A ran 20 ga wannan wata a nan birnin Beijing, wasu shahararrun masanan tattalin arziki na kasa da kasa sun bayyana a gun wani taro cewa, a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, tattalin arzikin kasar Sin ya sami sakamakon da ya jawo hankulan mutane sosai, karuwar da ta samu a kowace shekara ta kai kashi 9 cikin dari. Amma, ya kasance da matsaloli wajen albarkatan halittu da muhalli da bambancin birane da kauyuka a lokacin da ta raya tattalin arzikinta, tana fuskantar kalubale a fannoni da yawa a lokacin da ta ci gaba da bunkasuwarta.
A gun taron dandalin manyan jami'ai na raya kasar Sin da ake shirya yanzu a nan birnin Beijing, shugaban bankin raya Asiya Haruhiko Kuroda ya ba da tabbaci mai yakini ga sakamakon da kasar Sin ta samu a cikin shekaru fiye da 20 da suka wuce, ya bayyana cewa, a cikin shekaru 25 da suka wuce, halin da kasar Sin take ciki wajen raya tattalin arziki ya jawo hankulan mutane sosai da sosai, kwatankwacin karuwar GDP ya kai kashi 9.6 cikin dari, kwatankwacin karuwar cinikayya da ta yi da kasashen waje ya kai kashi 14.6 cikin dari. Kasar Sin ta riga ta zama ko za ta ci gaba da zama karfin ingizawa mai muhimmanci ga wadatar da shiyyar Asiya da tekun Pasific.
Babban shugaban kamfanin Fedex kuma babban shugaban farko na zartaswa na kamfanin na tarayyar Amurka Frederick Smith ya bayyana cewa, a cikin lokacin da bai kai shekaru 30 ba, karuwar tattalin arziki da kasar Sin ta samu ta samar wa jama'ar kasar Sin babbar fa'ida. Mutane dubu dubai sun kubutar da kansu daga wajen talauci, zaman rayuwarsu ya kara kayutatuwa, wannan ba wanda ke iya tsammanin haka ya ba.
Shahararrun masanan tattalin arziki na kasa da kasa wadanda suke halartar taron sun bayyana cewa, karuwar tattalin arzikin kasar Sin cikin zaman karko da lami lafiya ita ma ta jawo sha'awar 'yan kasuwa na kasashen waje wajen zuba jari da yawa ga kasar Sin, wannan kuma ya yi sassaucin matsin da ta samu wajen samar da aikin yi, a sa'I daya kuma ta ba da tasiri mai yakini ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya.
Wani mashahurin masanin tattalin arziki kuma shehun malamin jami'ar Golumbiya ta kasar Amurka wanda kuma ya taba samun lambar yabo na Nober a fannin tattalin arziki Joseph Stiglitz ya samar wa gwamnatin kasar Sin shawara cewa, ya kamata ta ci gaba da daidaita huldar da ke tsakanin bunkasuwar tattalin arziki da muhalli a lokcin da ta tsara shirin raya kasa na nan gaba, ya bayyana cewa, bukatun kasar Sin sai kara daguwa suke yi wajen muhalli a lokacin da take raya tattalin arziki. Yawan karfe da sumunti da take amfani da su ya kai kashi 28 da kashi 30 cikin dari bisa na duk duniya , wannan ya kawo matsi mai tsanani ga muhallinta, samun dauwamammen ci gaban kasar Sin yana da nasaba da karfinta wanda ko zai iya daidaita wadannan batutuwan muhalli ko 'a'a.
Masanin tattalin arziki na farko na Morgan Stanley Mr Stephen Roach ya gabatar wa gwamnatin kasar Sin shawara cewa, ya kasance da wasu matsaloli a lokacin da ake jurewar hanyar zuba jari don sa kaimi ga samun karuwar tattalin arziki zuwa hanyar kara yawan saye-saye a yau da kullum don sa kaimi ga raya tattalin arziki. Kudadden da ake tanada a cikin bankuna a kasar Sin na da yawan gaske, shi ya sa yadda za a cim ma burin nan na samun jurewar ba abu mai sauki ba ne da za a iya daidaitawa.
Ayyukan da kasar Sin take yi yanzu na ba da goyon baya ga raya kauyuka sun sami amincewa daga wajen babban sakataren kungiyar yin hadin guiwar tattalin arziki na taron nan Donald J.Johnston, ya ce, shirin da kasar Sin ta tsara wajen kara zuba jari don rage bambancin birane da kauyuka da ba da ilmin tilas a fayu a cikin shekaru 9 da sauransu na da kayu sosai.(Halima)
|