Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-13 21:30:31    
Kasar Sin tana kokarin fama da hadarurrukan da suka auku a wuraren aiki

cri

Assalamu Alaikum, jama'a masu karatu, barka da sake saduwa a cikin shirinmu na yau na Duniya ina Labari. A shekarar bara, saurin karuwar tattalin arzikin kasar Sin ya kai kashi 9.9 cikin kashi dari, amma a sa'i daya kuma, mutane kimanin dubu 127 sun mutu domin gamuwa da hadarurruka iri iri lokacin da suke aiki. Dai Xingwang, wani mahakan kwal na lardin Jiangsu da ke gabashin kasar Sin, yana damuwa sosai domin hadarurruka su kan faru a ma'adinan haka kwal. Dai ya ce, "A wasu kananan ma'adinan haka kwal, hadarurruka iri iri su kan faruwa. Mahakan kwal kamar ni mu kan jin damuwa a kowace rana bayan shigowarmu a cikin kananan ma'adinan kwal, ko za mu iya fitowa daga ma'adinan kwal da rai, ko za mu iya jin dadin zamantakewarmu. Ba mu mai da hankali ko za mu iya neman kudi da yawa ba."

To, me ya sa halin kwanciyar hankali a wuraren aiki da ake ciki a nan kasar Sin ya yi tsanani kwarai kamar haka? Ko wane irin matakai ne gwamnatin kasar Sin za ta dauka domin fama da irin wannan hali? Yanzu ga wani bayanin musamman da wakilanmu suka aiko mana.

Game da dalilan da suka sa aukuwar irin wadannan hadararruka da yawa, a cikin rahoton aiki da firayin minista Wen Jiabao ya yi, ya ce, "Ba a aiwatar da manufofin tabbatar da kwanciyar hankali kamar yadda ya kamata ba, wasu injunan tabbatar da kwanciyar hankali suna ja da baya. Yanzu, ana bukatar kwal sosai, sabo da haka, masana'antun haka kwal ba su mai da hanhali kan halin kwanciyar hankali da suke ciki sun kara saurin haka kwal. Sannan kuma, wasu jami'ai da ma'aikatan kananan gwamnatocin wurare daban-dabam ba su iya cimma nauyin da aka dora musu ba, har ma wasu jami'ai da ma'aikatan gwamnatocin wurare daban-dabam suna neman moriyar radin kansa."

Game da matakan fama da hadarurruka iri iri, Mr. Wen ya bayar da matakai 7 domin fama da su. Mr. Wen ya nemi gwamnatocin wurare da masana'antu da su kara bin tsarin tabbatar da yin aiki a cikin halin kwanciyar hankali. Sannan kuma, ya nemi manyan kamfanonin haka kwal da su sayi ko su kyautata matsakaita da kananan ma'aikatar haka kwal. A shekarar da muke ciki, gwamnatin kasar Sin za ta ware kudin Renminbi yuan biliyan 3 domin goyon bayan ayyukan gwaje-gwaje na yin amfani da gas na ma'adinan kwal. Bugu da kari kuma, za a kara yin bincike kan matsalolin cin hanci da suka faru a masana'antun kawo albarka.

Li Yizhong, shugaban babbar hukumar sa ido kan halin kwanciyar hankali da masan'antun kasar Sin suke ciki ya bayyana cewa, "Abin da ya fi muhimmanci shi ne kafa da kyautata tsarin duba aikin tabbatar da kwanciyar hankali a masana'antun kawo albarka. Lokacin da ake duba sakamakon da wani jami'i ko wata gwamnati suka samu, dole ne a hada da irin wannan sakamako da kimanin rasuwar mutane na masana'antu."

Li Yizhong ya ce, ko da yake halin tabbatar da kwanciyar hankali ya samu kyautatuwa a shekarar bara, amma har yanzu wasu muhimman sharuda suna da bambanci kwarai da na kasashe masu arziki. Abin da Li Yizhong yake damuwa shi ne, domin ya kasance da dalilan tarihi, manyan masana'antun haka kwal na gwamnati suna bukatar kudin Renminbi yuan biliyan 68.9 domin tabbatar da kwanciyar hankali a fannin kawo albarka. Amma kudaden da gwamnatoci za su samar musu ba za su ishe su ba. Idan masana'antun haka kwal na wurare daban-dabam ba za su kara zuba jari a cikin ayyukan tabbatar da kwanciyar hankali ba, shi ke nan, ba za a cimma burin raguwar kimanin rasuwar mutane a cikin shekaru 5 masu zuwa da aka tsara ba.

Domin hadarurruka iri iri su kan faruwa a kananan masana'antun haka kwal inda ba su da karfin tabbatar da kwanciyar hankali, Du Xiaxing, babban direktan kamfanin samar da kwal da ake girke da shi na Shanxi ya ce, yana fatan hukumomin gwamnati da abin ya shafa za su tsara matakai filla filla domin manyan kamfanonin haka kwal na gwamnati za su iya sayen kananan masana'antun haka kwal. (Sanusi Chen)