Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-03-13 15:42:21    
AU ta tsai da kuduri kan aikin kiyaye zaman lafiya a Darfur na kasar Sudan

cri

Ran 10 ga wata, kwamitin zaman lafiya da tsaron kai na Kawancen Kasashen Afirka wato AU ya tsai da kudurin tsawaita wa'adin aiki na sojan kiyaye zaman lafiya da ake girke a yankin Darfur da ke yammacin kasar Sudan zuwa karshen watan Satumba na wannan shekara, a galibi dai kuma ya yardar da mika aikin kiyaye zaman lafiya ga Majalisar Dinkin Duniya bayan karshen watan Satumba. Masu nazarin harkokin yau da kullum suna ganin cewa, an fito da wannan shiri ne saboda bangarorin da abin ya shafa suka yi rangwame kan batun kiyaye zaman lafiya na Darfur.

Nan take gwamnatin kasar Sudan ta yi maraba da wannan kuduri. Lokacin da yake zantawa da wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua ta wayar tarho, jadakan kasar Sudan da ke kasar Habasha kuma zaunannen wakilin kasar da ke kawancen AU ya bayyana cewa, kudurin da aka tsai da kuduri ne da zai iya biyan bukatun yawancin mutanen kasar Sudan. Ya kuma nuna cewa, a galibi ne kawancen AU ya yarda da mika aikin kiyaye zaman lafiya a Darfur ga majalisar, amma bai tsai da kuduri na karshe ba tukuna, sa'an nan kuma, kafin ta aika da sojojinta zuwa Darfur, tilas ne majalisar ta samu amincewa daga gwamnatin kasar Sudan. Ban da wannan kuma, kudurin ya bukaci bangarori 2 na Darfur masu gwagwarmaya da juna da su kara saurin yin shawarwarin zaman lafiya, kuma su bi yarjejeniyoyin da suka daddale a da, musamman ma yarjejeniyar tsagaita bude wuta.

Kafin kawancen AU ya tsai da wannan kuduri, bangarorin da abin ya shafa sun riga sun nuna bayyana ra'ayoyinsu a bayyane. Kawancen AU ya yi bayani a watan Janairu na wannan shekara cewa, da kyar ya dauki nauyin da aka danka masa saboda tsawaita wa'adin aiki na sojan kiyaye zaman lafiya a fannin kudi, ya kuma ba da shawarar cewa, bayan da aka cika wa'adin aiki na sojan kiyaye zaman lafiya a karshen watan Maris na shekarar bana, sojojin kasashen duniya za su mamaye gurbin sojan kawancen AU da su kiyaye zaman lafiya a Darfur. Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, tana son daukan wannan aikin kiyaye zaman lafiya. Kasar Amurka kuma tana ganin cewa, kungiyar tsaron kai ta NATO za ta iya taka rawa mai amfani a Darfur. Amma gwamnatin kasar Sudan tana tsayawa tsayin daka kan rashin yarda da sojojin da ba na kasashen Afirka ba da su shiga Darfur, ta nuna cewa, wannan zai kawo wa mulkin kan kasar illa, zai kuma tsoma baki cikin harkokin gida nata. A 'yan kwanakin nan da suka wuce, mutanen kasar Sudan sun sha yin zanga-zanga a birnin Khartoum, hedkwatar kasar, don nuna goyon bayan gwamnatinsu.

Wani shahararren mai nazarin harkokin siyasa na kasar Sudan kuma tsohon kamfanin dillancin labaru na kasar ya yi nuni da cewa, ba abin ban mamaki ba ne da kawancen AU ya tsai da wannan kuduri, saboda kasashen duniya sun riga sun gano cewa, gwamnatin kasar Sudan tana tsayawa tsayin daka sosai kan rashin yarda da kasashen waje da su tura sojojinsu a kasar, haka kuma ba za ta canja matsayinta cikin dan lokaci ba. kudurin da aka tsai da a wannan gami ya samar wa bangarorin da abin ya shafa da zarafi wajen cin gaba da yin mu'amala.

A zahiri kuma, a cikin 'yan kwanakin da suka wuce, gwamnatin kasar Sudan ta ba da haske game da cewa, ta iya amince da sojojin kasashen waje, amma akwai sharadi, wato tilas ne su shiga Darfur ne bayan da bangarori 2 masu gwagwarmaya da juna suka daddale yarjejeniyar zaman lafiya. Yanzu gwamnatin kasar Sudan ta sami rinjaye a kan teburin shawarwari. Idan yanzu ana yarda da sojan kasashen waje da su shiga yankin da ke fama da hargitsi, za a kawar da rinjayen da gwamnatin kasar Sudan ta samu a cikin fagen daga da kuma teburin shawarwari duka.

Wata matsala daban da gwamnatin kasar Sudan take nuna damuwa a kai ita ce, wasu kasashen yamma sun nuna gaba gare ta, idan wadannan kasashe sun sarrafa sojojin kasashen waje, ko kuma sojojin wadannan kasashe sun shiga kasar Sudan, ba za a amfanawa shimfida kwanciyar hankali a kasar Sudan wajen mulkin kai da halin da take ciki a fannin siyasa ba. Saboda haka, gwamnatin kasar Sudan suna fatan da fakro bangarorin da abin ya shafa za su sami ra'ayi daya kan mambobi da jagoranci da iko da kuma yankunan da sojojin kasashen waje za su tafiyar da ayyukansu.

Kwamitin zaman lafiya da tsaron kai na kawancen AU ya tsai da kuduri kan batun Darfur na kasar Sudan a ran 10 ga wata, amma takarar da ke tsakanin bangarorin da abin ya shafa ba ta gama ba tukuna, ko gwamnatin kasar Sudan da dakarun Darfur da ke adawa da gwamnatin za su rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya nan gaba kadan ba da dadewa ba ko a'a, zai zama daya daga cikin muhimman dalilan da suka ba da tasiri kan matsayin da bangarorin da abin ya shafa suke tsayawa a kai.(Tasallah)