Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-17 17:12:52    
Masana daga bangarori daban daban sun yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su karfafa hadin gwiwa don rage yawan mutanen da ke fama da talauci da kuma samar da ilmin da ya wajaba

cri

A ran 16 ga wata, an yi shawarwari kan harkokin ilmi da horaswa a birnin Beijing, inda wakilai sama da 100 da suka zo daga kungiyar kasa da kasa ta majalisun tattalin arziki da harkokin yau da kullum da makamantansu da kuma hukumar kula da tattalin arziki da zaman al'umma ta MDD suka yi shawarwari dangane da rage yawan mutanen da ke fama da talauci da kuma ilmantarwa da dai sauran batutuwa. Mahalartan taron sun yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu don neman rage yawan mutanen da ke fama da talauci da samar da ilmin da ya wajaba da dai sauran manufofin bunkasuwa na karni daya a cikin shekaru 10 masu zuwa.

Makasudai takwas da shugabannin kasashe daban daban suka tsai da a shekara ta 2000, wato ciki har da rage yawan mutanen da ke da tsananin fama da talauci da rabi da samar da ilmin da ya wajaba kafin shekara ta 2015, su ne abin da muke kira shirin MDD na manufofin bunkasuwa na karni daya. Bisa kidayar da MDD ta yi, an ce, har zuwa yanzu dai, akwai mutane sama da biliyan daya wadanda ke fama da matukar talauci, kudin zamansu a ko wace rana bai kai dala daya ba. Bayan haka kuma, akwai yaran da yawansu ya wuce miliyan 100 wadanda shekarunsu sun kai shiga makaranta amma sun kasa sabo da talauci, musamman ma a shiyyar Afirka da ke kudu da Sahara.

Mataimakin shugaban hukumar kula da tattalin arziki da zaman al'umma ta kasar Benin, Tabe Gbian ya bayyana a gun taron cewa, yaya za a samar da ilmi a tsakanin mutanen da ke fama da talauci har zuwa yanzu dai ya ci gaba da zama babban kalubale a gaban kasashen Afirka masu yawa. Ya ce, 'Afirka a baya take a wajen ba da ilmi. Matsalar da muke fuskanta a halin yanzu ita ce karancin kudi, kuma muna tsananin bukatar warware ta. Sabo da ilmi tushe ne na bunkasuwar sauran abubuwa, a sabo da haka ne ma, shirin MDD na manufofin bunkasuwa na karni daya yake da matukar muhimmanci.

Madam.Hanifa Mezoui, shugabar sashen kula da kungiyoyin da ba na gwamnati ba na hukumar kula da tattalin arziki da zaman al'umma ta MDD, ta nuna cewa, a kasashe da shiyyoyin da suka fi rashin samun ci gaba a duniya, akwai muhimmanci sosai a bunkasa harkar ilmi da horaswa don karya karfafa juna da talauci da rashin samun ilmi suke yi. Ta ce, 'binciken da kungiyoyin da ba na gwamnati ba suka yi ya shaida cewa, sabo da karancin samun hanyoyin horaswa da kuma ilmantarwa kamar yadda ya kamata, mutane ba su iya bunkasa karfinsu na neman ci gaba ba, har ma ya kawo barazana a kan kokarin da ake yi na neman tabbatar da manufofin bunkasuwa na karni guda.'

Mahalartan taron suna kuma ganin cewa, bunkasuwar ilmi da ta tattalin arziki suna iya sa kaimi ga juna. A cikin shekaru 5 da suka wuce, bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma da aka samu a kasashen Asiya sama da 30, ciki har da kasar Sin da ta India, ta rage yawan mutanen da suka yi fama da talauci da kuma kasa shiga makarantu a duk fadin duniya.

Labarin da muka samu daga hukumomin kula da harkokin ilmi na kasar Sin ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana mayar da ilmi a muhimmin matsayi da ya kamata a bai wa fifikon bunkasa shi, kuma ta sa kaimi da a mai da hankali a kan kauyuka da kuma talakawa a wajen ba da ilmi. A halin yanzu dai, yawan mutanen da suke samun ilmin tilas a nan kasar Sin ya riga ya kai kashi 94%. Ban da wannan kuma, nan da shekaru biyar masu zuwa, kasar Sin za ta kara zuba jarin da yawansa ya kai fiye da yuan biliyan 200 a wajen ba da ilmin tilas, kuma za ta tabbatar da rashin biyan kudin samun ilmin tilas a kauyuka a shekaru biyu masu zuwa.

Madam.Hanifa Mezoui ta bayyana cewa, kasar Sin misali ne mai kyau a wajen hada bunkasa ilmi da kuma bunkasa tattalin arziki, kuma bunkasuwar kasar Sin ta ba da taimako a wajen tabbatar da manufofin bunkasuwa na karni daya.(Lubabatu Lei)