Idan ba ku manta ba, daga ran 18 ga watan Satumba zuwa ran 20 ga watan Disamba na shekara ta 2005, mun shirya gasar kacici-kacici game da 'Taiwan wani tsibiri ne mai ni'ima na kasar Sin'. Ga shi a yau, muna farin ciki matuka da shaida muku cewa, mun riga mun kawo karshen wannan gasa, kuma kamar yadda muka yi muku alkawari yayin da muke shirya wannan gasa mai ban sha'awa, za mu ba da kyaututtuka ga wadanda suka amsa tambayoyin daidai.
Masu sauraro, sauraron bayanai kan gasar ke da wuya, sai nan da nan aminai masu sauraro suka aiko mana amsoshinsu ba tare da wani jinkiri ba, kuma yawan bayanansu ya wuce 2,200. To, a cikin shirinmu na yau, bari mu sanar da ku a kan wadanda suka ci nasara a gasar.
Da farko, muna farin ciki da gaya muku cewa, daga cikin wadanda suka shiga gasar, sashen Hausa ya zabi mutum daya wanda ya sami kyautar musamman, wato zai sami damar kawo ziyara a nan kasar Sin ba tare da biyan kudi ba, kuma wannan mutumin da ya taki sa'a shi ne malam. Abdullahi Garba Baji daga jihar Kano da ke tarayyar Nijeriya.
Ban da wannan kuma, sashen Hausa ya zabi mutane 5 da suka sami matsayi na farko, da 8 da suka sami matsayi na biyu da kuma mutane 12 da suka sami na uku. Yanzu, bari in karanto sunayensu bi da bi.
Wadanda suka sami matsayi na farko su ne:
1) Malam Yahaya Salisu daga jihar Nassarawa ta tarayyar Nijeriya
2) Malam Musa Buba dan Fulani daga jihar Bauchi ta kasar Nijeriya
3) Malam Auwal Muh'd Maunde daga jihar Adamawa ta kasar Nijeriya
4) Malam Ibrahim Z.Othman daga jihar Kaduna ta kasar Nijeriya
5) Malam Abdulhadi Abubakar daga jihar Gombe ta kasar Nijeriya
Wadanda suka sami matsayi na biyu su ne:
1) Malam. Shu'ai M.Koshe /Itas daga jihar Bauchi ta kasar Nijeriya
2) Shugaba Bello Abubakar Malam Gero daga jihar Sokoto ta kasar Nijeriya
3) Malam.Ladidi Rabi'u A.Usman Mailu daga jihar Jigawa ta kasar Nijeriya
4) Malam.Sani Dahiru daga jihar Palateau ta kasar Nijeriya
5) Malam.Umar Abubakar Jalingo daga jihar Nassarawa ta kasar Nijeriya
6) Malam.Ibrahim Muhammed Zaria daga jihar Abuja ta kasar Nijeriya
7) Malam.Abba Sabo daga jihar Jigawa ta kasar Nijeriya
8) Shugaba alhaji Karami daga jihar Bauchi ta kasar Nijeriya
Wadanda suka sami matsayi na uku su ne:
1) Mrs.Maryam Musa daga jihar Nassarawa ta kasar Nijeriya
2) A'isha Mammai daga jihar Katsina ta kasar Nijeriya
3) Jamilu Muh'd daga jihar Gombe ta kasar Nijeriya
4) Baba Mala Kachalla daga jihar Borno ta kasar Nijeriya
5) Fatsuma Isah daga jihar Yobe ta kasar Nijeriya
6) Lubabatu Ahmed KD daga jihar Taraba ta kasar Nijeriya
7) Ya'u Hoh'd Bakanike daga jihar Niger ta kasar Nijeriya
8) Ali Aliyu D.K. Kamba daga jihar Kebbi ta kasar Nijeriya
9) Safiya Salisu daga jihar Jigawa ta kasar Nijeriya
10) Salihu Adama daga jihar Nassarawa ta kasar Nijeriya
11) Abubakar SadiqNingi daga jihar Bauchi ta kasar Nijeriya
12) Hamid Ahmed Buhari daga jihar Adamawa ta kasar Nijeriya
To, bari mu taya wa wadannan masu sauraronmu murna, kuma za mu aika musu kyaututtuka bisa matsayin da suka samu a cikin gasar. Muna fatan za su yi kokari don kara samun nasarori a sabuwar gasar da za mu shirya a nan gaba.
Sa'an nan kuma, ga shi akwai akwatin gidan wayarmu a birnin Lagos na kasar Nijeriya, wato Lagos Bureau,China Radio International, P.O.Box 7210, Victoria Island, Lagos
To, masu sauraro, wannan shi ya kawo karshen shirinmu na yau. Da haka, ni Lubabatu ke cewa, mu huta lafiya daga nan Beijing.(Lubabatu Lei)
|