Firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya yarje tambayoyin da manema labaru na gida da na waje suka yi masa bayan da aka rufe zama na 4 na majalisar wakilan jama'ar kasa ta l0 dangane da maganar raya sabbin kauyuka da maganar Taiwan da dai sauran maganganu.
Wen Jiabao ya bayyana cewa, makasudin raya sabbin kauyuka na gurguzu na kasar Sin shi ne domin bunkasa sha'anin noma da kuma kyautata aikin kawo albarka da sharadin zaman rayuwa na manoma.
Wannan dai wani muhimmin mataki ne da aka dauka domin zamanintar da kasar. Ya kuma jaddada, cewa wajibi ne a ba da tabbaci ga hujjar manoma da kuma samar musu babbar moriya yayin da ake raya sabbin kauyuka na gurguzu.
Game da maganar Taiwan, Wen Jiabao ya karfafa magana, cewa muddin an nace ga bin ka'idar kasar Sin daya tak, kuma idan jam'iyyar Minjin ta yi watsi da tsarin ka'ida kan samun 'yancin Taiwan, to kuwa bangaren babban yanki yana so ya mayar da martani yadda ya kamata domin yin tuntuba da shawarwari tare da ita.
Ban da wannan kuma Wen Jiabao ya bayyana ra'ayinsa kan aikin daidaita awalajar kudin Renminbi, da maganar da ta shafi dangantakar dake tsakanin Sin da Japan da kuma tsakanin Sin da India da dai sauran maganganu. ( Sani Wang )
|