Ran 22 ga wata, an rufe taron dandalin tattaunawa kan batun ruwa na duniya na karo na hudu wanda hukumar kula da harkokin ruwa ta duniya da gwamnatin kasar Mexico suka shirya cikin hadin guiwarsu a birnin Mexico. Wakilai mahalartan taron sun sami ra'ayi daya a kan cewa, samun ruwa mai inganci babban hakkin duk 'yan adam ne. Wannan yana da matukar muhimmanci ga hadin guiwar kasa da kasa don kare albarkatun ruwaye.
An shafe wani mako ana yin wannan taron dandalin tattaunawa kan batun ruwa na duniya, babban taken taron nan shi ne "daukar matakai a wurare daban daban don magance kalubale a duk duniya". Wakilai sama da dubu goma wadanda suka fito daga kasashe da shiyyoyi sama da 100 ciki har da kasar Sin sun yi tattaunawa sosai ga manyan batutuwa biyar kamar bunkasuwar tattalin arziki da kyautata yin amfani da ruwa da kulawa da albarkatun ruwaye daga duk fannoni da dai sauransu.
Wakilai ministoci na kasashe sama da 50 da wakilan kungiyoyin kasa da kasa sun shirya taron ministoci tun daga ran 21 zuwa ran 22 ga wata, sun yi musanyan manufofi da kasashe daban daban ke bi game da yadda ake kare albarkatun ruwa da yin amfani da su yadda ya kamata, sa'an nan kuma sun zartas da "Sanarwar Ministoci" a ran 22 ga wata. A cikin sanarwar, an jaddada cewa, wajibi ne, samun ruwa mai inganci aikin gwamnati ne, musamman ma zai zama babbar manufa da kasa da kasa ke bi wajen neman samun ci gaba mai dorewa. Haka nan sanarwar ta sa kaimi ga kasashe daban daban da su ci gaba da daukar matakai wajen tabbatar da manufar bunkasuwa ta shekaru 1000 ta majalisar dinkin duniya, wato yawan mutane marasa samun ruwa mai inganci zai ragu da rabinsu a shekarar 2015.
Abin da ya cancanci a ambata shi ne, kasashen Asiya da shiyyar tekun Pacific sun kara karfin hadin guiwarsu wajen kula da albarkatun ruwaye. A lokacin taron dandalin tattaunawar nan, wakilai da suka fito daga kasashen Asiya da shiyyar tekun Pacific sama 10 kamar Sin da Japan da Korea ta Kudu da New Zealand da Singapore da sauransu sun shirya taron ministocin tsare ruwa na Asiya da shiyyar tekun Pacific, kuma sun sami ra'ayi daya a kan yin taron dandalin tattaunawa kan batun ruwa na Asiya da shiyyar tekun Pacific. Haka zalika jami'ai masu kula da harkokin ruwa na gwamnatocin kasashen Sin da Japan da Korea ta Kudu da kwararrunsu sun shirya taron cikin hadin guiwarsu, kasashen nan uku suna fatan za su kara yin musaye-musaye da kara karfin hadin guiwa a tsakaninsu da gamayyar kasa da kasa a fannoni daban daban.
Rawar da kasar Sin ke takawa wajen kare albarkatun ruwaye da yin amfani da su da ra'ayoyinta kullum sai kara jawo hankulan gamayyar kasa da kasa yake yi. Ko da yake yawan ruwaye da kasar Sin take da su ya kai kashi 6 cikin dari bisa na duniya a yanzu, fadin filayen gonakinta kuma ya kai kashi 9 cikin dari bisa na duniya, amma kasar Sin tana amfani da su wajen ciyar da mutane da yawansu ya dauki kashi 22 cikin dari bisa na duniya. Sa'an nan kuma ta sami babban ci gaba wajen bunkasa harkokin tattalin arziki da zaman jama'a har ba a taba ganin irinsa ba a da, wannan babban taimako ne da kasar Sin ta bayar ga samar da zaman lafiya da bunkasuwa a duniya. Malam Wang Shucheng, ministan tsare ruwa na kasar Sin ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai ga matsaloli da aka gamu da su a fannin ruwaye, tana kyautata hanyoyi da take bi wajen tsare ruwa bisa manufar neman samun ci gaba mai dorewa, ku ma ta sami sakamako a zahiri. Yayin da ake bunkasa aikin tsare ruwa, gwamnatin kasar Sin ta mayar da aikin samar wa jama'a ruwa mai inganci bisa matsayin babban dawainiyarta, ta riga ta daidaita matsalar samar da ruwan sha mai inganci ga manoma da yawansu ya kai miliyan 67 a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, sa'an nan kuma za ta kara samar da ruwan sha mai inganci ga mutane miliyan 100 a cikin shekaru 5 masu zuwa. Ya kara cewa, kasar Sin za ta cim ma manufar samun bunkasuwa na shekaru 1000 na majalisar dinkin duniya kafin shekarar 2015. (Halilu)
|