A gun taron shekarara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da ake yi a nan birnin Beijing, gwamnatin kasar Sin ta tsai da manufar cewa, yawan muhimman abubuwan kazamtarwa da za a zubar cikin shekaru 5 masu zuwa zai ragu da kashi 10 cikin 100 bisa na yanzu. Wannan ne karo na farko da gwamnatin kasar ta sa wannan takiti cikin manufar sa ido kan tattalin arziki daga duk fannoni a lokacin da take tsara tsarin matsakaici da kuma dogon wa'adi, kuma ya zama daya daga cikin batutuwan da wakilai mahalartan taron ke yin tattaunawa sosai a kai. To jama'a masu sauraro yanzu za mu karanta muku wani bayanin da wakilinmu ya ruwaito mana kan wannan labari.
Yanzu, kasar Sin tana cikin wani lokacin samun bunkasuwar tattalin arziki da sauri, a sa'i daya kuma matsi da ake yi mata wajen muhalli da albarkatun kasa sai kara tsanani yake a kowace rana, ruwan da ke cikin koguna da tafkoki da yawa ya kazamta, ingancin iska na wasu birane yana ta lalacewa, matsalar kazancewar muhalli ta riga ta zama daya daga cikin batutuwan da Sinawa suke tattaunawa a kai.
Dangane da wannan matsala, Mr. Zhou Shengxian, shugaban babbar hukumar kiyaye muhalli ta kasa wato muhimmiyar hukumar kula da harkokin kiyaye muhalli ta kasar Sin yana da abubuwa da yawa da yake ji a zuciyarsa. Ya ce, "Bisa matsayina na wani ma'aikacin kiyaye muhalli, ina da ra'ayin musamman game da raya kasa, wato shi ne bisa wani sharadi na musamman, raya kasa konewa ke nan, abubuwa da ake konewa su ne albarkatun kasa, abin da ya yi saura shi ne kazancewar muhalli, abin da aka kirkiro kuwa shi ne GDP wato jimlar kudin da aka samu daga aikin kawo albarkar kasa."
Madam Qian Yi, wakiliyar majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta ce, tana son yin tafi domin wannan manufar da aka tsayar a gun taron. Wannan kwararriyar kiyaye muhalli da ta zo daga jami'ar Qinghua da ke nan birnin Beijing ta ba da hakikanan shawarwarinta kan yadda za a tabbatar da wannan manufa, ta ce, "Ra'ayina shi ne ya kamata a daidaita matsalolin dukkan mafaran kazancewar muhalli daya bayan daya. Dukkan masana'antu, idan sun zubar da abubuwa kazamtarwa, ya kamata kowanensu ya rage yawan abubuwan kazamtarwa da ya zubar da kashi 10 bisa 100, sai in an yi haka ne za a iya tabbatar da yawan abubuwan kazamtarwar da dukkan masana'antun suka zubar ya ragu da kashi 10 bisa 100."
Wakilai da yawa na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin sun yi daidai kamar madam Qian Yi ta yi, dukkansu sun mai da hankali sosai kan batun kiyaye muhalli, kuma suna ta ba da ra'ayoyi ko shawarwarinsu domin cimma manufar rage yawan abubuwan kazamtarwar da za a zubar bisa halayen ayyuka na kansu.
Wakili He Da wani babban manaja ne na kamfanin narke karafa na Huai a lardin Jiangsu da ke gabashin kasar Sin, cikin 'yan shekarun da nan da suka wuce, kamfaninsa ya yi jarrabawa a fannin kiyaye muhalli, kuma sun samu babbar nasara, yanzu suna nan suna kara daukar matakai domin rage yawan abubuwan kazamtarwar da za su zubar. Ya ce, "Muna da wani mafarki, abubuwan da muke konewa yanzu domin narke karafa su ne kwal da garin gawayi da kuma iskar da ake kira Oxygen, idan an yi amfani da robar da aka zubar maimakon garin gawayi, ba ma kawai za a iya kau da jujin da aka zubar cikin zaman yau da kullum ba, har ma za a iya samun abubuwan konewa cikin tsami kuma ba tare da kazantar da muhalli ba. " (Umaru)
|