A ran 11 ga wata a nan birnin Beijing, Hu Jintao, shugaban kasar Sin, kuma shugaban kwamitin tsakiya na soja ya bayyana cewa, ya kamata a kara karfin rundunar sojan kasa Sin domin fuskantar hadari da kiyaye zaman lafiya da hana da kuma yako nasarar yaki.
Mr. Hu ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake halartar tattaunawa cikin kungiya-kungiya na taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin. Ya kuma ce, ya kamata a kara yin gine-gine rundunar soja, kuma ya kamata rundunar soja ta dauki aikin kiyaye mallakar kai da kwanciyar hankali na kasar a matsayi na farko, da tabbatar da samun kwanciyar hankali domin kiyaye da bunkasa kasar.
Sa'an nan kuma Mr. Hu ya bayyana cewa, ya kamata a raya rundunar soja ta hanyar kimiyya, da yin kokarin kara karfin fuskantar barazanar kwanciyar hankali da kammala ayyukan soja iri daban-daban, da daga matsayin aiwatar da harkokin rundunar soja ta zamani. (Umaru)
|