Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-14 20:43:57    
A yi yawon shakatawa a magangarar ruwa da ake kira Huangguoshu a kasar Sin

cri

Magangarar ruwa mai suna Huangguoshu tana lardin Guizhou da ke a kudu maso yammacin kasar Sin. Wannan magangarar ruwa ita ne mafi girma a kasar Sin. Tsayin magangarar ruwan nan ya kai mita 74, wato ke nan ya tashi daidaita da tsayin wani gini mai hawa sama da 20. Ruwa na fadowa da sauri daga kokuwar kwazazzabai zuwa kwari mai zurfi, in ka gani, sai ka ce, lallai, fadowar ruwan nan ta yi kamar manyan rakuman ruwa da ke tashi da sauka a cikin koguna. Karar da ake ji a yayin da ruwan ke cin karo da duwatsu ta yi amo sosai, kana kuma wani abu kamar hazo kan tashi sama-sama. In wani ya tsaya a wuri mai nisan mita 50 ko 60 daga magangarar ruwan nan, to, tufafinsa za su jika shakwab da ruwa da ke fitowa daga magangarar ruwan nan.

Magangarar ruwa ta Huangguoshu wata karamar magangarar ruwa ce idan an kwatanta ta da sauran shahararrun magangarun ruwa na duniya. Amma abin da masu yawon shakatawa ke sha'awarta ainun shi ne domin akwai wani kogo da ke kan ratsin tsakiyar dutse. Tsawon kogon nan ya kai sama da mita 100. Kuma a jikin kogon, akwai kananan kofofi guda 6. Masu yawon shakatawa su kan shiga cikin wannan kogo, su tsaya a bakin wadannan kananan kofofi, su more idanunsu wajen magangarar ruwan nan ta kananan kofofin. Bayan da malama Han Ye, yar yawon shakatawa ta birnin Beijing ta ziyarci magangarar ruwa ta Huangguoshu, sai ta bayyana cewa, "magangarar ruwa ta Huangguoshu ita ce mafi kyaun gani da na taba ziyarta. A lokacin da nake tsaye a bakin kofar da ke kan jikin kogon dutsen nan, na hangi ruwa da ke fadowa daga kokuwar kwazazzabai zuwa kwari mai zurfi, sai ruwa mai kayatarwa ya burge ni kwarai."

Ban da wannan kuma a cikin kogon nan, za a ga wata bakar gizo-gizo mai launuka 7 da ke bisa kwarin. Abin mamaki shi ne, inuwarta na tafiya tare da mutane. Haka zalika in masu yawon shakatawa sun tara da hannunsu, to, za su ji ruwa da ke fadowa daga kokuwar kwazazzabai zuwa kwarin nan mai zurfin nan. Lalle, wannan hali ne mai kayatarwa sosai. Malam Abe, dan yawon shakatawa wanda ya fito daga kasar Japan ya bayyana cewa, magangarar ruwa ta Huangguoshu magangarar ruwa ce wadda bai taba ganin irinta ba a da. Ya ce, "akwai manyan magangarun ruwa guda uku a duniyar yanzu. Ban da magangarar ruwa ta Huangguoshu, sauransu kuwa daya tana kasar Amurka, sauran wata daban kuma tana kasar Zimbabwe. A da, na riga na yi yawon shakatawa a magangarun ruwa na Amurka da na Zimbabwe. Bayan da na ziyarci magangarar ruwa ta Huangguoshu, ana iya cewa, ba ma kawai kyaunta ya tashi daidai da sauran manyan magangarun ruwan nan biyu ba, har ma ya fi su a wasu fannoni. A magangarar ruwa ta Huangguoshu, ana iya tsayawa a bakin kofar da ke kan jikin kogon dutsen nan, a hangi ruwa da ke fadowa daga kokuwar kwazazzabai zuwa kwari mai zurfi, wannan ba a iya yin haka a magangarun ruwa na sauran kasashe."

Abin nadama shi ne, nan take kasa kan tsotse ruwa da ke sauka daga magangarar ruwa ta Huangguoshu, sabo da haka a duk shekara ruwa ba ya kwanciya a kasa.

To, jama'a masu sauraro. Nan gaba, idan kun sami damar zuwa lardin Guizhou da ke kudu maso yammacin kasar Sin, to, kamata ya yi, ku yi yawon shakatawa a wurin magangarar ruwa ta Huangguoshu, domin ku yi kallon ruwa da ke fadowa daga kokuwar kwazazzabi zuwa kwari mai zurfin nan. (Halilu)