A gun babban taro na 60 na M.D.D. da aka yi a ran 15 ga wata, an zartas da kudurin kafa majalisar hakkin dan Adam bisa kuri'u masu rinjaye na nuna yarda. Kofi Annan, babban sakataren majalisar ya ba da sanarwa kan wannan batu cewa, wannan kuduri yana da ma'anar tarihi, zai sa kaimi ga sha'anin hakkin dan Adam na M.D.D. da zai shiga wani sabon mataki.
A gun taron jefa kuri'a da aka yi a wannan rana, sai kasashen Amurka da Isra'ila da Marshall Island da kuma Palau kawai ne wadanda suka jefa kuri'u na ki, kuma da akwai sauran kasashe 3 wadanda suka janye jiki, sauran kasashe 7 wadanda kuma suka rasa ikon jefa kuri'a ne sabo da sun tsawaita lokacin biyan kudin karo-karo ga majalisar, ban da wannan kuma da akwai kalilan din kasashe da ba su halarci taron ba.
Ba abu mai sauki ba ne zartas da wannan kuduri bisa kuri'u masu rinjaye. Bisa "takardar sakamako" da aka daddale a gun taron shugabannin M.D.D. da aka yi a shekarar 2005 an tanadi cewa, za a kafa majalisar hakkin dan adam maimakon kwamitin hakkin dan adam da ake da shi yanzu a birnin Geneva. Ko da yake kasashe daban-daban sun yardar da wannan takardar bisa ka'ida, amma abubuwan da suka fata ganin su daban-daban ne.
Domin kawar da bambancin da ke tsakanin wadannan kasashe, bayan da aka shafe watanni 5 ana ta yin shawarwari da tattaunawa, wato a ran 23 ga watan jiya, Jan Eliasson, shugaban wannan taron majalisar ya mika wa dukkan kasashe mambobin majalisar kofin shirin kuduri game da kafa majalisar hakkin dan Adam, wannan shirin kudurin ya daidaita sabanin da ke tsakanin kasashe daban- daban sosai kan batutuwan sikelin majalisar da ma'aunan shiga cikin majalisar da kuma hanyar tafiyar da harkokinta. Da ma Mr. Eliasson yana fatan za a zartas da wannan shirin kuduri na majsalisar hakkin dan Adam ta hanyar yin shawarwari, amma kasar Amurka ta tsaya ta nemi da a jefa kuri'a kan wannan shirin kuduri.
Bayan da aka zartas da wannan kuduri, zaunannen wakilin kasar Amurka da ke M.D.D. ya yi jawabi cewa, ko da yake Amurka ba ta amince da wannan sabuwar hukumar sosai ba, amma har ila yau tana son yin hadin gwiwa da ita, kuma za ta yi kokari tare da sauran kasashe mambobin majalisar, ta yadda za ta zama wata hukuma mai karfi kuma mai amfani.
Kudurin da babban taron M.D.D. ya zartas a ran 15 ga wata ya tanadi cewa, majaliasar hakkin dan Adam wata hukuma ce da ke karkashin babban taron majalisar, bayan shekaru 5 masu zuwa, M.D.D. za ta sa ido kan matsayin wannan majalisar. Kuma an rarraba kujeru 47 na majalisar hakkin dan Adam bisa ka'idar adalci wato bisa barbazuwar yankunan kasashe.
Bisa kudurin da aka tsayar an ce, A ran 16 ga watan Yuli na wannan shekara majalisar tattalin arziki da zaman al'umma ta M.D.D. za ta soke kwamitin hakkin dam Adam, kuma za a kira taro na farko na majalisar hakkin dan Adam a ran 19 ga watan Yuli na wannan shekarar da muke ciki.
Bayan da aka zartas da wannan kuduri, Zhang Yishan, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin da ke M.D.D. ya yi jawabi cewa, ya kamata majalisar hakkin dan Adam ta dauki wannan kuduri bisa matsayin jagorancinta wajen tafiyar da harkokinta a nan gaba, ta daidaita matsalolin hakkin dan Adam ta hanyar adalci da rishin yin zabi, ta yadda wannan hukumar ba za ta taka rawar da kwamitin hakkin dan Adam ya yi na yin dagiya wajen siyasa ba. Mr. Zhang ya kuma bayyana cewa, kasashen duniya da jama'ar kasashe daban- daban suna sa fatan alhairi sosai kan majalisar hakkin dan Adam, suna fatan majalisar za ta iya ba da gudumawarta yadda ya kamata, kuma ta sa kaimi ga dukkan mutanen duniya da su samu hakkin dan Adam da 'yancinsu sosai. (Umaru)
|