifi a gaban shari'a ko a'a, idan muka ga gwamnatocin ba su kai masu laifi a gaban shari'a ba, to, za mu bin bahasin nauyin da ke bisa wuyansu. Na biyu, idan ma'aikatan gwamnatocin suka hana a kai masu laifi a gaban shari'a, to, za a gurfanar da shi a gaban shari'a.'

Bangaren 'yan sanda yana taka wata muhimmiyar rawa wajen kare ikon mallakar ilmi, mai ba da taimako ga ministan tsaron zaman lafiyar jama'a na kasar Sin Zheng Shaodong ya bayyana cewa, sanarwar za ta sa kaimi ga 'yan sanda da su gudanar da ayyukansu na kai naushi ga wadanda suka aikata laifin karya dokar ikon mallakar ilmi.

Karya ikon mallakar ilmi musamman yin kayayyakin jebu ya zama wata matsala a duk duniya. Gwamnatin kasar Sin tana kokari a kan kai naushi gare su ba tare da kasala ba. A cikin shekaru 5 da suka gabata, kasar sin ta kwace kayayyakin Vedio da littattafai da yawansu ya kai miliyan 457, a cikin shekarar bara, an kwace da lallata kayayyakin da yawansu ya zarce miliyan 100. Mataimakin shugaban hukumar ikon dabi ta kasar Sin Yan Xiaohong ya bayyana cewa, kare ikon mallakar ilmi yana bukatar lokaci, amma ana iya rage wannan lokaci. Ya ce,

'Ya kamata mu kara nazarin mataikan da za a dauka wajen kai babban naushi ga wadanda suka aikata laifi domin kawar da matsalar karya dokar ikon mallakar ilmi. A matsayin wata kasa mai tasowa, kasar Sin tana bukatar lokaci domin kare ikon mallakar ilmi, kasashe masu sukuni su ma sun taba yin wannan tafiya. Game da kasar Sin, muna fata za a iya rage wannan lokaci bisa yiyuwa, amma da kyar a kawar da matsalar nan cikin wani gajeren lokaci.'(Danladi)