Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-16 17:03:56    
Tunesia, wani fure da ke tofowa a cikin hamada

cri

Idan ana son samun wata kasa da 'babu aibi' a wajen yawon shakatawa daga taswirar duniya, to, dole ne zan gabatar muku da kasar Tunesia.

A kasar, kana iya samun dukan abubuwan da za su tabbatar da rashin aibu. Akwai teku da sahara, akwai jama'a masu tawali'u, akwai farashi mai sauki. Kada kuma mu manta da hakurinta. A kasar, har ma kana iya ganin coci-coci na Yahudawa. Da safe, bayan da ka zagaya Kairouan, birni mai tsarki na musulmi a Afirka ta arewa, sa'an nan a yamma, kana iya zuwa Hamma-Mat, wato gabar bahar Rum wanda ke cike da kide-kiden Andalusia, inda kuma kana iya shan rana?

Tunesia ta yi kamar ta zo duniya ne musamman domin yawon shakatawa. Wannan kasar da fadinta bai kai murabba'in kilomita dubu 100 ba, tana jawo masu yawon shakatawa na waje kusan miliyan 5 a ko wace shekara, kudin waje da ta samu daga wannan fanni ma ya kai dalla biliyan 2. Bisa kidayar da kungiyar UNESCO ta yi, an ce, akwai wuraren tarihi na dan Adam da yawansu ya kai sama da 12 a kasar. A kasar kuma, kana iya ganin wayin kai na zuriyoyi daban daban. Da wayin kai na Rome da al'adun Girika da kuma tarihin Vandali duka kana iya samun amsoshinsu a kasar Tunesia.

A kasar Tunesia, za ka ji mamakin kayayyakin yawon shakatawa masu inganci na kasar. A kasar, akwai hotel iri daban daban har dubu gomai, kuma yawancinsu suna da halayen musamman na kansu, farashinsu ma yana da sauki. Bayan haka kuwa, gwamnatin Tunesia ta yi dimbin aiki wajen kyautata aikin yawon shakatawa a kasar, a wurin shakatawa na ko wane birni akwai bus da za su iya jigilar masu yawon shakatawa daga wurin zuwa hotel. A kasar, akwai kuma kasuwannin Madina. A cikin Larabci, Medina ma'anarsa shi ne tsohon birni, a wurin, kana iya ganin 'yan kasuwa masu dimbin yawa wadanda ke tallan tsarabobi na wurin.

Ko da yake Tunesia kasa ce karama, amma tana da hanyoyin da suka fi inganci a arewacin Afirka. akwai babbar hanya mai matukar kyau da ta shimfidu daga gabar bahar Rum da ke arewa har zuwa Sahara da ke kudu. Alamun da ke kan hanya ma sun bai wa masu yawon shakatawa na kasashen waje saukin tafiya a kasar. Ban da wannan, tafiye-tafiye a cikin jiragen kasa da na sama a kasar ma akwai dadi.

Muhimman abubuwa uku da suka fi jawo masu yawon shakatawa zuwa kasar Tunesia su ne 3S, (Sahara, Sea, Sun), wato Sahara da teku da kuma rana. Kafin ka je Tunesia, kamata ya yi ka shirya yin kamping a Sahara. Ko shakka babu, fitowar rana da faduwarta a Sahara za su burge ka, har ma ba za ka iya mantawa da su ba har duk rayuwarka. Sa'an nan kuma, ya kamata ka je gabar bahar Rum, a wurin akwai kayayyakin tarihi na Carthage wadanda suka shafe shekaru 3000 suna wurin. Bayan haka, a Tunesia, kana iya shan rana a duk shekara, shi ya sa kana iya shirin zuwa wurin a ko yaushe.

Amma idan kana son irin yanayi na murnar lokacin hutu, to, ya kamata ka je kasar a watan Yuli da na Agusta, a lokacin, za ka gamu da mutane miliyan biyu da suka zo daga Turai wadanda ke yawon shakatawa a wurin. Amma idan ba ka son ganin mutane masu yawa, lalle ne ya kamata ka je kasar a Watan Maris zuwa Mayu, a lokacin, an fara dumi, ga shi kuma furanni sun tofo.

Amma idan burinka shi ne ganin fitowar rana da faduwarta a Sahara, to, watan Oktoba zuwa watan Maris mai zuwa lokaci ne mai kyau, musamman ma a watan Nuwamba a Douz, a kan yi bikin Sahara a ko wace shekara, wanda bai kamata ya wuce ka ba.(Lubabatu Lei)