Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-17 15:45:52    
Mazaunan birnin Beijing suna kaunar motsa jiki a tsakanin al'ummominsu

cri

Jama'a masu karatu, a cikin shirinmu na yau, za mu ga wani muhimmin fanni game da motsa jiki da jama'ar kasar Sin suke yi, wato yadda mazaunan kasar Sin suke motsa jiki a tsakanin al'ummominsu da ke birane. Sai mu shiga cikin al'ummar gabashin Nongguang da ke kudu maso gabashin birnin Beijing, mu ga yadda mazaunan wurin suke motsa jiki a kullum.

A ko wace rana da safe a wani dandali na al'ummar gabashin Nongguang na birnin Beijing, mutane da dama su kan yi wasan takobi mai suna 'Taiji' a harshen Sinanci. Da farko, malama Liu Xiuming, wadda ta yi ritaya daga wata makaranta ta koyi yadda ake yin wasan 'Taiji', sa'an nan ta koyar da wasan ga makwabtanta. A hankali a hankali, yawan mutanen da suke yin wasan 'Taiji' ya zarce 70, haka ma wadanda suke sayen takubba da tufafi da kaset ?kaset da veido domin wasan. Game da haka, Malama Liu Xiuming ta yi alfahari da wannan sosai, ta ce,

'Mutane masu yawan gaske suna yin wasan 'Taiji', ciki har da tsofaffi masu shekaru 70 ko 80 da haihuwa da kuma matasa masu shekaru fiye da 20. Ya zuwa yanzu, mun yi shekaru 7 muna wasan 'Taiji', ta haka, muna kyautata halin da jikinmu yake ciki, muna da lafiyar jiki sosai.'

Ko wane mutumin da yake wasan 'Taiji' ya san kyautatuwar jikinsa. Malama Shen, wadda ta yi ritaya, ta gaya mana cewa,

'Tun da na fara wasan 'Taiji', a lokacin sanyi, ban gamu da mura kamar da ba. Abu mai muhimmanci shi ne da mutane da yawa muke wasan tare, ina jin dadin zama sosai bayan da na yi ritaya daga aiki. A halin yanzu, wasan 'Taiji' ya yi kamar aikina, ko wace rana da safe da na tashi, sai nan da nan na zo wurin na yi wasa, to, wannan yana da kyau sosai.'

Shugaban wasan takobi na 'Taiji' Malam Wang Bohua ya gaya mana cewa, a da tsofaffi da yawa ba su da lafiyar jiki, wasu suna da hawan jini, wasu ba su iya yin barci da kyau da dare. Amma ta hanyar wasan 'Taiji', ba kawai sun sami lafiyar jiki ba, har ma suna jin dadi a zuciya. Ya ce,

'Ta yin wasan 'Taiji' cikin shekaru 7, a halin yanzu, mazaunan al'ummar suna da lafiyar jiki, suna iya ci abinci da yawa, suna iya yin barci sosai, tsofaffin da ke da hawan jini ba su shan magunguna a yanzu, mazaunan suna samun moriya daga wasan 'Taiji'. Sabo da haka, ko wace rana suna wasan.'

Ban da wasan takobi na 'Taiji', mazaunan al'ummar gabashin Nongguang suna sha'awar sauran ayyukan motsa jiki kamar wasan kwallon tebur da dai sauransu. Shugabar al'ummar Malama Zhao Lihui ta gaya mana cewa,

'A halin yanzu dai, muna gudanar da ayyukan motsa jiki iri daban daban, kamar wasan badminton da kwallon tebur da wasan 'Taiji' da wasan raye-raye da dai sauransu.'

Shugaba mai kula da harkokin al'adu da wasanni ta al'ummar gabashin Nongguang Malama Jia Jinning tana ganin cewa, wasan al'adu da na motsa jiki suna jawo hankulan mazauna wurin, sabo da haka mazaunan suna nisantar caca da sauran abubuwa marasa kyau, ta haka, mazaunan suna hadin kai a fannoni daban daban. Ta ce,

'Yayin da muke wasa tare, idan wani mutum ya gamu da wata matsala, sai dukkanmu mu taimake shi. Ta wasannin, mazaunan al'ummar suna fita daga gidajensu, suna taimakawa juna.'

Ko da yake a wasu wurare, karancin na'urori su kan kayyade wasannin motsa jiki da mazaunan al'ummomin birnin Beijing su kan yi, amma gwamnatin birnin tana mayar da wannan matsala da ta zama wani muhimmin aiki da take gudanarwa domin samar wa jama'a jin dadi. Dokar motsa jiki a birnin Beijing da aka fara yin amfani da ita a ranar 1 ga watan Maris ta bayar da wani tsari a fannin doka game da motsa jiki da mazaunan birnin Beijing suka yi. Tare da bunkasuwar aikin share fage na wasannin Olympics da za a shirya a shekarar 2008 a birnin Beijing, za a kara kyautata na 'urorin motsa jiki a al'ummomi daban daban na birnin Beijing. Haka kuma, muna iya cewa, bunkasuwar motsa jiki a Beijing ta yi kamar bunkasuwar wasannin a al'ummomi na sauran birane na kasar Sin.(Danladi)