Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-27 17:24:57    
Sashen kasashen waje na makarantar midil ta Huiwen ta Beijing

cri

A shekarun baya da suka wuce, saboda kasar Sin ta daga matsayinta wajen ilmi mai zurfi da kuma kara ba da tasiri a tsakanin kasashen duniya, mutanen kasashen ketare masu yawa sun zo kasar Sin don yin karatu a jami'o'i, haka kuma, wasu sun yi karatu a makarantun midil a kasar. Don ba da sauki ga 'yan makarantun midil masu dalibta cin jarrabawar shiga jami'o'in kasar Sin lami lafiya, hukumomin ilmi na kasar Sin sun kafa makarantun midil na kasashen waje a wasu manyan birane. A cikin shirinmu na yau na "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya", za mu gabatar muku da sashen kasashen waje na makarantar midil ta Huiwen ta Beijing.

Makarantar midil ta Huiwen ta Beijing, wata shahararriyar makaranta ce da gwamnatin kasar ta kafa a shekaru fiye da 130 da suka wuce. Ta kafa sashen kasashen waje a shekaru 12 da suka gabata, don daukar 'yan makarantun midil na kasashen waje.

Wani sabon babban gini da ke arewacin wannan makarantar midil sashe ne na 'yan makarantun midil na kasashen waje. Yanzu suna koyon Sinanci. "sannu! Yauwa sannu! Yau bari mu fara daga darasi na 14?"

Hanyar da malaman wannan makaranta suke bi wajen ba da ilmi ta sha bamban da ta sauran makarantun midil a kasar. Dalibai 20 sun kafa rukunnoni daban daban a lokacin karatu. Tare da taimakon malamansu, wadannan 'yan makarantu 4 ko 5 sun kafa wani rukuni sun zauna tare sun karanta darasi sun duba kamus sun yi tattaunawa tare, lokaci-lokaci kuma sun saurari malamansu a tsanake, sun ji dadin karatu sosai.

Madam Zhang Shunzhi, malama ce da ke koyon Sinanci a nan, ta gabatar da cewa, koyon ilmi cikin rukunnoni daya ne daga cikin matakan da makarantar midil ta Huiwen take dauka don sajewa da al'adun kasashen waje a fannin karatu da kuma kwarewar fahimtarsu."babban makasudi na yau shi ne sabawa darasin da muke koyo, wato kawar da cikas wajen koyon kalmomin da aka tanada cikin wannan darasi. Dalibai sun yi karatu cikin rukunnoni, za su fi koyon ilmi da kansu, kuma rukunoninsu za su taka rawa, ban da wannan kuma, za a yi tsimin lokaci, a ganina, za a sami sakamako mai kyau."

Muhimmin makasudin makarantar midil ta Huiwen shi ne yin kokarin samar wa 'yan makarantu da hanyoyin zamani wajen koyarwa da yin karatu, da kuma hali mai kyau da suke ciki wajen yin karatu, ta yadda za su iya cika burinsu na shiga shahararrun jami'o'in kasar Sin, kuma za su zama gwanaye daga duk fannoni. Shi ya sa, darektar sashen kasashen waje na makarantar midil ta Huiwen madam Jin Jie ta ba da karin haske cewa, "mun samar da darussa ne don taimakawa 'yan makarantu cin jarrabawar shiga shahararrun jami'o'in kasar, wannan babban makasudinmu ne, amma ban da wannan kuma, muna fatan za su iya wasu fasahohi."

Malaman makarantar midil ta Huiwen sun koyar da dalibai na kasashen waje abubuwan da a kan jarraba a cikin jarrabawar shiga jami'o'in kasar, ta yadda 'yan makaranta za su iya samun maki mai kyau, za su cika burinsu. Sa'an nan kuma, ta dora muhimmanci kan Sinanci da Turanci da ilmin naurori masu aiki da kwakwalwa da dai sauransu, ta kuma horar da kwarewar 'yan makaranta ta hanyar yin ayyukan zaman al'umma da kuma yawon shakatawa cikin himma da kwazo. Dalibai sun kara yin maraba da ra'ayin da makarantar Huiwen take rike da shi wajen koyarwa.

Bisa adadin kididdigar da ma'aikatar ilmi ta kasar Sin ta bayar, an ce, a shekarun nan da suka wuce, yawan daliban kasashen waje masu dalibta yana ta karuwa a ko wace shekara a kasar Sin, a cikin shekarar 2004 da ta gabata, jimlarsu ta kai fiye da dubu 110, wadda ta karu da kashi 42 cikin dari in an kwatanta da ta shekarar 2003, daga cikinsu yawan 'yan makarantun midil na kasashen waje da suke yin karatu a kasar Sin ya kuma karu sosai. Yanzu akwai makarantun midil gomai kamar yadda sashen kasashen waje na makarantar midil ta Huiwen yake a nan Beijing, tun daga shekarar 1994 har zuwa yanzu 'yan makaranta fiye da dubu 3 daga kasashe 30 ko fiye sun taba yin karatu a sashen kasashen waje na makarantar midil ta Huiwen. Dukan wadannan 'yan makaranta sun shiga jami'o'in kasar Sin ne bayan da suka gama karatu, a cikinsu kuma kashi 80 cikin dari nasu sun shiga shahararrun jami'oin kasar, kamarsu Jami'o'in Beijing da Tsinghua.

To, masu sauraronmu, wannan shi ya kawo karshen shirin 'kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya' daga nan sashen Hausa na Rediyon na Kasar Sin, *** ne ke cewa ku huta lafiya.