Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-23 16:07:14    
Bangarori daban daban da suke shafar batun nukiliyar kasar Iran suna fuskantar babban zabe

cri
An riga an yi makonni biyu da  sanar wa kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya batun nukiliyar kasar Iran, amma zaunannun kasashe biyar da ke Majalisar Dinkin Duniya har wa yau dai ba su yi rangwame a tsakaninsu a kan batun ba. 'Yan kallo suna ganin cewa, yanzu, bangarori daban daban suna fuskantar zabi mai muhimmanci, sakamakon da za a samu zai ba da muhimmanci ga makomar batun nukiliyar kasar Iran.

A ran 20 ga wannan wata, kasar Amurka da Rasha da Sin da kuma kasar Jamus da Britaniya da Faransa da ke cikin kawancen kasashen Turai sun yi shawarwari a kan batun nukiliyar kasar Iran a birnin New York, amma bangarorin daban daban ba su sami ra'ayi daya ba. Kasar Amurka da Britaniya da Faransa da Jamus sun bayar da ra'ayinsu cewa, ya kamata kwamitin sulhu ya  zartas da wata sanarwar shugaba , game da wannan, kasar Britaniya da kasar Faransa sun kuma gabatar da daftarin shirin sanarwar shugaba. kan haka , wakilan kasar Rasha da kasar Sin sun gabatar da ra'ayoyinsu masu banbamci a fannoni biyu. Da farko, daftarin shirin nan ya nemi babban jami'in hukumar makamashin nukiliya  ta duniya da ya sake gabatar wa kwamitin sulhu sabon ci gaban da kasar Iran take samuwa a kan batun nukiliya a cikin kwanaki 14 ta yadda kwamitin sulhu zai kara daukar matakai. Kasar Rasha da kasar Sin suna ganin cewa,  lokacin da aka kayyade ya yi kadan ga daidaita batun . An labarta cewa, Kasar Rasha ta yi fatan za a tsaiwaita lokacin zuwa watan Yuni don Majalisar hukumar makamashi ta duniya ta sake kiran taronta. Sa'anan kuma, sabanin da ke tsakanin kasashen biyu wato kasar Rasha da Sin da kasashe hudu na yamma suna kasancewa ne a kan amfanin da hukumar makamashi ta duniya ta yi a halin yanzu. Bangaren kasar Sin da Rasha suna ganin cewa, an sanar da batun nukiliyar kasar Iran ga kwamitin sulhu ne kawai, wannan na da bambanci da gabatar da aka yi ga kwamitin .Saboda haka, ya kamata kwamitin sulhu ya ci gaba da ba da goyon baya ga aikin hukumar makamashi ta duniya, amma bai kamata a maye gurbinsa ba, kuma a ci gaba da daidaita batun nukiliyar kasar Iran bisa tsarin hukumar kuma ta hanyar diplomasiya.

Na biyu, kasar Iran har wa yau dai tana nacewa ga bin manufarta ta rashin nuna rangwame. Wasu masu binciken batun suna ganin cewa, wannan ba ma kawai ya kawo wa kasashe uku wato kasar Britaniya da Jamus da Faransa wadanda suke shiga aikin sulhuntawa kai tsaye bakin ciki ba, hatta ma ta sa babban jami'in hukumar makamashi ta duniya Mohamed Baradei wanda ke bisa matsayin 'yan ba ruwanmu ya kasa hakuri, taurin kai da kasar Iran take yi ya sa kawancen kasashen Turai sun shiga jerin Amurka ta yadda za su yi ta yin hadin guiwa a tsakaninsu, kuma ta sa kasar Amurka ta sake samun damar ba da jagoranci ga daidaita batun nukiliyar Iran daga baya zuwa gaba. Ra'ayoyin jama'ar Turai suna ganin cewa, an riga an rufe tagar kasar Iran ta neman damar samun fa'ida ta hanyar yin amfani da sabanin da ke tsakanin kasar Amurka da kasashen Turai, idan gardamar da ke tsakanin kasar Amurka da kasar Iran kan batun nukiliya ta zama rikicin soja, to ba za a iya kawar da ra'ayi daya da kasashen Turai da kungiyar tsaron Nato za su samu ba.

Kwanan nan, kasar Amurka tana kara karfin niyyarta. A cikin wani rahoton da shugaba W.Bush ya bayar a ran 16 ga wannan wata, ya bayyana cewa, kasar Iran babban kalubale ne ga kasar Amurka. A cikin kasar , wasu mutane suna ganin cewa, a kan batun nukiliyar kasar Iran, halin da ake ciki ya yi tamkar yadda halin da ake ciki kafin barkewar yakin kasar Iraki.

Amma, kasar Iran tana da nata kimantawa mai faranta rai a kan halin  da ake ciki yanzu, a ganinta, kasar Amurka ba za ta iya samun isasshen karfi daga gida da waje ba don nuna goyon baya ga farmakin soja da za ta yi wa kasar Iran  .

Amma mutane da yawa suna ganin cewa, idan kasar Amurka da kasar Iran ba su yi wa juna rangwame ba, to bangarorin biyu ba za su kawar da hargitsin da ke tsakaninsu ba.(Halima)