Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-20 16:36:26    
Kasar Sin ta rika kara yin mu'amala da hadin gwiwa da kasashen duniya a fannin ilmi mai zurfi

cri

Jama'a masu karantawa, tun daga sabon karni har zuwa yanzu, kasar Sin ta yi ta yin mu'amala da hadin gwiwa da kasashen duniya a fannin ilmi mai zurfi, ta kuma samar da sharudda masu kyau wajen horar da gwanaye da yin ayyukan nazarin kimiyya.

Jami'ar Beijing tana daya daga cikin shahararrun jami'o'i na kasar Sin. A 'yan shekarun nan da suka wuce, jami'ar nan ta mayar da bude kofarta ga kasashen duniya a matsayin muhimmiyar manufarta wajen bunkasuwa, ta kara yin mu'amala da hadin gwiwa da kasashen waje ta hanyoyin shigo da littattafan koyarwa da yin hadin gwiwar nazari. Mr. Xia Hongwei, wanda yake aiki cikin sashen kula da yin hadin kai da kasashen waje na jami'ar, ya nuna cewa, Jami'ar Beijing ta ci riba sosai daga wajen yin mu'amala da hadin kai da kasashen waje. Ya ce: "saboda yin mu'amala da kasashen waje a cikin shekarun nan da suka wuce, jami'armu ta ci riba, musamman ma an samar mana da sabbin ra'ayoyin koyarwa. Littattafai da hanyoyi na zamani a fannin koyarwa sun kara wa malamanmu sani, malamanmu sun yi koyi da sakamako mafi kyau da aka samu a fannin koyarwa, sun hada su da halin da kasar Sin take ciki a yanzu, ta haka an sami sakamako mai kyau. "

Ban da wannan kuma, Jami'ar Beijing ta yi hadin kai da takwarorinta na kasashen waje wajen ayyukan nazari cikin himma da kwazo.

Ban da yin mu'amala da hadin gwiwa da kasashen waje kuma, kasar Sin ta hada da kasashen waje sun yi hadin gwiwar tafiyar da jami'a, sun aika da dalibai masu dalibta ga juna, kuma sun kai wa juna ziyara da dai sauransu.

An gabatar da cewa, saboda ta yi hadin kai da kasashen waje a fannin tafiyar da jami'a, kasar Sin tana fatan shigo da hanyoyi na ba da ilmi da koyarwa da kuma fasahohin gudanarwa na zamani daga kasashen waje don kara daga matsayin da take tsayawa a kai a fannonin malamai da ingancin koyarwa a jami'o'i da kwalejojinta, da kuma ingiza gina fannonin ilmi da suke baya-baya da horar da gwanaye.

Tun da can har zuwa yanzu, aika da dalibai masu dalibta zuwa kasashen waje yana daya daga cikin manyan hanyoyin da kasar Sin take bi wajen koyon kimiyya da fasaha da hanyoyin koyarwa na zamani da kuma yin mu'amalar aikin ba da ilmi. Dalibai da masana kimanin dubu 800 sun je kasashen waje don yin karatu ko kara ilmi a cikin shekaru 25 da suka wuce. A sa'i daya kuma, dalibai masu dalibta daga kasashen waje suna ta karuwa, a shekarar da ta gabata, daliban waje fiye da dubu 110 sun zo kasar Sin karatu, wanda ya ninka fiye da sau 4, in an kwatanta su da na shekarar 2003.

Mr. Ki Joon Kwon, wani dan kasar Korea ta Kudu, yana karatu a kwalejin gudanar da tattalin arziki na Jami'ar Beijing. Yana ganin cewa, yin karatu a kasar Sin mataki ne da ya dauka bisa basira. Ya ce: "saboda manufofin ba da fifiko da gwamnatin kasar Korea ta Kudu da manyan masana'antun kasar suka bayar, yanzu 'yan Korea ta Kudu da ke zuwa kasar Sin don yin karatu sai kullum kara karuwa suke. 'Yan makarantar sakantare namu 6 ko 7 sun zo Jami'ar Beijing don yin karatu. "

A shekarun baya da suka gabata, gwamnatin kasar Sin ta dauki matakai a jere, don samar da hali mai kyau da dalibai masu dalibta daga wurare daban daban na duniya a fannonin karatu da zaman rayuwa.

Kasar Sin ta kuma ba da taimako ga abokanta na kasashe masu tasowa, sun more nasarorin da kasar Sin ta samu daga aikin ba da ilmi da kimiyya da fasaha tare. Ga misali, gwamnatin kasar Sin ta ba da sukolashif har fiye da dubu 17 ga kasashen Afirka 50, don taimaka musu wajen yin karatu a kasar Sin; haka kuma, ta aika da malaman koyarwa fiye da 530 don taikama kasashen Afirka wajen raya fannonin ilmi da suke baya-baya.

Lokacin da yake halartar wani taron duniya da aka yi a nan Beijing a kwanan baya, Mr. Sintayehu Woldemichael, jami'in ma'aikatar ilmi ta kasar Habasha, ya gaya wa wakilinmu cewa, tun daga shekarar bara, kasar Sin ta kara ba da sukolashif ga 'yan kasar Habasha, sun yi wa kasar Sin godiya sosai saboda abokantaka da taimako. Ya kuma ba da karin haske cewa: "ko wace jami'ar kasar Habasha ta kafa hulda a tsakaninta da takwaranta na kasar Sin. Sun yi nazarin kimiyya cikin hadin kai, sun yi musayar malamai da juna. Irin wannan hadin gwiwa ya amfana wa dukan bangarorin kasashen Habasha da Sin."(Tasallah)