Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-15 18:52:52    
Tarurruka guda biyu a idon baki daga kasashen waje

cri

Jim kadan bayan rufe taron shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta duk kasar Sin da na majalisar wakilan jama'ar duk kasar a shekarar 2006. Wadanda suka jawo hankulan mutane kamar yadda wakilai mahalartan taron majalisar wakilan jama'ar duk kasa da kuma mambobi mahalartan taron ba da shawara kan harkokin siyasa ta duk kasar suka yi, su ne baki daga kasashen waje wato ' yan jarida na kafofin watsa labaru na kasashen waje da kuma jakadun kasashen waje dake a nan kasar Sin, wadanda suka dauki labarai ko saurari jawabai da aka yi a gun tarurrukan nan guda biyu. Lallai suna da nasu ra'ayoyi game da tsarin siyasa, da salon yalwatuwa da kuma shirye-shirye na makoma na kasar Sin.

' Yan jarida fiye da 400 na kafofin watsa labarai da yawansu ya kai 180 daga kasashe fiye da 35 sun dauki labarai a gun wadannan tarurruka guda biyu da kasar Sin ta yi a wannan shekara. Zaunannaniyar ' yar jarida mai suna Caroline ta mujallar mako-mako da ake kira ' Le Point' tana aiki har na tsawon shekaru 20 ko fiye a nan kasar Sin, ta fadi cewa :

' Tarurrukan nan biyu da aka yi sun kasance tamkar agogon yanayin sama ne, wanda ya iya gwada sauye-sauye da canje-canje na zaman al'ummar kasar Sin. Na ga wakilai sun halaraci tarurrukan rike da inji mai kwakwalwa, kuma wakilai da yawa ba su kai shekaru 40 da haihuwa ba, kuma na ga akwai wakilai mata da yawa da kuma wakilai ' yan kananan kabilu saye da kyawawan tufafi. Ban da wannan kuma wakilai mahalartan tarurrukan sun iya amsa tambayoyin da manema labaru na Sin da na kasashen waje suka yi musu yadda ya kamata.

Domin kara yin bayani kan wadannan tarurrukan biyu da kuma samar da sauki ga daukar labarai, an ba da labarai kai tsaye kan yadda ake yin tarurrukan, an kuma shirya tarurruka fiye da l0 na watsa labarai; kazalika, an bude kofa ga kafofin watsa labarai na kasashen waje yayin da kungiyoyi fiye da 35 suke yin shawarwari. Yin haka, ya samar wa manema labaru na kasashen waje damar kara fahimtar tsarin siyasa na kasar Sin. To, ga abun da manemin labaru na farko na Tashar redio mai hoto ta ' Al-Jazeera' Mr.Izzat ya fada :'Lallai ci gaban da kasar Sin ta samu yana da muhimmiyar ma'ana ga dukkan kasashen Larabawa. Tun bayan da aka soma yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje a kasar Sin, duk duniya ta mai da hankali akanta sosai ko a fannin tattalin arziki ko a fannin siyasa. Yanzu ya kasance da babbar tazara tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa a fannin siyasa da na tattalin arziki. Don haka ne, kamata ya yi kasashen Larabawa su yi koyi da kasar Sin.'

Jama'a masu sauraro, an kuma gayyaci jakadu fiye da l00 domin halartar taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar duk kasa duk domin taimaka musu wajen kara fahimtar yanayin yalwatuwar kasar Sin. Jakadan kasar Fransa dake kasar Sin Mr. Philipe Guelluy ya furta, cewa:

' Majalisar wakilan jama'ar kasa har kullum takan ba da babban taimako ga kasar Sin wadda take samun manyan sauye-sauye a kowane lokaci.Amma duk da haka, takan gamu da tulin wahalhalu. Ba mai yiwuwa ba ne dukkan mutanen kasar Sin su samu wadata a sa'I daya. Ni kam ina sha'awar yadda za a kawar da wadannan wahalhalu.'(Sani Wang )