Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-23 16:30:00    
wata wasika daga mai sauraronmu

cri

Jama'a masu sauraro, barka da war haka, kuma barkanmu da sake saduwa da ku a wani sabon shirinmu na amsoshin wasikunku. Ni ce Lubabatu ke gabatar muku da wannan shiri kuma ke yi muku sallama daga nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin da ke nan birnin Beijing. Masu sauraro, a cikin shirinmu na yau, zan karanto muku wata wasika da ta fito daga hannun wani mai sauraronmu na kullum, wato Malam.Salisu Muhammad Dawanau daga birnin Abuja, inda ya nuna yabo a kan shirye-shiryenmu da kuma ba mu wasu shawarwari masu matukar kyau dangane da shirye-shiryenmu. To, yanzu, sai ku saurara yadda wannan wasika ta kasance.

A cikin wasikar, Malam.Dawanau ya ce, ko shakka babu, yabon gwani ya zama dole. Gidan rediyon kasar Sin ya cancanci yabo, domin ya taimaka kwarai da gaske wajen fadakarwa da wayar da kai da ilmantarwa da kuma fahimtar da mutanen wasu kasashe dangane da gaskiyar abubuwan da suke faruwa a kasar Sin da kuma nahiyar Asiya baki daya.

Bugu da kari, wannan gidan rediyo ya taimaka wajen fito da kasar Sin da Sinawa a idanun duniya ta yadda duk mutum mai hankali zai fahimta, kuma ta hanyar wannan gidan rediyo, kasar Sin ta dada kyautata kawancenta da wasu kasashen duniya a dukkan nahiyoyi, kuma wannan ya sa duk kasashen duniya yanzu suna rigegeniya wajen yin koyi da kasar Sin musamman a hanyoyin ci gaba da kuma bunkasa ta fannoni masu yawa.

A yau, miliyoyin mutane daga kasashen duniya sun kasance cikin sanin kusan duk abubuwan da ke faruwa da kuma gane manufofin kasar Sin ta kafa wannan gidan rediyo mallakar kasar Sin.

Muna iya fahimtar hakan idan muka yi la'akari da yadda gidan rediyo na kasar Sin ya dada fadada watsa shirye-shiryensa ta harsuna har arba'in da uku, ga kuma shafin gidan rediyon na internet wanda ke dauke da muhimman bayanai game da kasar Sin.

A nan, zan so in karkata akalar wannan rubutu nawa zuwa sashen Hausa na gidan rediyo na kasar Sin, wanda yawa-yawan Hausawa masu sauraren sashen da kuma masu alaka ko kuma mu'amala da harshen Hausa suka sani cewar sashen ya dade da kafuwa. Ina yi wa wannan sashe fatan ci gaba da ayyuka da ya saba, a kullum, don ya dada bunkasuwa sosai, kuma ko da yake na tabbata ba za a rasa matsaloli irin wadanda su kan taso sa'a-sa'a ba, amma na yi amanna da cewa ma'aikatan sashen suna yin kokari sosai don ganin an guje wa ko an kauce wa wadannan matsaloli yayin da suke tasowa.

Sabo da haka, a kullum na kan yaba wa ma'aikatan sashen kwarai da gaske, kuma ina da yakinin cewar yawa-yawan masu sauraren ingantattun shirye-shiryen sashen za su yarda da abin da na fada idan muka yi la'akari da irin gagarumar ci gaba da ake samu a sashen wajen gudanar da shirye-shirye masu kayatarwa da ilmantarwa tun daga kafuwar sashen fiye da shekaru arba'in da suka wuce.

A matsayina na mai sauraren sashen Hausa na gidan rediyo na kasar Sin, fata nake a kullum na ga gidan rediyon ya dada ci gaba kuma ya cimma nasarorinsa. Sabo da haka, ga wasu shawarwari masu amfani daga gare ni.

1. A kirkiro wani fili mai suna WAIWAYE ADON TAFIYA(a madadin shirin me ka sani game da kasar Sin). Sau da yawa, sai mun dubi abubuwan da suka faru a baya kafin mu yi gyara bisa abin da muke hange a can gaba.

Sabo da haka, ina ganin kirkiro wannan shirin zai taimaka don zai zamo tamkar manuni ko madubi gare mu masu saurarenku ta hanyar dada wayar mana da kai, da kuma dada fahimtar da mu wajen sanin tarihin kasar Sin da tarihin shugabannin kasar Sin wadanda suka kwanta dama, da na yanzu da kuma sanin tarihin wasu muhimman wurare da dalilin gina su ko kafuwarsu da dai sauran abubuwan da suke halarta ga masu saurarenku su sani.

A ganina, wannan shirin zai taimaka mana masu saurarenku da wadanda suke da sha'awar son sanin tarihin kasar Sin da Sinawa wajen sanin tarihin jaruman shugabanni da mutane masu kwazo wadanda su ka yi suna da fice a fannoni daban daban, da kuma wuraren da suke da dogon tarihi da muhimmanci na kasar Sin da na nahiyar Asiya baki dayanta. Kuma na tabbata wannan shiri zai samu karbuwa sosai ga masu saurarenku ta yadda har za a yi koyi da wadannan shugabanni.

2. Haka kuma, ina ganin yana da kyau in kuka fara buga wata mujalla ta sashen Hausa kamar the Messenger ta sashen Turanci ko da kuwa sau hudu ne a shekara ta yadda za ku rika yada manufofin kasar Sin, bayan shirye-shiryenku, a duniya.

3. Kuma ina ganin yana da kyau idan ku ka ba da wani fili na musamman ta yadda za ku rika karanta wasikun shawarwari da kuma ra'ayoyin masu saurarenku, a kalla sau daya a ko wane mako.

4. ya kamata ku rika yin shirye-shiryenku sau biyu a ko wace rana a madadin yadda kuke yi a yanzu.

Ku huta lafiya. Mai saurarenku a kullum,

Salisu Muhammad Dawanau

To, Malam Dawanau, a madadin dukan ma'aikatan sashen Hausa na gidan rediyon kasar Sin, ina yi maka godiya kwarai da gaske, sabo da shawarwari masu kyau da ka ba mu, haka kuma sabo da sauraron shirye-shiryenmu da kake yi a kullum. Gaskiya ne mun karu da shawarwarinka, kuma wasikarka ta karfafa mana gwiwa ta sa kaimi gare mu don mu kara kokari mu kara kyautata shirye-shiryenmu. Masu sauraro, a nan ma na yi farin ciki ina so in sanar da ku cewa, a watan Janairu na wannan shekara, wato 2006, sashen Hausa ya fitar da wata jarida a karo na farko, wadda muka sa mata suna 'ZUMUNTA', inda muka buga labarai masu yawa da suka jibinci al'adu da zaman al'umma da yawon shakatawa da dai sauran fannoni daban daban, kuma da akwai hotuna masu ban sha'awa, haka kuma mun buga wasiku masu kyau da masu sauraronmu suka aiko mana a cikin jaridar, ga shi a wannan jarida ta farko, mun buga wasikar da na karanta muku dazun nan, wato daga hannun Malam Salisu Muhammad Dawanau. Sabo da haka ne ma, muna fatan za mu kara samun wasiku daga wajen masu sauraronmu, don ku ba mu shawarwari ko ra'ayoyinku dangane da shirye-shiryenmu, ta yadda za mu inganta shirye-shiryenmu. Masu sauraro, tilas ne mu sa aya a nan. A madadin kowa da kowa, ni Lubabatu daga nan Beijing ke cewa, mu kasance lafiya.(Lubabatu Lei)