Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-27 16:38:14    
Shagalin wasan kwallon kwando na CBA ya zama wani kasaitaccen biki a kasar Sin

cri

A shekarun nan da suka wuce, rukunin wasan kwallon kwando na kasar Sin yana koyon fasahohin da mutanen kasar Amurka suka samu a fannin wasan kwallon kwando a tsanake, Hadaddiyar Kungiyar Wasan Kwallon Kwando ta kasasr Sin ta shirya hadaddiyar gasar ta wasan kwallon kando ta CBA a shekaru 11 da suka wuce, bisa fasahohin da ta yi koyi daga hadaddiyar gasar wasan kwallon kwando ta NBA ta kasasr Amurka a fannoni masu yawa, yanzu hadaddiyar gasar CBA ta zama hadaddiyar gasa ce ta koli kuma mafi ba da tasibi a yankin Asiya. Shagalin wasan kwallon kwando na CBA da aka saba shiryawa karshen mako sau daya a ko wace shekara, ya zama wani kasaitaccen biki ne ga masu son wasan kwallon kwando na kasar Sin, kamar yadda shagali na NBA yake.

Ran 17 ga watan Maris, ran Jama'a. A ran nan da yamma, an bude shagalin wasan kwallon kwando na CBA na shekarar 2006 a birnin Shanghai.

Kamar yadda a kan yi a da, an yi kwanaki 3 ana yin shagalin wasan kwallon kwando na CBA da aka saba shiryawa a karshen mako, wanda ke kunshe da kashi biyu, wato gasar wasan kwallon kwando ta dukan shahararrun 'yan wasan kwallon kwando da aka yi tsakanin kungiyoyin yankin arewacin kasar da yankin kudancin kasar a ran 18 ga watan Maris da dare, da kuma harkokin wasanni da aka shirya ga masu son kwallon kwando. An fi dora muhimmanci kan masu son kwallon kwando da su sa hannu cikin shagalin a wannan gami, an jaddada cewa, wajibi ne wannan shagali ya faranta wa masu son kwallon kwando rai, haka kuma, al'ummar kasar. Shi ya sa, babbar kirar da aka yi a wannan shekara ita cewa, 'kamunka ke nan yanzu, kai tauraro ne.', wato 'it's your turn?you are the star.' A bakin Turawa.

Saboda an shirya sosai, shi ya sa, a cikin kwanaki 3 da suka wuce, masu son wasan kwallon kwando na Shanghai dubu gomai sun shiga wannan shagali sun ji dadinsu sosai.

A ran 18 ga watan Maris da dare, an yi gasar wasan kwallon kwando ta dukan shahararrun 'yan wasan kwallon kwando. Filin wasa na Shanghai da ake yin wannan gasa cike yake da masu son wasan kwallon kwando misalin dubu 10, kungiyoyi 2 sun yi takara mai tsanani sosai, gwanintarsu sun samu ban tafi daga 'yan kallo, a karshe dai, kungiyar yankin kudancin kasar Sin ta lashe kungiyar yankin arewacin kasar da cin 93 da 90.

A cikin dukan gasannin wasan kwallon kwando na dukan shahararrun 'yan wasan kwallon kwando da aka yi a da, akwai abubuwan da aka tuna da su cikin zukatan mutane. A cikin gasar da aka yi a shekarar 1997, dan wasa da ke baya mafi nagarta a Asiya Hu Weidong ya sami maki 44, a cikin gasar da aka yi a shekarar 2001, Yao Ming ya ba da taimako ga wani yaro da ya burma kwallo, dukan 'yan kallo sun ba da tausayi. A cikin gasar da aka yi a shekarar da muke ciki, dan wasan da ke gaba-gaba Hu Guang ya ci nasara sau 3 a jere a cikin gasar burma kwallo, ya zama dan wasa ne na farko da ya ci nasara sau 3 a jere a cikin gasar burma kwallo tun bayan da aka fara gasar wasan kwallon kwando ta dukan shahararrun 'yan wasan kwallon kwando har zuwa yanzu. Ban da wannan kuma, dan wasa na kasar Amurka Join Smith da ke aiki cikin kungiyar Honghe ta Yunnan ya zama dan wasan kwallon kwando mafi nagarta a wannan gami, wannan ne karo na farko da 'yan wasan kasashen waje suka zama 'yan wasan kwallon kwando mafi nagarta.

Bayan gasar, Mr. Smith ya bayyana cewa, lambar yabo ta dan wasan kwallon kwando mafi nagarta lamba ce mai muhimmanci a cikin rayuwarsa a fannin wasannin motsa jiki.(Tasallah)