Jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin wata jiha ce wadda take da kayayyakin tarihi da na al'arun gargajiya da yawa, cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, gwamnatin kasar Sin ta mai da muhimmanci sosai kan ayyukan kiyaye kayayyakin tarihi da na al'adun gargajiya na jihar, kuma ta ware makudan kudade domin wannan aiki.
Yanzu, ana nan ana yin wani babban aikin kiyaye da yin gayre-gyare ga manyan haikalai guda 3 na tarihi wato fadar Potala da haikalin Roubulinka da na Sakya na jihar Tibet, gwamnatin kasar Sin ta ware kudin Renminbi Yuan miliyan 330 domin wannan aiki, ya zuwa yanzu an riga an kashe kudi Yuan miliyan 190 don yin wannan aiki, aikin nan da ake yi kuma ya kawo amfani ga kiyaye kayayyakin tarihi da na al'adun gargajiya masu tarihi na shekaru dubbai na jihar Tibet.
Jihar Tibet tana daya daga cikin larduna da jihohi wadanda ke da kayayyakin tarihi da na al'adun gargajiya mafiya yawa a kasar Sin, Yawan ni'imtattun wurare masu ban sha'awa na tarihi da ake da su yanzu a jihar Tibet ya kai fiye da 2000. Gwamnatin tsakiya ta kasar Sin kullum tana mai da muhimmanci sosai wajen kiyaye kayayyakin tarihi da na al'adun gargajiya na jihar Tibet, Daga karshen shekaru 80 zuwa farkon shekarun 90 na karnin da ya wuce, gwamnatin kasar Sin ta ware kudin Renminbi Yuan miliyan 53 domin yin gyare-gyare na mataki na farko ga fadar Potala, daga baya kuma ta ware kudin Renminbi Yuan miliyan 330 domin kiyaye da yin gayre-gyare ga muhimman ni'imtattun wurare masu ban sha'awa guda 3 na tarihi na jihar Tibet, zuwa karshen shekarar 2003, jimlar kudin da gwamnatin kasar Sin ta ware domin kiyaye kayayyakin tarihi na jihar Tibet ta kai fiye da Yuan miliyan 600.
Mr. Nimaciren, shugaban hukumar kula da kayayyakin tarihi ta jihar Tibet mai tafiyar da harkokin kanta ya bayyana cewa, a lokacin da aka aiwatar da shiri na 10 na shekaru 5-5 na raya kasa wato daga shekarar 2001 zuwa ta 2005, kuma a karkashin kulawar gwamnatin tsakiya da ta jihar, an kiyaye muhimman kayayyakin tarihi da na al'adun gargajiya na jihar Tibet sosai. Yanzu ana nan ana yin gyare- gyare ga muhimman wurare masu ban sha'awa na tarihi guda 3 lami lafiya, kuma za a kammala ayyukan gine-gine a wannan shekarar da muke ciki. Ban da wannan kuma an riga an fara aikin share fage domin yin gyare-gyare ga tsohon wurin Jiangzizongshan na yin dagiya da maharan Ingila da lambun Langsailin da aka samu yarda ga yin su daga wajen hukumar kayayyakin tarihi ta kasar.
Mr. Nimaciren ya ce, daga shekarar 2001 zuwa ta 2005, sassan kula da kayayyakin tarihi na matakai daban-daban na jihar Tibet sun yi aikin safiyo da tsara shirin kiyaye da gyare-gyare ga haikalai guda 10 ciki har da haikalin Jokhan, kuma an tsara shirin kiyaye kabarin sarkin Tibet da tsohon wurin da ake kira Karuo da sauran muhimman ni'imtattun wurare masu ban sha'awa na tarihi.
Cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, sassan gwamnatin kasar Sin kuma sun kara karfinsu domin tsaron zaman lafiya na kayayyakin tarihi na jihar Tibet, yanzu, fadar Potala da haikalin Gandan da na Daipung da sauran muhimman sassan kiyaye kayayykin tarihi dukkansu sun yi rajistar kayayyakin tarihi na matakai daban-daban. Ban da wannan kuma, a kowace shekara hukumar kayayyakin tarihi ta jihar Tibet ta kan daddale "yarjejeniyar daukar alhakin kiyaye kwanciyar hankali ta kayayyakin tarihi" a tsakaninta da sassan kiyaye kayayyakin tarihi guda 7 na jihar, wannan ya kawo amfani ga kiyaye kayayyakin tarihi da na al'adun gargajiya masu daraja na jihar Tibet ta kasar Sin. (Umaru)
|