Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-22 16:32:01    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(16/03-22/03)

cri
An rufe wasannin Olympic na nakasassu na yanayin hunturu na karo na 9 a birnin Torino na kasar Italiya a ran 19 ga wata, bisa agogon wurin. Wasannin Olympic na nakasassu na yanayin hunturu kasaitaccen wasanni ne na koli da kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na duniya ya shirya wa dukan nakasassu na duk fadin duniya. 'Yan wasa nakasassu fiye da dari 6 daga kasashe da yankuna 39 sun shiga wannan wasanni, ta haka, an samar da sabon matsayin bajimta wajen yawan kungiyoyin wakilan kasashe da kuma yawan 'yan wasa. An kafa manyan gasanni 5 da kuma kananan gasanni 58 a wannan gami. Kungiyar wakilan kasar Sin ba ta sami lambobin yabo a wannan gami ba, a cikin dukan 'yan wasa 7 masu shiga wannan wasanni, Han Lixia wata mahauniya ta zama ta 7 a cikin gasar wasan skiing a tsakanin duwatsu mai tsawon kilomita15 ta mata. Kasashen Rasha da Jamus da Ukraine sun fi samun lambobin zinare a wannan gami. Za a yi wasannin Olympic na nakasassu na yanayin hunturu na karo na 10 a birnin Vancouver na kasar Canada a shekarar 2010.

Ran 15 ga wata, mutanen kasar Sin kimanin dubu 10 sun ji dadin ganin kofin duniya na Hadaddiyar Kungiyar Wasan Kwallon Kafa ta Duniya wato FIFA da idanunsu a cikin Jami'ar Beijing, wanda karo ne na farko da aka nuna kofin duniya ga al'ummar kasar Sin. Dukan masu ziyara sun iya daukan hoto tare da wannan kofi ba tare da biyan kudi ba, kuma nan take sun iya samun hotuna. Ban da wannan kuma, masu ziyara sun iya kallon sinimar da ta shafi gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa da kuma halartar wasanni a jere. Wannan ne karo na farko da kofin duniya ta zo kasar Sin, nuna kofin duniya a nan Beijing wani kashi ne na 'ziyarar kofin duniya na kungiyar FIFA a duk duniya'.

Ran 16 ga wata, a birnin Zurich na kasar Switzerland, kungiyar FIFA ta tsai da kudurin kara karfin yanke hukunci ga ra'ayin wariyar al'umma ko kuma harkokin nuna bambanci a cikin gasannin wasan kwallon kafa. Kungiyar FIFA ta ba da wata sanarwa a ran nan cewa, nan gaba idan wata kungiya ta saba dokoki sun nuna ra'ayin wariyar al'umma ko kuma yin harkokin nuna bambanci, to, za a kwace mata maki 3 da ta samu a cikin hadadiyyar gasa, idan ta sake saba dokoki, za a kwace mata maki 6, idan ta yi ta yin hakan, to, za a kankantar da ita daga hadadiyyar gasar da take ciki, har ma za a hana ta ci gaba da yin gasa . Za a hana kasar da wannan kungiya take ciki ta shiga gasannin duniya har shekaru 2. A shekarun nan da suka wuce, kungiyar FIFA ta dora muhimmanci kan nuna kiyewa ga ra'ayin wariyar al'umma ko kuma harkokin nuna bambanci, ta jaddada cewa, dukan 'yan Adam sun iya yin wasan kwallon kafa ba tare da yin la'akari da al'ummominsu da fatansu da kuma addinan da suke bi.

Akwai wani labari daban da ya shafi kungiyar FIFA, an ce, ko da yake an yi kirar jinkirtar da yin rajista domin gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta shekarar 2006, amma a ran 16 ga wata, kungiyar FIFA ta tsai da kudurin ci gaba da bin shirin da ta tsara a da, wato za a kammala aikin yin rajista a ran 15 ga watan Mayu na shekarar da muke ciki, a lokacin nan tilas ne kungiyoyi masu shiga gasa za su gabatar da sunayen 'yan wasa 23 da za su shiga gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta shekarar 2006.(Tasallah)