Yanzu kasar Sin ta mai da hankali kan kudade masu yawa da fararen hula su kan kashe wajen ganin likita. Bisa binciken da ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin ta yi, an ce, mutanen da yawansu ya kai kashi 80% suna ganin cewa, yawan kadaden da su kan kashe wajen kiwon lafiya da ke cikin dukan kudaden da su kan kashe ya karu, in an kwatanta da na shekaru 10 da suka wuce. Majiyyata masu yawa sun nuna fargaba wajen ganin likita saboda kudaden da su kan kashe suna ta karuwa.
To, donme a kan kashe kudi da yawa wajen ganin likita a kasar Sin? Mene ne matakan da gwamnatin kasar ta dauka don warware wannan matsala? Yaya sakamakon da ta samu? A cikin shirinmu na yau na "kimiyya da aikin ba da ilmi da kuma kiwon lafiya", za mu gabatar muku halin da kasar Sin take ciki a wannan fanni. Fararen hula na kasar Sin masu yawa sun nuna damuwarsu kan kudaden da suka kashe wajen kiwon lafiya. Madam Guo, mai shekaru fiye da 50 da haihuwa, wata tsohuwa ce da ke zama a nan Beijing, ta bayyana cewa: "ba ni da kudin shiga da yawa, kuma ban ajiye kudi da yawa ba. Yanzu ba ni da lafiya, ina damuwa cewa, idan in kamu da wani ciwo, farashin magunguna yana da tsada, yaya zan je ganin likita? In ban iya biyan kudi ba, to, ina son in mutu."
Asibitocin gwamnati suka sami rinjaye a kasar Sin, amma donme a kan kashe kudi da yawa wajen ganin likita a nan? Wani muhimmin dalilin da ya sa haka shi ne saboda wasu asibitoci sun nemi samun riba kawai, ta haka kudaden da a kan kashe wajen ganin likita suna ta karuwa; wasu likitoci kuma sun yi wa majiyyata binciken da ba na wajaba ba, da yin amfani da magunguna masu tsada, ta haka, za a kara wa asibiti da kansu kudin shiga. Sa'an nan kuma, gwamnatin kasar Sin ba ta zuba isasshen kudi cikin hukumonin kiwon lafiya na al'umma ba, wannan ya tilasta wa asibitocin su kara neman samun riba.
Don daidaita wannan matsala, gwamnati da hukumomin da abin ya shafa na kasar Sin sun yi dabara, suna daukan wasu matakai masu amfani. Ga misali, an fara kafa asibitoci ba tare da cin riba masu yawa ba a biranen Beijing da Xinjiang da Zhejiang da wasu wuraren kasar. Saboda goyon baya daga gwamnatin kasar a fannin kudi, wadannan asibitoci sun yi kokarin rage kudin da aka kashe wajen ganin likita, sun rage nauyin da aka danka wa majiyyata.
Madam Wang Ling, shugaban asibitin Shangdi da ke nan Beijing, ta nuna cewa:"mun zabi magungunan mafi araha, wadanda suka dace da dokokin kasar. Muna son yin iyakacin kokarinmu wajen rage nauyin da aka danka wa majiyyata a cikin asibitinmu. "
Fararen hula sun yi maraba da asibitin Shangdi saboda ta ba da taimako gare su sosai.
Ban da wannan kuma, a lardunan Henan da Zhejiang da Shandong, wasu asibitoci sun bi hanyar kayyade kudin da aka kashe wajen shawo kan wani ciwo don rage kudaden ganin likita.
Yanzu a biranen Tianjin da Shanghai da Nanjing, saboda kokarin da hukumomin kiwon lafiya na kasar suka yi, wasu asibitoci sun yi amfani da sakamakon bincike daya a tsakaninsu, don rage wa majiyyata kudaden ganin likita.
Ministan kiwon lafiya na kasar Sin Mr. Gao Qiang ya fayyace cewa, a lokacin da kasar Sin tana daukan matakan da aka ambata a baya, ta yi shirin gabatar da shirin yin kwaskwarima kan tsarin kiwon lafiya gaba daya, don warware matsalar kudade masu yawa da aka kashen wajen ganin likita daga tushenta. "mun dade muna nazarin zurfafa yin kwaskwarima kan tsarin kiwon lafiya a birane, mun riga mun sami wasu ra'ayoyi, muna kara yin muhawara kan cikakken shirinmu."
Mr. Gao ya kara da cewa, kafin gwamnatin kasar ta gabatar da shirinta, kananan hukumomin za su yi kokarin neman samun dabarori da hanyoyin da za su bi wajen sasauta matsalar da fararen hula suke fuskanta wajen ganin likita.
|