Assalamu alaikum, jama'a masu karatu, barka da sake saduwa a cikin shirinmu na yau na Duniya ina Labari. Bi da bi ne aka rufe tarurrukan shekara-shekara na majaliasar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin da majalisar dokokin kasar Sin. A gun bikin rufe taron majalisar dokokin kasar Sin da aka yi a ran 14 ga wata, mahalartan taron sun amince da "tsari na 11 na shekaru biyar-biyar na raya tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sin" da gwamnatin kasar Sin ta gabatar tare da kuri'u masu dimbin yawa. Yanzu ga bayanin da wakilanmu suka aiko mana.
Muhimmin batun da aka tattauna a gun tarurruka biyu na shekarar da muke ciki shi ne tattauna tsarin neman bunkasuwar kasar a cikin shekaru 5 masu zuwa. Wannan tsari yana da bambanci sosai da shirye-shiryen da aka gabatar a da. Da farko dai, madam Geng Qing-qing ta bayyana muku muhimman abubuwa game da wannan tsari. Madam Geng ta ce, "A fannin tattalin arziki, dalilan makamashin halittu da muhallin da muke ciki suna kayyade saurin neman bunkasuwar tattalin arziki, amma dangane da maganar neman guraban aikin yi, ana fatan za a kara saurin neman bunkasuwa. A sakamakon haka, saurin karuwar GDP zai ragu kadan a cikin shekaru 5 masu zuwa. Sannan kuma, dole ne a rage yawan makamashin halittu da za a yi amfani da shi. Sabo da haka, dole ne a nemi moriyar tattalin arziki ta hanyar raya kimiyya da fasahohin zamani. Bugu da kari kuma, za a kara yin gyare-gyare kan sha'anin kasafin kudi da hukumomin sha'anin kudi cikin hali mai dorewa."
Abin da ya fi muhimmanci a cikin wannan tsari na 11 na shekaru biyar-biyar shi ne kasar Sin tana kokarin sauya hanyar neman bunkasuwar tattalin arzikinta. A da, kasar Sin ta dogara kan makamashin halittu domin neman bunkasuwar tattalin arziki, amma yanzu za a dogara kan sabbin ilmin kimiyya da fasahohin zamani domin neman bunkasuwarta. Game da wannan batu, Mr. Jiang Weixin, mataimakin shugaban kwamitin kula da harkokin yin gyare-gyare da raya kasar Sin ya bayyana cewa, "Za a kara sa ido kan aikin yin tsimin makamashin halittu. Kasar Sin za ta kuma aiwatar da muhimman ayyukan yin tsimin makamashin halittu 10, kuma za ta bi sawu da sa ido da yin bincike kan masana'antu 1000 wadanda suke yin amfani da makamashin halittu masu yawan gaske."
Aikin ba da ilmi tushe ne na raya kimiyya da fasaha. A cikin tsari na 11 na shekaru biyar-biyar, ana mai da hankali sosai kan aikin ba da ilmi, musamman a kauyuka. Sabo da haka, firayin minista Wen Jiabao ya gabatar da cewa, za a kara ware kudade sosai domin raya aikin ba da ilmi, kuma za a kyautata sharudan ba da ilmi a wurare masu fama da talauci. Mr. Wen ya ce, "A cikin shekaru 5 masu zuwa, kasar Sin za ta ware kudin Sin Renminbi yuan biliyan 218.2 daban domin aikin ba da ilmin tilas. Kuma za a tabbatar da samar da kudade domin makarantun firamare da na sakandare na kauyuka. Bugu da kari kuma, za a kyautata tsarin ware kudade domin gyaran fuskokin makarantun firamare da na sakandare na kauyuka. Sakamakon haka, za a iya tabbatar da ganin cewar kowane yaro na kauyuka ya samu damar shiga makaranta."
Amma, jama'a farar hula sun fi mai da hankali kan zamantakewarsu. A cikin wannan tsari na 11 na shekaru biyar-biyar, an tabbatar da cewa za a sa manoma miliyan dari 1 su samu ruwan sha mai tsabta, kuma za a kara shimfida ingancin hanyoyi a kauyuka, yara masu fama da talauci ma za su iya shiga makaranta. Yawan kudin shiga da kowane mutum ya samu zai karu da kashi 5 cikin kashi dari. Sannan kuma, manoma marasa lafiya wadanda ba su kamu da ciwo mai tsanani ba za su iya samun jiyya a kauyukansu, idan sun kamu da ciwo mai tsanani, za su iya samun jiyya a asibitocin da ke garin gundumarsu. Bugu da kari kuma, za a samar da guraban aikin yi miliyan 90. Muhallin da muke ciki zai samu kyautatuwa kamar yadda ake fata. (Sanusi Chen)
|