Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-24 17:18:45    
Kasar Sin ta zama memba mai kokari a cikin kungiyar WTO

cri

Jama'a masu karatu, barkanmu da sake saduwa a cikin shirinmu na yau na Bunkasuwar kasar Sin. A ran 18 ga wata Lahadi an rufe taron koli na kungiyar cinikayya wato WTO na 6 a Hong Kong. A gun taron, an samu wasu cigaba kan maganganun aikin gona da shigar da kayayyaki ba irin na amfanin gona ba a cikin kasuwanni da maganar neman bunkasuwa. A gun taron, kasar Sin ta yi kokari sosai domin halartar shawarwari iri iri, kuma ta bayar da ra'ayin yin cinikin waje cikin adalci. Abubuwan da kungiyar wakilan kasar Sin ta yi a gun taron sun jawo hankulan mutane kwarai. Wasu masana sun bayyana cewa, a cikin shekaru 4 da suka wuce bayan da shigowar kasar Sin a cikin kungiyar WTO, kasar Sin ta kara samun fasahohin yin shawarwari a tsakanin bangarori da yawa a kai a kai. A sa'i daya, tana cika alkawari da bude wa kasashen waje kofar kasuwanninta. Yanzu ta riga ta zama wata memba mai kokari a cikin kungiyar WTO.

Lokacin da yake tabo maganar yadda kasar Sin ta yi a gun taron koli na kungiyar WTO da aka yi a Hong Kong, Mr. Pascal Lamy, babban direktan kungiyar WTO ya bayyana cewa, "Kasar Sin tana da wayo kwarai wajen yin shawarwari. Yadda za a yi shawarwari wata tsohuwar fasaha ce a kasar Sin tun daga shekaru aru aru da suka wuce."

Ko da take matsayin uwar taron, kasar Sin ta bayar da ra'ayinta cewa, ya kamata a fi mai da hankali kan moriyar yawancin membobi masu tasowa. A gun taron Hong Kong, kungiyar wakilan kasar Sin ta yi kira ga membobin kungiyar WTO da su ba kasashe matalauta 49 shigar da kayayyaki ba tare da sun biya kudin kwastanm da kaso ba.

A gun taron, lokacin da ya tabo ra'ayoyin da kasar Sin ta bayar, Mr. Bo Xilai, ministan kasuwanci na kasar Sin ya ce, "Lokacin da ake yunkurin yin cinikin waje cikin 'yanci a duk fadin duniya, dole ne a mai da hankali kan moriyar yawancin membobi masu tasowa. A sakamakon haka, yawancin membobi masu tasowa za su iya samun damar kama sahun sauran kasashen duniya. Sabo da haka, dole ne a mai da hankali kan halin musamman da membobi masu tasowa ke ciki kuma a bambamta halaye daban-dabam na membobi masu sukuni da na membobi masu tasowa."

Ra'ayin kasar Sin wani lamiri mai kyau ne ga manoma matalauta na membobi masu tasowa. Kamar yadda sauran membobi wadanda suke da mutane masu yawan gaske kuma da bambance-bambamce a tsakanin yankuna da sana'o'insu suke ciki, matsakaicin yawan kudin shiga na kowane Basine ya yi kadan wato ya kai dalar Amurka 1400 kawai. Bugu da kari kuma, yawancin mutanen kasar Sin manoma ne. Yawan mutane matalauta ya kai miliyan dari 2 a nan kasar Sin. Mr. Bo Xilai ya nuna cewa, ko da yake har yanzu kasar Sin tana fama da matsaloli iri iri, amma tana bayar da gudummawarta kwarai ga duk duniya. A shekara ta 2005, darajar yawan kayayyakin da za a shigo da su a kasuwannin kasar Sin za ta kai dalar Amurka wajen biliyan dari 6, wannan ya yi alamantar da cewa kasar Sin wata babbar kasuwa ce ga sauran kasashen duniya. Hakazalika, gwamnatin kasar Sin ta riga ta shelanta cewa, ta yafe wa kasashe matalauta dukkan basusukan da kasar Sin ke bin su kafin karshen shekara ta 2005.

Ko da kasar Sin ta fi shan wahalar ra'ayin kare cinikin waje a duk duniya, a gun taron Hong Kong, kasar Sin ta kuma nemi membobin kungiyar WTO da su amince da cikakken matsayin takarar harkokin kasuwanci da kasar Sin take bi. Tana kuma fatan za a kara gyara matakan fama da yunkurin sayar da kayayyaki da farashi mai arha da ake yin amfani da su yanzu domin hana yin irin wadannan matakai ba bisa doka ba.

Lokacin da take halartar aikin tsara ka'idojin cinikayya na kungiyar WTO, kasar Sin tana kuma cika alkawuran da ta dauka lokacin da aka shigo da ita a cikin kungiyar WTO. A cikin shekaru 4 da suka wuce, kasar Sin ta riga ta rage harajin kwastam har sau 4. Kafin shigowarta a cikin kungiyar WTO, jimlar harajin kwastam ta kasar Sin ta kai kashi 15.3 cikin kashi dari, amma yanzu ta kai kashi 9.9 cikin kashi dari kawai. A sakamakon haka, darajar kayayyakin da aka shigo da su a kasuwannin kasr Sin ta karu da ta kai kashi 30 cikin kashi dari a kowace shekara. Kan yadda kasar Sin take bin ka'idojin kungiyar WTO yadda ya kamata, Mr. Bert Hofman, wakilin farko na Bankin Duniya da ke zaune a nan birnin Beijing ya ce, "A cikin 'yan shekarun nan, an yaba wa gwamnatin kasar Sin sosai domin lokacin da take fuskantar cecekucen cinikayya, kasar Sin ta kan yin kokari domin daidaita irin wannan cecekuce bisa ka'idojoin kungiyar WTO. Ko da yake mai yiyuwa ne kasar Sin ba ta iya samun kyakyawan sakamako a wasu lokuta ba."

Bugu da kari kuma, kasar Sin tana kokari wajen budewar kasuwanninta ga sauran kasashen duniya a kai a kai. Mr. Bo Xilai, ministan kasuwanci na kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da bude kasuwanninta ga sauran kasashen duniya bisa matakan da ta tsara a nan gaba. Kuma za ta kara halartar yunkurin bunkasa tattalin arzikin duniya bai daya.(Sanusi Chen)